Sashe 16
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuma hankalinsa a tashe yake cewa da Iyam,"Yanzu me zamu yi mata? Ko asibiti zamu tafi? Iyam ba na son abin da zai taɓa min yaro, ba na son abin da zai taɓa Zahra'u, ina son su dukansu sune rayuwata".
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR09FT5*
_Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._
__________________________________
Washegari ban farka ba sai ƙarfe tara. Hakanma da ƙyar na iya tashi saboda zazzaɓi da ciwon kan da na kwan da shi. Ga ɓarin zuciyata da ya dinƙa min ciwo don ko da asuba da nayi sallah haka nayi ta nishi ina jin zuciyata kamar ana soya min ita, shi kansa farko yay banza da ni yana ji ina ta faman kiran sunan Allah cikin wahala, ashe zuciyar tasa da sauran tausayina sai ya tashi ya samo min pain relieve wurin Matarsa, naƙi karɓa na sha a ganina akan me zai karɓo min magani wurin kishiya, kuɗin siyo min me bai da shi? Asibiti kuwa dama bana saka rai don rabon da nayi ciwo yace naje asibiti har na mance, idan na buƙaci zuwa sai ya kama ƙorafin na fiya ciwo da raki, in nemi paracetamol na sha asibitinma ko naje shi zasu ba ni.
Duk sanda yay furucin nan sai dai na girgiza kaina, Namiji ne shi Ƙayar Ruwa, amma ban da rashin adalci irin nasa ko da muna zaman lafiya sarai yasan irin ƙarfin hali na ciwona, sai nayi ciwo ma na gama ban bari ya gane ba. Kuma idan shine ke ciwo mura wannan ya dinƙa kwakwazo, sannan a hakan Zahra'un da ta zo kafin ta samu cikin ma kusan duk sati suna hanyar asibiti bata da lafiya, amma bai taɓa ƙorafi ba.
Ai har sai da na ga ciwo na neman kashe ni kana na karɓa maganin na sha baƙin ciki na daɗa tokare min zuciyata, danasani da nadamar ƙin tsayawa nayi karatuna na baibaiyeni, don duk da wannan tarin baƙin cikin ban fuskance shi ba, a ƙalla da ina aiki ko ba'a biyana da yawa nafi dai ƙarfin na ce da Nazifi ya siya min magani balle har ya ƙuntata mini.
Ni dai maganin ma da na sha sai naji tamkar ana ƙaramin zafin ciwon, haka nayi ta malelekuwa a ƙasa ina hawaye, ga zafin ciwo ga fargabar tunanin Allah sa ba ciwon zuciya ne ya kama ni ba, shima dai abun sai ya ba shi tsoro ya shiga binciken paracetamol ya kawo min, ƙarshe dai sai ruwan zamzam ya tsiyaya ya tofa min bismilla ƙafa sha tara ya ban na sha tukunna na samu sukuni na koma bacci.
Agogo na kalla naga har goma saura, rashin ganin Nazifi a ɗakin banji wani mamaki ba, don na san dama yau ba lallai ya bi ta kaina ba idan zai fita, kuma ba saboda tausayin ciwon da nake ba, sai saboda na faɗa masa Allah ya saka min katse min baccin da yay akan biyan buƙatar wata can da alhakin ci da ita ba akaina yake ba, har ina faɗin ba zan yafe ba shine yace kar na yafe na ce dama ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne ko ban ce ya saka min ba zai saka min ne. Shine har ya na ƙara faɗa min shi fa bai ƙaunar duk wanda ba zai so ƴaƴansa da uwar ƴaƴansa ba, kuma akan hakan yana iya ɓatawa da kowa.
Na sakko a gado cikin ƙarfin hali, ɗakin na gyara anan nayi wanka kana na koma ɗakina na shirya. Saudatu na kallona tace,"Yaya Sa'ida ba ki da lafiya ne?".
Na ce da ita,"Lafiyata lau".
"Naga idonki yay jawur". Ta faɗa tana taɓa jikina sai ta ƙara cewa,"Kuma kin ji jikinki ma zafi".
Bance mata komai ba na buÉ—e wadrobe ina kwaso kayan wanki, sai sannan idona ya kai kan Rumana da ke bacci. Na kalli Saudatu ina cewa,"Lafiyar Æ´ar nan bata je school ba?".
Saudatu tace,"Nima ina bacci ta ƙwanƙwasa ta shigo naga tana hawaye".
Rigar da ke hannuna na ajiye, na yaye bargon da ta rufa da shi ina taɓa jikinta, babu wani zazzabi don haka na shiga tashinta. Ta buɗe ido tana miƙa ganina kuma tayi firgigi ta miƙe zaune tana micimici da idanu. Ina mata kallon shiga taitayinki da ni na ce,"Rashin lafiyar ƙarya saboda kar kije makaranta ko? A haka kike so mu shirya da ke? Salon ki jawo min zagi da cin mutunci ace ni nake hana ki saboda ina baƙin cikin ban haifa ba, koma me za'a gaggaya min ai kin sani dai tun da gaban idonki ake komai. Ina ce har alƙawari kika min akan ba za ki ƙara yin abin da zai jawo min faɗa ba. To saukar min a gado ki ficen kije can, kuma kar na sake naji kin ambaci sunana a bakinki".
Ƙasa tayi da kanta kafin ta sauka ta fita jiki a sanyaye. Na ci gaba da haɗa kayan Saudatu sai magana take min akan na kwanta na huta kuma akwai kuɗi a wurinta ko taje ta siyo min magani nace mata a'a.
Haka na gama na shiga banɗaki ina wankewa tana tayani ɗauraya, babu yanda bata yi da ni ba akan na barta tayi ita ɗaya, ni kuma bana so ne ciwon da nake ji ya kwantar da ni shiyasa gwara na motsa jikin nawa. Yau ɗin dai haka na ke jina sukuku babu wani daɗi, Da ace akwai injin wanki ne sai na ƙyale mata, to tun zuwan Iyam ƴan uwansa suka lalata shi, kowacce ta tashi zuwa sai ta yayibo uban kayan wanki, dama ni ba damuwa nayi da amfani da shi ba dan ko da na ke wankin Iyam ma ban taɓa yi da shi ba.
Mun fita shanya kawai na ga Rumana durƙushe gefen ɗaki ta kifa kai sai shashshekar kuka take yi a hankali a hankali. Ban saurareta ba nayi gaba, sai kuma duk naji zuciyata ba zata iya watsi da yarinyar ba na barwa Saudatu shanyar na dawo. Kanta na tsaya na kira sunanta ta ɗago tana kyarmar jiki.
"Don Allah Anty kiyi haƙuri".
Harara na galla mata nace,"Rufe min baki ni, ba damar ayi miki faɗa sai ki kama kuka, idan kinje makarantar zan miki faɗan ne? Ke ba ki san ni kike bari na kwana a ciki ba, ni kike jawa maganganun ɓacin rai".
Ta saka kuka tana rungume ni tace,"Anty ai ba ƙin zuwa nayi ba, yau ba ki zo kin tashemu ba kuma da Atika ta tashi bata tasheni ba. Sai da ta gama shiryawa na farka, kafin na shirya an tafi kaita shine Anty Amarya tace zata aiki direba na haƙura da zuwa ko na karɓo kuɗin mota ko na tafi a ƙasa".
Tausayi naji ta bani, duk sanda na kalleta sai na tuna wahalar da suka bani, haka sai na tuna wulaƙancin da iyayensu suka yi min, da wanda ake kan yi har yanzu, don na kasa mantawa da dukan da Uwayensu suka min, haka na kasa mantawa da a dalilin sharrinsu watana goma sha ɗaya cif ban taka gidan ubana ba. To amma ita yanzu duk ta maƙale min, ko shareta nake ta dinga kuka kenan tana bani haƙuri, kuma wai saboda ta daina wancan mugun halin Iyam sai take tsangwamarta, itama ƴar uwartata da ta samu ɗaurin gindi sai ta daina kulata, shi kansa gogan saboda Rumanan a wajena take bai fiya lura da lamarinta ba, Atikar dai ita ce ƴar gata a wurinsa tunda tana wurin amaryarsa, ni Rumanan ma har tausayi take bani nayi nayi ta koma can wajen Zahra'un taƙi ita tafi son wajena.
Na ce,"To kin yi breakfast?".
KaÉ—a min kai tayi alamar a'a. Muka sauka naje na dafa mata indomie don ni ban jin ma zan iya cin wani abu kam, Saudatu kuwa tana azumi da yake alhamis da alhamis bai wuceta.
Da rana muna falo muna kallo sai ga su Ummaa sun zo. Da fara'ata na miƙe ina musu sannu da zuwa, fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata, ina cewa ga wurin zama sai ce tayi. "A'a ai ba wurinki muka zo ba, ba ki ga kayan hannun mu ba ne, me ciki muka zo dubawa da kayan barka kafin a haihu mu ƙaro wasu".
Nayi murmushi na ce,"Allah sarki to an gode. An zo lafiya ya Malam?".
Tana jefa min banzan kallo irin wanda Iyam ke min tace,"Malam na lafiya".