Sashe 77
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka muka yi sallama, ji nayi ina ma bai kashe wayan ba, sai dai yanda na jisa ɗin kaman da damuwa a tare da shi. Har zan koma baccin sai na tuna maganarsa, haka na miƙe ba yanda na iya na buɗe ƙofa, brush da macline na ɗauka na fita, haka na shiga banɗaki sai aikin murmushi na ke yi ni ɗaya ko me yasa oho, ina dai neman zama kamar wata zararra.
Sanda na shiga ɗakin Ummani ne na ga da gaske ashe ƙarfe sha ɗaya, nayi mamaki sosai yauhe rabona da bacci irin haka, na kama yiwa Ummani ƙorafin rashin tashina tace,"Kaman zan karya ƙofan haka na dinƙa bugu, kina can sheme kamar sumamma ba ki san me ake ba".
Nayi dariya ina cewa,"Yo ina na sani ma ni, wallahi banji ba ko kaÉ—an. Yanzu yau haka Abbaa ya fita ban gaida shi ba".
Tace,"Yo shi ai tsoroma kika ba shi, sai da ya leƙa ta taga yaga kin jiya kwanciya hankalinsa ya kwanta".
"Allah sarki Abbaana, bara na kira shi a waya". Na faÉ—a ina fita a É—akin, wayata na É—akko sai da na shiga kitchen na É—auko abin kari kunu da awara tukunna na dawo na samu Ummani.
Ina shan kunun ina jin idon Ummani akaina wanda na san tana kallona saboda nishaɗin da ta ganni a ciki, ni kaina na rasa dalilin murmushina da kasa ɓoye shi.
"Ɗazu na ke gayawa Abbaanki kan zancen ba ki son auren nan, yace zai kira iyayen yaran ya faɗa musu zu so su karɓi kuɗinsu...".
Ai bata ƙarasa na tsinci kaina da saurin bakin ce mata. "Ummani nayi istikara jiya".
"Au tuntuni ke da ba ki nemi zaɓin Allahn ba".
Kaina ƙasa na ce,"Ni dai yau ɗin naji zuciyata ta samu natsuwa da lamarin, kuma ma har naji kamar ina sonsa, ɗazu ya kira waya yace anjima zai zo ya kai ni wurin aiki, nace masa Abbaa ba zai bari ba yace zai faɗawa Abbaan, kuma Ummani sai ya iya faɗa masa ɗin ko?".
Na ƙarashe zancen ina ɗagowa na dubeta, murmushi naga tana yi wanda yasa naji kunya. Bata ce min komai ba sai na sunkwi da kai ƙasa ina bata labarin ma yanda na yiwa Safiyya jiya, sai ta bani wayarta tace na kirata da ita ai ba zata ƙi ɗaga tata ba, ina ƙoƙarin kiran wayata tayi ƙara, ban san lambar don sai da na jinkirta kafin na ɗaga, ina ɗagawan naji muryansa na cewa,"Kin ci abincin?".
Kasancewar Ummani a wurin sai na kasa yin magana, na yunƙura zan tashi tace,"Yi zamanki".
A hankali nace masa,"Ina ci ne yanzu". Sai ya marairaice da cewan,"Ki aje min nawa idan na zo za ki bani da hannunki". Sai ya sake cewa,"Na faÉ—awa Abbaa yace babu matsala, amma ni da ke duk muji tsoron Allah, idan su basa ganinmu Allah na ganinmu".
Nayi shiru ya katse ni. "Baby yanzu ni da ke sai mu iya aikata wani abun mara kyau? Me ma muka sani to? Ko ke kin sani?".
Na cije harshe ina cewa,"Sai ka zo É—in dai". Na faÉ—a ina saurin kashe wayar.
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR09FT5*
Maman Khairi da Maman Yasmin haka suka miƙe tsaye wajen gyara ni ciki da waje, kayan mata kamar hauka Maman Yasmin tasa na tura uban kuɗi aka yo aike tun daga niger, ga Safiyya ma da nata tasa aka kawo min daga sokoto, sam ba'a son raina na ke amfani da magungunan ba, haka na ke shansu a dole wani da daɗi wani ba daɗi, wani ma sai na kusa amai ma na ke iya sha, haka zan ta yiwa Safiyya ƙorafi Maman Yasmin ma na yita mata nurƙufanci, don ni a nawa ganin wannan abubuwan duk ba su da amfani duba da irin rayuwan da nayi a baya, amfanin da na dinƙi yi da su a banza.
Safiyya ce ma me cewa ai yanzu zan san amfaninsu tunda sai yanzu ne zan yi auren, in daina lissafin wancan buhun a sahun maza, in bari in zan maganar ƴan iska mahaukata sai na ke sako shi a ciki, amma na bar tuna na taɓa aure a baya tunda dai ban haifa na baro ba.
Da Safiyya muke ta shige da ficen abubuwan da na ke siya ta ɓangarena, itama haka ta tura min 100k ta account a matsayin gudunmawa, naji daɗi sosai da kuɗin na bawa Yaya Imam nace ya siyo buhun shinkafa da fulawa sai ya bawa Abbaa. Shima yay ta min godiya har da ƙwallata don ce masa nayi sirri ne tsakanina da shi.
Na siya shadda nayi mana anko iri ɗaya ni da Ummani da Abbaa, sannan na siya wani kalan daban na ɗinkawa yayyuna da matansu da ƴanƴansu har da budurwan Yaya Al'amin ma, shigar da na ke so muyi ranar ɗaurin aure kenan, Uwata kuwa kayanta sunan sai ana gobe ɗaurin aure zan ɗakko in bata, don so na ke farin cikin saman fuskarta ya ninku sau dubun dubata, danƙararen less ne na siya mata guda biyu mai shegen tsada kuma nasa aka yi mata ɗinki na zamani, atamfofi biyu kowanne da shigar takalmi da mayafinsa, Abbaa nah ba da kala ɗaya na barsa ba bayan shaddar ɗaurin aure har da set biyu na yi masa na boyel.
Salim ya tura min dubu hamsin na kuɗin gyaran jiki da lalle da kitso, ranar kuwa Safiyya ta dinƙa masifa wai yaushe Brother ya koyi tsumulmula basu sani ba, zata kira shi na hanata sai ta kira Ummansu ta faɗa mata, Umman nasu ma ta kama faɗa wai ko bai da shi ai ba ya bani 50k a matsayin kuɗin gyaran jiki ba balle kuma yana da shi, itama tace zata kira shi taci mutuncinsa nayi ta roƙonta da ƙyar ta haƙura ta ƙyale, ko kusa bana sawa Salim ido musamman akan kuɗinsa, ni yanda yake nuna min bai da wani kuɗi, ko hira muke yi zai ce in koyi haƙurin zama da shi a yanda yake, shi ba mai kuɗi ba ne amma insha Allahu zai yi ƙoƙarin ganin ban nemi wani abu daga gare shi na rasa ba, ba zan yi kukan babu ba in Allah ya yarda, saɓanin yacca na san labarin kuɗinsa a wurin Safiyya, to nima dai a haka na ke binsa dama ni abun hannun namiji ba damuna yay ba, har ce yay min motan da yake zuwa da shi ma na ogansa ne, wannan dai na jisa ne kawai ban wani yarda ba, kawai dai na san kyauta a soyayya da daɗi musamman ma a wurin wanda zaka aura, to ni zan iya cewa bai taɓa kawo min wani abu da sunan kyauta ba, kuma ko da na faɗawa Ummani ma ce tayi kar in sa hakan a raina, ƙila tsarinsa ne a haka sai na shiga cikin gidansa tukunna zai buɗe min aljihunsa, kuma gwara ma hakan akan ya buɗa min a waje sai na shiga daga ciki kuma ya matse kayansa, idan kuwa na nuna masa ban damu ba babu ƙorafi babu tambaye tambamye balle sa ido sai nafi kima a idonsa, shi kansa sai yafi jin daɗin yi min, balle ma mene na damun kai tunda ina aikina ina samu sosai kuma ga kasuwancin da na ke na kawo min kuɗi.
Yau dai ƴan uwa sun ƙara cika gidanmu, Hajiya Ummani an kasa zaune an kasa tsaye, ayi can ayi nan, gidan ya kacame da hayaniya, ni da ban son hayaniya duk sai kaina ya ɗauka yay nauyi, na ƙagu ma ayi a gama taron a watse, du da ina ta faman mita akan me ma za'a tsaya yin wani taro aure ba auren budurwa ba, Maman Yasmin ta danno min zagi tace in ci gaba da maida kaina baya hakan yana da kyau ai.
Yau tun asuba da na tashi kasa komawa bacci nayi, Maman Khairi ma da ta ganni da duku dukun Safiya a gidan Maman Yasmin sai ta kama tsokanata wai ta lura na zaƙu dai a ɗaura auren nan, yau ni ce babu baccin asuba. Nayi dariya kawai na shige ciki ni bata san me nake wa ba, ai kuwa na sha tsiya a wurin su Adama da duk mutanenmu dai na ƙauye da suke kwana gidan Maman Yasmin, ni da naje na ƙarasa haɗa kayayyakina takurawarsu ta hana ni sai baro gidan nayi na dawo gidanmu.
Ɗakin Kaka na shiga inda anan aka ajiye akwatunan lefena da aka haɗa guda sha biyu, ɗauke da kaya masu tsada da kaya na alfarma, da aka kawo su ni dai sai dana tofe abuna da adu'oi saboda baki, kaya kamar ɗiyan wata ƙusar, ko shi da na ɗauka hoto na tura masa sai da yace mun fitar da shi kunya, da shi aka ce ya haɗa ba zai haɗa masu kyan haka ba, har da ce min yanzu da su Granny ba su yi karo karo an haɗa masa ya kawo wannan kuɗin ba ya zai yi? Ni kuwa na ce ummm shine yay ƙwafa wai in koka da ranar haɗuwarmu.
Akwatun da ke É—auke da abayoyi na buÉ—a na É—auko guda É—aya, pink colour tasha ado, na É—akko agogo da yari ma har da sabon takalmi.
Umman Batula ta ƙwala min kira na fita da sauri ina ɓoye kayana cikin hijabina kar a gani a ishe ni da mita, ni kuwa yau ban ga me hanani cakarewa da kwalliya ba.
"Kije ga ruwan can na kai miki banÉ—aki, akwai wani daban cikin koriyar robar nan ki zauna a ciki sai ya huce sai ki fito".
To kawai nace mata na wuce ina ƙunƙuni, wai ba za'a kiraka gefe a faɗa maka abu a sirrance ba sai an gama yayataka a bainar nasi kowa yaji me zaka yi. Shiyasa tunda ta zo da naji kiranta ina fitowa na ke faɗawa banɗaki, sai ta ƙara wani ince gani ciki.