← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 113

Sashe 27

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina nan zaune zaman asibitin duk ya gundure ni, ba don yace lallai na tsaya sai ya zo tukunna mu tafi tare ba, niyyata muna gama gaisawa naga yaran sai na juya. Ba abin na fita daga wajen ɗakin ba duk ƙannen Nazifi ne da Yayyansa, ni kam da na zauna tare da su gwara na zauna nan ɗin suyi ta min habaicin, don nafi jin zafin cin mutuncin ƴan uwan Nazifi akan na ƴan uwan Zahra'un. game ɗin ludo na saka mana a wayata muke yi ni da Rumana, hankalina ya bar kan kowa sai dai kunnuwana ba su fasa jiye min yacca ake ta aikin yada min baƙaƙen maganganu ba ana aibata ni, zuciyata taji ba zata jura ba kawai na miƙe na kama hannun Rumana muka fice.
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR13FT5*
Maman Yasmin da Maman Khairi da Yaya Nusaiba wato Yayar Safiyya suna ta hirarsu, ni dai ina daga gefe ina jin su sama sama, nayi wanka lokacin na shirya cikin wasu kaya marasa nauyi da Maa ta bayar aka kawo min, hankalina duk ba ya jikina, zuciya da gangar jiki sun cika da kewar Salim, babu abinda na ke son ji a yanzu sama da muryarsa, don na san ba zan samu ganinsa ba ko da ace yana cikin gidan.

Idona na rufe Safiyya ta shigo tana faÉ—in,"Ke to ga Æ´arki nan ta addabi mutane a kaita wurin New Mommy". Nayi saurin buÉ—e ido ina kallon Rofi'at É—in da murmushi, zaune na tashi na buÉ—a mata ta taho da gudunta ta shige jikina, Allah ya gani tun ba'a je ko ina ba na kamu da soyayyarsu, muna can muna magana ashe yarinya har tayi bacci, gyara mata kwanciyarta nayi a jikina.

"Safiyya hanya dai lafiya ai babu matsala ko?".

Ta baro hirar da suke ta waigo tana kallona tace,"To banda abinki ba tare da security suke ba, ki kwantar da hankalinki nan da ƙarfe uku na dare za ki gansu".

"To Allah ya kawo su lafiya". Na faɗa ina kwantar da kaina kan filo, sai da muka yi dai wayar da su Mama A'i suka ce min wallahi lafiya lau suke gasu ana ta fafara gudu da su akan hanya, zuwa ƙarfe ɗaya ma za su iya zuwa. "To Allah ya kawo ku lafiya Mama A'i".

Cikin baccin da ya fara fizgata naji yo ƙarar wayata, da sauri na farka na ɗaga ina sawa a kunne ko numbern ban duba ba, can naji muryan mace cikin turanci na ce min,"Ba dai har kin yi bacci ba".

"Umm wa ke magana?". Muryarta ya bayyana irin rashin jin daɗin nan da cewa,"Kudrat ce". Fuskata a yatsine na ce,"Ayyah barka da dare". Haƙuri ta shiga ba ni kan kiran da ta min nayi bacci, na ce mata,"babu komai ai".
Sai ta sake cewa,"Shi ne ba ku biyo ta nan ba kun barni ni É—aya a gida shiru".
Na kyaɓe baki ina cewa,"Kema ai sai kika ƙi zuwa nan ɗin".
Murmushinta tayi wanda ke bayyana bata da damuwan komai tace,"Ki yi haƙuri shi ne yace ba sai na zo ba, yaran kawai za'a kai, amma ɗazu Maa tace gobe da safe nima na taho tunda akwai party da za'ai".

Murya a daƙile na ce,"Allah ya kaimu".
Tana son jana da hira ina ga ko kaɗaicin gidan ne ya dameta, da kuma mijin nata da basu samu yin waya ba don alamun hakan ya nuna, tana ta ce min fatan dai Yarana ba su dame ni ba ko, na ce mata ga Rofi'at ma kusa da ni har tayi bacci, ni dai na nuna mata bacci na ke ji, muka yi sallama nayi cilli da wayar gefe tare da jan dogon tsaki wanda har sai da Yaya Nusaiba ta tambaye ni lafiya, kawai nayi saurin kulle idona da zummar a cikin bacci nayi, nan kuwa haushi da takaicin kiran Kudrat ne, aikin banza ita ko kishi ma bata yi zata wani kira ni da ƙatuwan muryanta ita lallai ga ta me kirki, ta bar ni inji da damuwan rashin jin Salim ɗina ma, shegen iyayi da neman suna da makirci irin na su na ƙabila, ƙwafa nayi ina janye Rofi'at a jikina na juya mata baya.

Ni fa banga ta bacci ba yau sai ta Allah kuma, babu nutsuwa sam tare da ni, kowa ya shigo yaga yanda na takure kaina sai kallo da ido sai ace baƙunta ce, Safiyya ma haka ta zo ta gama zuba min surutunta sai da ido kawai na ke kallonta, ita ce ma ta fahimci yanayin da na ke ciki tace bari dai taje ta jiyo min labarin mijin nawa wurin Sir, na zama ƴar soyayya zan mace musu tun basu kai ni ɗaki ba. bayan fitarta duk na zaƙu ta dawo ta sanar min halin da mijina ke ciki, na ɗaga waya zan kirata sai naga ashe ta bar wayan nata anan, ni dai nayi ta faman juyi akan gadon duk na rasa me ke min daɗi, su Maman Khairi ma da suka lura da ni sai suka shiga min shaƙiyanci irin na su wanda har sai da naji kunya, tun kuwa da nasa filo na rufe fuskata ban ƙara buɗewa ba.

Sai ƙarfe biyu da rabi Umman Batula suka iso, da aka tashe ni ma ce na ke gari ne ya waye jin hayaniya da hasken fitilun gidan da ba zaka taɓa cewa dare ba ne, naji daɗin ƙarasowarsu lafiya kuma ina ganin hakan na rarumi wayata na kuma kiran Salim shiru kiran bai tafiya.
Hankalina sai ya tashi idona ya cika da ƙwalla, rabona da shi fa tun safe, shima magana muka yi a tsaitsaye, jiya kam dama totally banji muryansa ba, ni kuwa wanne irin horo wannan aikin na su yake min, dama haka aikin na su ya ke da barin mutum cikin fargaba da tashin hankali? Kuma babban abin da ya ɗaga min hankali da yace jirginsu ne zai kewaye a can wani ƙurgummin daji. rumtse ido nayi jin hawaye na neman sakko min na rungumo Rofi'at jikina gabana na ta faɗuwa, haka bacci ya sace ni ina ta adu'an Allah yasa dai lafiya, ya kula min da mijina a duk inda yake.

Da asuba ma da muka yi sallah ban iya komawa bacci ba, ina kallon su Mama A'i da Maman Khairi aka yi sallah aka koma bacci, kowanne to a gajiye yake sai faman miƙa suke yi, ga shi sun samu gado wawakeke da katifa me bala'in taushi. Har gari ya fara wayewa kaina na bisa gefen gado duk na kasa sukuni, zuciyata matse da taraddadi, idona kuwa na kasa ɗauke shi akan wayata ƙiris na ke jira in ga kiran Salim ya shigo.
Duk yanda na so na daure na kasa sai da na kira Ummani, ko da ta É—aga yanda taji muryana sai ta shiga tambayana lafiya, kwana nayi ina kuka?".

Nace mata,"A'a tun jiya ne bayan ɗaurin aure har yanzu bamu ƙara magana da Salim a waya ba, ko message idan na masa ba reply kuma ni har yanzu ban ji wani yace sun yi magana da shi ba".

Na faɗa da muryana tamkar zan yi kuka. Sai naji ta sauke numfashi tana tayani adu'a Allah yasa lafiya. "In Allah ya yarda lafiya, kin san yanayin aikinsu da kurɗa kurɗan shiga daji wataƙila suna wurin da babu network ne".
Haka ta ɗan kwantar min da hankali, sai da ta haɗa ni da Abbaa muka yi waya shima yana tambayana ya kwanan baƙunta nace masa babu daɗi duk nayi kewarsu, shima kuma yace in kyautata zato a raina in Allah ya yarda lafiya lau Salim yake koma a'ina ne.

Wajen takwas aka turo ƙofan ɗakin, idona karaf akai kaman zan ga Salim, baccin gajiya ne fal cikin ƙwayar idona amma har ga Allah ba zan iya ba, duk wanda ya ganni ya san hankalina ba kwance yake ba, abinci ne aka kawo mana kala kala na break fast, bayan tea da soyayyan bread da ƙwai, akwai ferfesun ganda da snacks da soyayyan kaza, sai kunun tamba da ƙosai, kowanne ya bani sha'awa amma ba zan iya ci ba, ko jiya ina ganin teba da miyan kuɓewa yawuna kaman zai dalala amma na kasa ci, to da wanne teste ɗin bayan wanda ke da ɗanɗanon bakin ya tafi da shi.

Haka su Maman Yasmin suka zage suka ci abincinsu ni kuwa ban iya ko kai hannu kwanon ba, ina zan iya cin abinci ban san a wanne hali Salim yake ciki ba, ai ko ruwa ba zan iya sha ba, ba yanda ba'a yi da ni ba na ce ni na ƙoshi, har da ƙaryan amai ma na ke ji, Safiyya na min iskancin wai da an kai ni na faɗi haka sai ta ce Salim ya iya aiki, su kuma duk tsammaninsu ƙulafucin gida ne babu wanda ya kawo a ransa cewa rashin jin mijina ya jefa ni a halin ƙaramar rashin lafiya.

Safiyya ta zo muka fita tare da ita Maa ce ke kirana, a É—akinta muka sameta cikin shiga na alfarma, tana ganina fuskanta ya washe da annuri, cike da kunya na isa kusa da ita inda take min nuni da na zauna, muka daÉ—a gaisawa da ita don tun sassafen da aka kai mana abinci muka fito gaba É—ayanmu muka same su a main falo ita da Mommi muka gaida su, kuma babu É—agawa Maa da Mommi É—in su ne suka je da kansu har É—akin da aka sauke su Mama A'i suka gaishe su, ashe can ma haka aka kai musu tulun uban abinci, ko ina za su kai shi oho.

Tana kwanto ni jikinta take ce min,"Kin ci kin ƙoshi?". Na ɗaga mata kai alaman ehh, sai tace min to nayi wanka anan na shirya, can sai na barwa sauran suma su sami kimtsawa. Kaya ta ɗebo min a wadrobe ɗinta riga da skirt na atamfar ankara, ta aje min duk wasu kayan shiryawa, ni dai duk a kunyace na ke na so ace ta bar ni na shirya a can cikin ƴan uwana, da taga itama alaman hakan tana murmushi take dafa kafaɗana tace,"Ni fa Mamanki ce babu batun jin kunya tsakaninmu, ki saki jikin ki da ni kinji daughter nah".
Chapter 27 · 0% Book details