Sashe 58
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na kunce jakata na ɗauko kuɗi na miƙawa Abbaa na ce ga shi ya riƙe, ganin yawan kuɗin sai ya saki baki yana kallona da ayar tambaya. A hankali na shiga masa bayanin cewa,"Abbaa da yake acan su kan bawa ɗalibai kuɗi duk ƙarshen wata mutum ya ɗan siya abubuwan buƙata na karatu da dai abin da mutum ba zai rasa ba, to a ciki Abbaa na ke ɗan cire wani abun ina ajiyewa har suka taru haka, don sai da wani course mate ɗina yazo nigeria na ce masa ya canja min su, da zai koma sai ya tafi min da su.
Abbaa ya mayar da ƙwayar idonsa kan kuɗin yana dubansu da jinjinawa yace,"To Sa'ida nan nawa ne kenan? Tun da na ke a rayuwata ban taɓa riƙe kuɗi masu yawan haka ba, naji su da yawa har danne hannu suke yi".
"Dubu Ɗari biyar ne Abbaa, dama na ce a ciki sai a bawa su Yaya wani abun sauran kuma ku riƙe kai da Ummani".
Murmushi me faɗi naga ya bayyana saman fuskarsa, kafin a hankali kuma ya kai hannu ya goge ƙwallar farin ciki, sannu a hankali ya shiga jero min goiya da sanya albarka kamar zai ƙarar da yawun bakinsa.
Ummani kuwa ta É—aga hannu sama tana godiya ga rabbi, faÉ—i take yi,"Haihuwa me daÉ—i, haihuwa me rana, Allah yay miki albarka wannan yarinya ya kawo miki babban rabo, ya azurtaki da mijin marainiya".
Abbaa ya miƙe ya fita zuwa ɗakin Kaka, bai jima sosai a can ba ya dawo ya zauna, bayan ya numfasa yay nisa tare da ce min.
"To yanzu Sa'ida ya ake yi kuma wajen neman aiki? Ko kuwa kana zaune ake neman ka?".
Nace,"Ehh to Abbaa zan fara rubuta CV daga nan sai in kakkai muga ko Allah zai sa a dace, sannan akwai hanya ma da ake bi idan Allah ya taimake ka ya haɗaka da mutane na gari sai kaga abin ya zo da sauƙi kuma cikin aminci".
Abbaa yace,"To shi abin da kika faÉ—a É—in ya ake yinsa?".
"Bayanai na zan rubuta Abbaa, kuma kaga tun da Allah yasa ma da result É—in a hannu kuma an samu me kyau ba za'a wahala ba in Allah ya yarda".
Yay ɗan jim kafin yace,"To shikenan Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi, idan Yayunki sun zo sai muyi magana da su naji, amma ban amince ki nemi taimakon wani ko hanya ta wajen wani ba, wannan duk Yayyunki zasu miki insha Allahu, mutane yanzu babu amana ke ba ƙaramar yarinya ba ce yanzu kina da hankalin tunani, idan kika rubuta shi bayanan duk ranar da za ki je kaiwa wajen ɗaukar aikin sai kiyi min magana mu tafi tare, Allah ya taimaka ya ƙara tsare mana ke da mutuncinki".
Na amsa da amin, mun jima muna ta hira da su don har sai ƙarfe sha ɗaya tukunna na baro ɗakin Abbaa, ina shiga ɗakina kuwa sai bacci, yau ko sallar dare ma ban samu damar yi ba sai da ana sallar asuba na farka shima da ƙyar, don har Abbaa ya tafi masallaci ban iya miƙewa ba, dama shi kafin ya tafi sai ya buga mana ƙofa ni da Yaya Al'amin har sai mun tashi mun buɗe kafin ya wuce.
Kwanana huɗu da dawowa Abbaa yace na shirya muje can ƙauye, ni da shi muka je ƙauyen su da na su Ummani muka gaggaisa da ƴan uwa sai da muka kwana biyu muka dawo.
Muna dawowa kuwa a washegari na dire a gidan Safiyya da yake itama anan Kano take Nasarawa GRA, mijinta me kuÉ—i ne É—an siyasa Babba da ake damawa da shi a wannan gwamnatin. Shekarata biyu a germany aka yi bikin har kusan kuka nayi a lokacin, na so ace ina nan aka yi bikin Safiyya, lokacin nawa tarewa tayi a gidanmu itace akan komai nawa.
Gidanta masha Allah kamar ba a kano ba, kuma Allah ya bata mijin marainiya, yana mugun sonta sosai, ko da ta haihu sunanta ya sakawa ƴar suke ce mata Ilham, to da ke ma dai ƙawarta sai a hankali halinta sai ita tsiya take tsula masa son ranta, Ummansu tana faɗa min tace in ke bata shawara ina yi mata faɗa don ita har ta fara gajiya da halinta.
Na dai bata shawara matsayina na amiyar ƙwarai, sai take ce min ita wallahi ban da mahaifanta auren nan ba yinsa zata yi ba, ita soyayyar duk da yake mata ba wani yarda tayi da ita ba saboda tun abun da ya faru akaina take tsoron sharrin kowanne namiji, na ce mata to ai ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, tayi ta adu'a kawai Allah kar ya kawo abin da zai canja daɗin zamantakewar aurenta.
Ranar yini nayi muna shafta ni da ita, don har magriba, zance daya sai ta kama min zancen fitar da mijin aure tunda na gama karatu, yanzu ko aure nayi karyar namiji yace zai wulaƙanta ni, haka nayi ta bagarar da zancenta har ta haƙura ta ƙyale ni, don ko a gida Ummani sai tayi ta cewa,"Karatu ya kammala, Allah kawo aikin yi da mijin marainiya".
Yi na ke kamar ban jita ba idan ta faÉ—i hakan, Abbaa kuwa kamar zuciyarmu É—aya, tun da na dawo banji ya ambata min kalmar miji ba, sha'anina kawai ya barni na ke yi babu wani takurawa, don sai in ce abinda na ke a yanzu ban yisa lokacin Æ´an matancina ba.
Ga shi dawowata zuwa ake ko da yaushe maneman aure ta ko'ina, ni kuwa nayi mirsisi naƙi fita ko idan Ummani ta lallaɓa ni naje soro na sha zamana tukunna in dawo, ni sam aure ya fita kaina bana fatan ma na sake maimaita shi, na ƙwammaci na mutu da na kara yin aure.
Abbaa ba ya sauraron duk wanda ya zo wajensa, sai yace shi a bar masa ƴa ta sarara ai ba a gidan ruƙo take ba balle a ƙwazzafeta.
Haka mu ke ta sana'armu ta siyar da zoɓo da kunun aya ni da mahaifiyata, ga awara ma da na ke yi ƴar order da mutane ke sawa, a rana sai nayi ta dubu biyar sama, masu siyan ma duk yawanci Safiyya ke haɗa ni da su, Maman Khairi zata siyar da firij ɗinta Yaya Imam yace to ya siyawa Ummani tunda ana samun wuta sosai, yafi ayi ta faman siyan kanƙara ko da yaushe.
Sana'ar ɗinkina kuwa ba kama ƙafar yaro, gowns na ke ɗinkawa ina ɗorawa a jiji app da instgram, Allah yasa min nasibi a nemana ko da yaushe sai nayi ciniki, kafin na fara ɗora kayan sana'ata sai naja lahaula wala ƙuwwa ƙafa goma tukunna, wannan sirri ne da duk wanda ya riƙe a kasuwancinsa zai sha mamaki.
A gefe É—aya kuwa Abbaa yasa Yayyuna suna ta fafutukar nemar min aiki, Yashaik ya rabawa mutanensa takarduna sun fi biyar, Yaya Imam ma da nasa jama'ar, shi kansa Abbaa sai da yace na basa file guda biyu ko da wataran a kasuwa zai ji ana hira tun da akwai Æ´an harkar siyasa da yawa kusa da teburin su.
Ta ɓangarena dai ni babu wani motsi da na ke yi, kawai dai naga su sun tsaya akan lamarin da iyaka ƙoƙarin su sai na barshi na san inda rabo za'a dace.
Ana haka wataran da daddare muna zaune a tsakar gida ni da su Abbaa, har da su Yaya Imam ma da yake duk dare idan suka dawo daga wurin aiki kafin su tafi gida sai sun zo nan sun ɗan jima a wajen iyayensu kana su tafi wurin iyalin su, ana hira Abbaa yana bamu labarin rayuwarsu ta da, ni kuma ina zancen idan na samu kuɗi shagon siyar da kaya zan buɗe, na nunawa Abbaa bidoyin whatsapp na irin yacca mata ke ta buɗe shago, aikuwa kowa ya ƙarfafa min gwiwa da tayani adu'a, Abbaa dai yace ba zai hana ni ba tunda neman halalina ne amma tare da Yaya Al'amin zamu ke zama a ciki, kamar kuma ya shiga zuciyata ya ga abin da ke ciki.
Wayata ce tayi ƙara, na ɗauka ina duba saƙon da ya shigo, kasantuwar datana a buɗe yake sai nayi gaggawan shiga email ɗin na duba, abin da na gani shi yasa ni ƙara tare da dire wayar ina ɗaga hannu sama ina faɗin Alhamdulillah, sai duk hankalinsu yayo kaina nima na maida hankalina gare su ina Kallon Abbaa tare da miƙa masa wayar na ce.
"Abbaa wani asibiti ne suke nemana naje interview jibi".
Yashaik ya miƙo hannu yana faɗin,"Mu gani".
Na basa suka shiga dubawa shi da Yaya Imam, lokacin kuma wani saƙon ke ƙara shigowa ta text message duka dai daga asibiti ɗaya.
Ai fa kowa sai murna tare da adu'an Allah sa a dace, Kaka bawan Allah sai ga shi ya rarrafo daga É—aki yana dogara sanda ya fito shima aka hau murna da shi.
Bayan kwana biyu kuwa na shirya da wuri don ƙarfe takwas suka rubuta cewar naje, Daren ranar ban rumtsa ina ta gayawa Allah haka iyayena ma, ƙarfe shida da rabi muka bar gida ni da Abbaa wai gudun kar mu makara azo a samu asara, ni dai da muka je baki na saki ina kallo, to asibiti babba haka na masu kuɗi wa ya kawo ni?.
Ina duban Abbaa na ce,"Anya kuwa nan ne?".
Abbaa ma dai shima da kokonto cikin ransa yace,"ÆŠauko takardar da kika curo".
Na fito da ita na ba shi, yace,"To ai sai dai mu shiga tare mu tambaya kinga ba lallai suna jin hausa ba ko?".
Da wannan dan wannan kam, muka shiga tare ya dakatar da wani dattijo yay masa sallama suka gaisa, hausar tasa dai bata fita sosai don haka da ni muka ƙarasa magana cikin harshen turanci. Ya tabbatar mana da nan ɗin ne yanzu haka ma ai an kusa fara interview ɗin nayi sauri na shiga kar layi yay yawa, Abbaa yace to idan ba rabo na ubangiji ba Sa'ida wannan asiti ai sai kallo daga nesa.