Sashe 15
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hmmm ba za ki gane ba ne Safiyya, ni fa duk faruwar wannan lamuran ba na so igiyar aurena ta girgiza, Safiyya idan Nazifi ya rabu da ni wa kike tunanin zai auri macen da bata haihuwa? Shima fa rashin haihuwar ne yasa ya juya min baya har yake ganina banza a wofi, yau idan ace na aje masa ɗa zai kalle ni ne yace ni da babu ɗaya a wurinsa? bayan haka Safiyya ba ki ganin irin rayuwar da zaurawa ke yi ne? Irin tarin ƙalubalen da suke fuskanta ba daga waje ba har da cikin gidan iyaye, a wannan ƙananun shekarun nawa ina zan kai zaman zawarci ni da na ke ɗorawa kaina damuwa da surutun mutane. Na gaya miki fa Kaka ya rantse aurena ya mutu zamana a gidanmu sai in faɗi yay ya mutu. Ko kaɗan mutuwar aure ba ta da daɗi Safiyya, yayin da zuciyarmu ke tafasa ne kawai muke ganin gwara rabuwa da ci gaba da zama, ke dai kawai ki tayani da adu'a ubangiji ya saita dukkan al'amura, ya kawo min sauƙi cikin wannan musibar".
Muryan Safiyya a sanyaye tace da ni,"To Allah ya kawo sauƙi ya saita tsakaninku. Amma lamarin kam sai dai ke ɗin uwar haƙuri, idan ni ce sai dai Baba ya kore ni a gidansa amma sai na kashe auren billahillazi, kuma ba zan bar gidan ba sai na fasa ƙoƙon kan mijin yasin, da irin rayuwar gidanki ai gwara yawon zawarcin ina tafe ana zagina, ina ce dai ba fitowa zai ajikina ba...".
Dafe goshi nayi ina girgiza kai nace,"Safiyya ya isa haka mana. Don Allah kike adu'a Allah ya sanyaya miki zuciya. Anyway yanzu dai ya ake ciki, kiran nan da kika min har naji sanyi a raina".
Numfasawa tayi kana tace,"Dama zan faɗa miki ne wannan ƙwararriyar chef ɗin zata fara classes na girki amma online zata yi, kinga kin samu dama sai kiyi joining ko? Gwara kema ki koyi girke girken zamanin nan da ake na larabawa kike girkawa kanki ke ɗaya kina ci kina barin ƴan iska da shaƙar ƙamshi da tsinkewar yawu".
"Uhmm to Safiyya ni kam don wa zan koyi girkin idan ba don shi ba, ai gwara na iya yaci na wuce gori. Amma nawa ne kuÉ—in da ake biya?".
"7k ne kuma kar ki damu da wannan zan biya miki, dama i want hear from you ne if kina so kar nayi azarɓaɓin biya miki ki gwanya ni".
Ina murmusa kunci na ce,"Alright na gode sosai ƙawar arziƙi, Allah barmu tare ya baki miji na gari. Sai batun spices na abinci da kika ce shima za ki haɗa ni da wacca zan ke siya a wurinta".
"Amin ya Allah na gode da adu'a. Ehhh spices kar ki damu akwai Mrs Arab zan haɗaku, ba lambarta ne a wannan wayar da sai na ba ki yanzu...Ai in sha Allah kwanan Nazifi zai raina kansa, sai yay danasanin duk abubuwan da yake miki, ke dai kike riƙe duk tips ɗin da na ke ba ki, ƙananun kayan ma zan sako su a mota jibi a taho miki da su, saura idan an kawo kike ƙin sakawa kin ji, wallahi Beb kayan da na siya miki kika saka kika gimla ta kusa da Nazifi na rantse miki da kansa zai kawo kansa ɗakinki, bar shege da mu yake zancen, itama matar tasa zata ci uwarta ne".
"Ƙawata ta kaina, shikenan to ina godiya kuma in sha Allah duk shawarwarinki gare ni zan ke amfani da su. Naji kin ce za ki yi aiki bara na barki haka sai da safe".
"Ok Beb bye bye take care. Allah kuma ya saka miki nan kusa. Zan tura miki lambar chef É—in sai kiyi mata magana tayi adding naki group".
Ta kashe wayar ni kuma na tashi naje na ɗauro alwala nayi sallar isha'i da ban yi ba. Ƙarar wayata na shigowar text na ɗauka ina duba lambar da Safiyya ta tura mini, 09030398006. Take ko nayi saving na shiga whatsapp na aje mata saƙo.
Cikin kwanaki biyun da suka biyo baya abubuwa sai ƙara faruwa suke, ƴan uwan Zahra'u kuwa sai shige da fice suke a gidan ana zuwa dubata da jiki, yanda suke ta nan da ita sai abun ya burgeni da bani sha'awa, ina jin ina ma ace ni ce, wato ashe haka me ciki ke zama ƴar gata ta kowanne ɓangare.
Nazifi da ƴan uwansa kuwa sun maida ita kamar ɗanyan ƙwai sai riritata suke yi, ni dai ina ta ganin abubuwan da yanzu ko kusa basa damuna ma sai dai nayi murmushi na girgiza kai, haka za suyi ta yada habaici idan suka zo, to ni kalmar juyan ma yanzu jinta na ke kamar iska bata taɓa zuciyata.
Shi kuwa da gayya sai ya shigo min ɗaki yana tambayata wai ina da abu kaza Baby ta kasa cin komai, ai na nake ganin za'a samu abu kaza, haka dai ni kam ban bi ta kansa ya gama surutunsa ya fice. Ranar ma da yana wajena sai ce yay in taimaka duk sanda nayi tuwo in ke zuba mata na ce ba zan iya ba, shine ya hau fushi wai a tunaninsa zan fishi farin ciki da samun cikin nan amma sai yaga akasin haka, bai taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba kuma yayi mamaki sosai, amma na sani yaron da za'a haifa shine farin cikinsa sama da komai a duniya, saboda haka gwara na koyawa zuciyata sonsa tun kafin yazo duniya idan ba haka ba kuma zaman mu da shi zai fi na baya muni.
Cikin ikon Allah da na ƙara dagewa akan adu'a sai na ɗan fara samun kan Nazifi, yanzu zai zauna da ni har mu ɗan yi magana, kuma ko ban je ɗakinsa ba zai neme ni, duk da ahakan ba gane masa na ke ba.
Kuma wani abun mamaki hakan sai yasa Zahra'u ta tsiro da wata tsirfa ta makirci ganin cikinta ya fito sosai, wato duk ranar da Nazifi ya dawo wajena ba zata bar ni da shi ba, sai mun kwanta sai kiranta ya shigo waya tana yi masa kuka ita cikinta, Small Baby yana takura mata, amai take tayi ta kasa bacci, zata ci abu kaza, tana ga haihuwa zata yi, abubuwa dai iri daban daban da ba ya iya haƙura shi kuma sai ya farka yaje wajenta, haka zai zauna ba zata barsa ya dawo ba sai asuba.
Lamarin tun bai damuna sosai har ya zo ya dame ni, na kira Ummani na faɗa mata sai ta shiga bani haƙuri kamar kullum tana faɗa min dama a irin wannan gaɓar akwai wahala, sai dai na ƙara haƙuri da kawar da kai, aduar nan dai kawai naci gaba kar na fasa.
Da dai naga abin ya ishe ni muka yi waya da Safiyya na ke faɗa mata, sai ce tayi nima in fara yi masa ƙaryar ciwo wala yana wurina wala bai wurina, ita zama ta haɗa ni da likitan da zaa ce ciki ne da ni, cikin ƙarya ai ba akaina aka fara ba. Ban dai ɗauki wannan shawarar ba kawai na yanke abin da na ke ganin yafi min, dama da ya kwanta gado sai bacci shine kawai sai na samu na saka wayar a silent, haka kafin nayi bacci zan ta ganin kiranta na shigowa, asuba nayi kuma zan riga shi farkawa na cireta a silent, sai da safe idan yaga kiran sai ya kama tambayata wai kwana biyu wanne irin bacci muke yi ne, sai in masa shiru bana tanka masa.
Yauma muna kwance mun ma yi nisa a bacci, kamar a mafarki naji ana ƙwanƙwansa ƙofa. Na kasa motsawa daga kwancen da na ke saboda mamakin da ya kama ni haka kuma kaina ya ɗaure, na tafi tunanin wa ye da bugu a daidai wannan lokacin haka? mirginawa nayi na ɗauko wayarsa don duba lokaci sai naga kiran Zahra'u na shigowa, ikon Allah kawai sai na kasa aje wayar na tsaya kallo har kiran ya katse, ƙarfe biyu lokacin. Tsaki nayi na aje wayar na koma na kwanta, can kuma sai aka ƙara ƙarfin bugu ka ce an biyo sahun karɓar bashi.
Ina kallonsa ya tashi zaune yana ɗaukar wayarsa ya duba, sai kuma naji yana magana shi ɗaya. "Allah yasa lafiya". Ya faɗa yana sauka akan gadon ya tafi ƙofa yana tambayar waye.
Wallahi tsammanina duk Iyam ce ko kuma ita Zahra'un, amma sai naji muryar Æ´ar aikinta na cewa.
"Alhaji Anty ce bata da lafiya".
Ai lokaci guda baccin ya bar idonsa da sauri ya buɗe ƙofar, yana niyyar fita na kasa haƙurin cewa da shi,"Ina zaka je kuma?".
Ya juye ya kalle ni fuska duk ta gama bayyana da damuwa yace,"Ba ki ji ba Amarya ce babu lafiya, ko za ki taso muje ki É—an taimaka mata".
Iya shaƙa na shaƙa har naji kamar na miƙe na wanke shi da mari. A yau kam bana tunanin zan musu uzuri, na gaji da cutarwar da ake min, Na ɓata rai ban miƙe daga kwancen da nake ba na ce,"Amma dai kasan hakan shiga hakki ne ko? Ita ciwonta ba ya tashi kullum sai taga kana wajena, a wajen nawa ma sai muna tsaka da bacci, wato kiran wayar ma da ta saba duk bai mata ba sai ta koma haɗawa da buga ƙofa? Wannan ai zalunci ne, mutum yay magana kuma ace yana baƙin ciki da hassada".
Wani kallo ya shiga yi min wanda na kasa fassara shi. Sakkowa nayi a gadon na isa bakin ƙofa zan mayar da ƙofar na rufe na ke cewa da ƴar aiki,"Ki koma kiyi jinyartata ko ki faɗa mata tasha magani".
Kafin na kai ga rufe ƙofar sai jiyo ihunta muka yi a falo, tana kiran,"Wayyo cikina, wayyo marata, Derling ka zo ka taimaka min don Allah, Derling mutuwa zan yi".
Ai kafin na ƙifta ido Nazifi ya fice, idona ya ciko da ruwan hawaye, ina tsaye naji Iyam na faɗin.
"Ki yi haƙuri Amarya ciki dama ya gaji haka amma ki daina kiran za ki mutu, mutuwa ba yanzu ba in sha Allahu. Zafin ciwo ne kawai sannu kin ji, ai kina ma ƙoƙari wallahi Allah ya ba ki da sauƙi".