← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 113

Sashe 64

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ƙwarai Abbaa ina son Sa'ida ba tun yanzu ba, ko a wancan lokacin na haƙura ne saboda ta nuna bata sona, kuma ko a yanzu ma zan iya haƙura idan har ta ce ba zata iya aurena ba, ba zan zamar mata dole ba kamar yanda ba zan so ayi mata dole ba, ni dai burina ne auren nagartacciyar mace kamar Sa'ida, idan kuma hakan bata Faru ba na san da cewa Allah ne ya rubuta cewar ba zan rayu da ita ba a inuwa guda matsayin ma'aurata, kuma zan karɓi hakan a madadin ƙaddara".

Abbaa yay ɗan jim kafin ya sake cewa,"Ka san da cewa ita ba budurwa ba ce bazawara ce ƙaddara ya rabata da mijinta?".

"Na san da hakan Abbaa".

Abbaa ya ƙara mayar masa da cewa,"Fatan kowanne miji ne ya samu zuri'a tare da matar aurensa, Shekaran Sa'ida goma da aure bata taɓa haihuwa ba Salim".

Ya sauke numfashi kana cikin tattausan lafazi irin nasa yace,"Abbaa komai yin Allah ne, Haihuwa da rashinta dukka lamarin ubangiji ne, wataƙila ubangiji ya jinkirta mata lokaci ne wataƙila kuma bata ɗaya daga cikin waɗanda ubangiji ya tsara za su samu rabon hakan, Allah shi ne masani kuma shi yasan daidai na yanda ya tsara rayuwarta, kuma yanda ya tsara mata ɗin shi ne mafi alkhairinta ba don baya sonta cikin bayinsa ba...Abbaa ni Sa'ida na ke so zan kuma zauna da ita a kowanne irin yanayi babu cuta babu tsangwama babu kyara face cikin nuna kalawa da soyayya".

Abbaa ya murmusa, tun farkon fara maganarsu da Salim yaji yaron ya burgesa saboda irin lafuzansa da ke fita daga bakinsa a nutse, kalami na me kaifin tunani da sanin yakamata gami da hankali. Abunda ya sani lokacin da zai aurawa Sa'ida Nazifi bai ji zuciyarsa na ƙarfafa masa gwiwar hakan ba, haka bai ji aminci da salamar da yake ji a yanzu ba.

"Salim na amince maka ka nemi soyayyar ƴata, ka shiga layin zauwaran da suke neman auranta, idan har tayi amanna da kai ni kuma zan aura maka ita, zan baka amanarta, ina son ƴata ya kamata kan da wannan, ka rubuta hakan a tafin hannunka saboda gaba...sai dai akwai sharaɗi game da auren, idan ka amince faƙat idan baka amince ba to sai dai kayi haƙuri".

Salim da kansa ke ƙasa tun ɗazu yana murmushi me kyau saboda samun nasararsa ta amincewar da Abbaa yay masa, furucin Abbaan yasa shi ɗago kai ba tare da alamu na sarewa ko kuma karaya ba, domin kuwa yana da tabbacin zai iya bin kowanne sharaɗi ne muddin zai samu Sa'ida, sai dai sam ya kasa ko da kallon gefen da Abbaa ya ke kamar yanda yay niyya saboda girman kwarjinin da Abbaan yay masa.

Abbaa yace,"Ka shirya jin sharaÉ—in nawa?".
"Ehh Abbaa".

"Yauwa! Sharaɗin shi ne ƴata tana aikin asibiti, da aikinta ka ganta saboda haka babu batun cewar idan ka aureta zaka dakatar da ita ma'ana zaka hanata zuwa aikinta, sannan tana burin ƙaro karatu anan gaba shima ba zaka hanata ba, bayan haka tana ƴan sana'ointa na hannu, ka yarda da wannan yarjejeniyar ko kuwa ya?".

Yay murmushin da sautinsa ya fita a ƙasan ransa, leɓensa kuma ya tale, to taya Abbaa yake tunanin cewa zai dakusarwa da Sa'ida karatunta ko kuma ya dakatar da ita aikinta? Idan da haka why zai shiga ya fita wajen ganin ta kawo wannan matsayin? Abinda yay mata don Allah yayi, kuma alƙawarinsa ne ba zata taɓa sanin hakan daga gare shi ba sai in Safiyya ce tayi katoɓarar faɗa mata duk da itama tayi masa alƙawari har abada ba zata sanar da Sa'ida ba shi ya ɗauki ɗawainiyar karatunta har matakin aikinta ba.
Kuma ba ya so kowa ya sani É—in domin za'a ga kamar yayi ne domin ya mallaketa, kuma itama with that reason zata iya zama with no other option ta tilastawa kanta saboda rama halacci da halacci.

"Abbaa na amince na karɓi sharuɗanka, ba zan zama me sauka daga kai ba, illa iyaka ma ni zan zama wanda zai ƙara tallafawa lamuran nata".

Abbaa yace,"Shikenan duk san da ka shirya kana iya zuwa ku gana da ita, amma bana so a É—auki tsawon lokaci ana abu guda".

Wannan karan sai da Abbaa ya jiyo sautin sanyayyan murmushinsa na samun nasarar da yay. Yana kallon yacca ya gyara tankwashe ƙafarsa kafin ya shiga cewa,"Na gode sosai Abbaa, na gode da bani dama, kuma da yardar Allah ba zaka yi nadamar aura mini ƴarka ba, nayi maka alƙawarin riƙe amanar da ka bani da dukkan ƙarfin ikona, zan kula da ita bisa gaskiya da aldalci".

Abba ya murmusa kafin yace"Ina fatan hakan ta kasance, Allah ya baka ikon tsayawa a tafarkin da yake daidai, Allah yay maka albarka".

"Amin ya Allah Abbaa, Allah ya ƙara muku lafiya da tsawon cin kwana".

Shiru ya gimla tunanin Abbaa sun gama da shi ko zai tafi ne, amma sai yaga ya gyara zama yana aikin jujjuya yatsunsa, Abbaa dai kallonsa yake tayi da murmushi tare da fatan Sa'ida ta amince. "Za ka wuce ne?".

Salim na ƙara yin ƙasa da kai da ƙyar ya iya buɗe baki cikin jin nauyi yace,"Abbaa idan ba damuwa ko zan iya ganinta kafin na wuce?".

Abbaa ya yunƙura ya miƙe yana cewa,"Babu matsala ka ɗan jira".

Abbaa ya wuce cikin gida, kai tsaye ɗakin Ummani ya shiga, tana zaune ita da Walida tana tsefe mata kai ya same su. Ummani ta bisa da kallo tana faɗin,"To ya ake ciki?". Tayi tambayar da zaƙuwa.

"Yana jiranta sai ki mata magana, amma kin san bani son tsayuwan ƙofar gida".

Ummani ta saki kan Walida tana cewa,"Ahh ai dama tun da safe nasa ta kimtsa É—akin Al'amin, ko kuwa su zauna a soron?".

Yay É—an jima kafin yace,"Shikenan su zauna can É—in".

"ÆŠakin Al'amin É—in?".
"Ehh".
"To bari na faÉ—a mata ta kimtsa ko".

Ta faɗa tana fita a ɗakin shi kuma Abbaa na tsokanar Walida da ƙwaƙwido, ta miƙe tana taɓara ya kama hannunta suka wuce ɗakinsa. Ummani na fitowa ta ƙwala kiran Yasmin wacca ke can wurin Kaka, sai gata da sauri ta fito tana zuwa Ummani ta bata maƙulli tace,"Je ki soro za ki ga baƙo ku gaisa ki buɗe masa ɗakin Al'amin kice an ce ya shiga, idan ba ya nan ki duba shi a ƙofar gida".

Yasmin ta karɓa maƙullin ta fita, a soron ta sameshi zaune yana karkaɗa maƙullan hannunsa, ta durƙusa tana gaida shi, bayan sun gaisa ne ta buɗe ɗakin kana ta dawo ta kuma durƙusawa gabansa tace,"Ummani tace ka shiga daga ciki". Yanayin ladabin yarinyar sai ya burge shi, yana mata murmushi yace,"Mene sunanki?".

"Sa'adatu amma Yasmin ake ce min".

Yace,"Umm nice name, kice ina gaida Ummani idan kin shiga".

Ta amsa da to daga bisani shi kuma ya miƙe ya shiga daga cikin ɗakin. Zamansa ba daɗewa Yasmin ta kuma dawowa ɗauke da farantin tangaran da jug da ƙananun kofuna akai sai purewater guda uku.

Ina zaune a ɗaki ina saka stones ɗin rigar dana gama ɗinkawa ɗazu, ban san me ya same ni ba tun a ɗazun dai na ke jina a cikin wani irin yanayi da na kasa gane masa. Abunda ban taɓa yi ba tun mutuwar aurena wai na zauna ina tunanin aure ko sha'awarsa, amma tunda na hau kan keke wani banzan tunani ke neman dagula min lissafi.
Kuma rabon da inji a raina na tuna da tsohon mijina da irin rayuwar da nayi a gidansa wallahi tallahi har na manta, amma yau ni ce tunanin Nazifi ke zuwar min da jin cewa ina ma na haÉ—u da shi ya ganni yaga yanda na koma da kuma irin matakin da Allah ya kai ni, kuma har na ke sha'awar ina ma na samu mijin da zai goge min tabon da Nazifi ya bar min shi da Æ´an uwansa.

Ummani ta shigo É—akin da sassarfa tana cewa da ni,"Ke tashi yi da sauri ki gyara jikin ki".

To na san fita zamu yi dama, saboda haka na miƙe ina gyara fuskata, ina ta kallon Ummani da farin ciki a tare da ita nace,"Wai me ya faru Ummani naga sai murna kike".

"Aa to ba ki so kiga ina farin ciki ne?".
"Ina ni, ai burina ku kasance cikin farin ciki a ko da yaushe".

Na faɗa ina sanya pin a jikin veil ɗin da na yafa na ke kallon Ummani da annurin fuskarta ke ƙaruwa na ce,"To Ummani ai ke ba ki shirya ba".

Tana murmushi me faÉ—i tace"Ai mun fasa waccan fitar, wannan shirin na ki ne ke É—aya, kin gama?".

Nace,"Ehh to amma me yasa kika fasa? Allah yasa ba Abbaa ne ya hana ki ba kinga dai kar a kuma abin kunyar da aka yi aƙi zuwar Hajiya Tabawa gaisuwa".

Tasa hannu cikin jakata tana ɗauko turare ta buɗe tana ƙara feshe ni da shi kamar wadda akewa kamun aure tace,"Bar batun can ko gobe ma je insha Allahu, kije ɗakin Al'amin akwai baƙo ku gaisa da shi".

Da mamaki ƙarara na ke kallonta na ce,"Gaida baƙo kuma Ummani sai naje a haka, ina lefin hijabi ma".

Ta ɓata fuska tana kama hannuna,"To matar liman, yau dai ɗaya mene laifi a ciki, ba ki ga kyan da kika yi a hakan ba ne, duk wanda ya kalle ki sai ya ƙara kallonki yanda kika san balarabiya".

Murmushi nayi da har haƙorana dukka suka bayyana. "Allah kin yi kyau da gaske na ke faɗa miki, tsab sai kin daɗa sace zuciya".

Sai naji kunya ta kama ni, tare da sabon mamaki wanda na kasa samun haske a inda Ummani ta dosa. Tare muka fito a ɗakin ina aikin ɓata fuska don tunda tace baƙo naji sam ban son zuwa gaisuwar balle kuma a cikin shigar da na ke. Zungurar kai nayi ina faman jan ƙafafu takalmi na sharaf sharaf Ummani ta figo ni,"Wai ke ƙaramar yarinya ce, ya za ki tafi a haka".

Na rufe ido na buɗe ina karyar da kai na ce,"Ummani shin baƙon wajen wa ya zo ne?".

"Wurin ki ya zo, don haka ki natsu ki yi tafiya a yangance irin ta mace me tsada kamar ki".
Chapter 64 · 0% Book details