← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 113

Sashe 1

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR1FT5*

__________________________________
A lokacin da na buɗe idanuwana cikin tsanani da raɗaɗin ciwo akan fuskar da ban taɓa sani ba na sauke su wato fuskar SJ wanda yay min rumfa a ƙoƙarinsa na taimako ga likita da ya buƙata na a rirriƙe ni. Kuma wannan shine mafarin shigowar rayuwar Sadiƙ Abubakar Jadda gare ni, kamar yanda silar siyan rake ya zama mafarin haɗuwata da Nazifi Bala Mai Kalwa. Na sha jinya a sanadiyar hatsarin da nayi kamar ba zan rayuwa ba don har sai da aka yi tunanin fitar da ni ƙasar waje domin a duba ƙwaƙwalwata a cewar likitoci ba ƙaramin buguwa nayi ba, hankalin ahalina ya tashi, natsuwa tayi ƙaura daga garesu domin ba su da kuɗin da za su fidda ni ba su da dalilin su, tsananin damuwar ne ma silar kamuwa da hawan jinin mahaifina domin shi a lokacin ce yay kawai a bari ubangiji yay ikonsa, shi kam ya cire rai da ni, duk da Amb Jadda ya ce ba su da damuwa su ne za su yi komai tun da sune sanadi, kuma kan ka ce mene wannan SJ da ke matuƙar ba ni kulawa har ya tattara bayanan komai zuwa ƙasar da za'a fitar da ni, sai ga shi kuma cikin hukuncin ubangiji a irin adu'oin da iyayena ke ta min da faɗi tashin ɗawainiyar asibiti da iyalan Amb Jadda ke ƙara yi akaina sai komai ya zo da sauƙi cikin ikon ubanji kuma na sami lafiya.

Ahalin Amb Jadda mutanene ma su tsananin mutunci da karramawa da sanin darajar ɗan Adam, Dr Hassana Abubakar Jadda macece ta gari wadda ta fita daban a cikin mutane, akwai ta da tsananin tausayi gami da kyautatawa, haka shima mijinta Amb Jadda mutum ne me tausayin talaka da son taimaka masa shi dai illarsa ɗaya shan sigari da har aka ce tayi masa illa ta taɓa lafiyarsa amma duk da hakan bai daina sha ba sai ma ƙari, wanda shan sigarinsa shi ne sanadin rashin jituwa tsakaninsa da Ɗansa SJ da ko magana bata haɗa su. Idan har magana wa junansu ta zama dole to suna isar da ita ta rubutun takarda ko kuma a waya, idan kuma a gida ne Maamee ita ce me aika saƙo a tsakanin uba ga ɗan, amma Amb Jadda in har zaka faɗa masa gaskiya akan shan sigari to zaku ƙulla gaba ne da shi.

Ko bayan sallamata a asibiti da aka yi Maamee bata watsar da mu ba, ta kan zo gidanmu ta gaishe da mahaifana nima kuma ta duba ni tana me ƙara bada haƙuri akan afkuwar hatsarin. Wanda a kowanne lokaci Ummani da Abbaa ke nuna mata babu komai hakan tsararran lamari ne da ubangiji ya shirya faruwarsa ko da bata sanadinta ba. Silar hakan kuma sai ya zama zumunci ya ƙullu tsakaninmu da ahalin Amb Jadda musamman ma ta ɓangarensu, don ana mu ɓangaren mu kan ja da baya da su duba da cewa ba tsararmu ba ne su, suna da kuɗin da ko da kaf zuriyarmu aka siyar ba za'a haɗa kaso biyu na daga dukiyar da Allah ya ba su ba, kuma su ɗin manyan mutanene da duniya ma ta san da zaman su.

Ta ɓangaren Nazifi me rake shima mutum ne me tsananin kirki na gaban kwatance, rashin zuwa makarantar da na ke yi ya tambayi su Safiyya dalili suka faɗa masa, a ranar ya zo duba ni da ledar kayan dubiyansa daidai ƙarfin talaka, sai ka rantse wani ɗan uwa ne na kusa. Kuma ba'a cika sati ba sai ga shi sun zo da ƙannensa maza da mata, suma zuwan na su da kayan dubiyarsu suka zo, haka aka dafo min miya da kaji da kayan marmari a leda. Kusan kullum sai ya zo duba ni, kuma ba ya zuwa haka kawai sai da kayan dubiya.

Daga nan kuma shikenan sai zumunci ya ƙullu a tsakaninmu domin kuwa bayan an sallame ni daga asibiti hatta Yayar Nazifi da Mahaifiyarsa sai da suka zo har gida duba jikina, da yake mahaifiyarsa macece mai faran faran yini ɗaya sai suka zama tamkar dama can an san juna ita da Ummani har Abbaa ke musu tsiya, ita dai tana ba su labarin ai Nazifin kan yi mata hirarmu ni da su Safiyya akan yabon hankalinmu da tarbiyarmu.

Tun daga wannan ranar kuma ko abincin gargajiya Iyam tayi sai ta aiko an kawowa Ummani duk da nisan da ke tsakaninmu da unguwarsu, aiken alkhairi duk ita ce, idan ta tashi haka zata ciko ƙaton kwano da daddawa ta ce a kawowa Ummani. Itama Ummani haka duk sanda ta samu abun arziƙi ta bani in kaiwa Iyam, idan na je gidan yini na ke sai Yayan Shago ya dawo ko Yaya Nazifi tukunna Iyam tasa a rakoni gida.

Tafiya tayi tafiya wata rana na dawo daga islamiya, na tarar da sabuwar mota kar a ƙofar gidanmu, zuciyata cike da mamakin su waye baƙin da muka yi, sai da na shiga gida na tarar da Maamee ita da Marfu'a da Madam waɗanda zuwansu babu jimawa kenan. Bayan gaisawarmu na wuce ɗan tsukukun ɗakina domin cire uniform, ina ciki Ummani ta ƙwala min kira nayi saurin ƙarasawa na fito da hanzari, a kicin na sameta ta dube ni tana cewa.

"Sanyo gyalenki ki kaiwa me suke ce masa ruwa yana waje".

Nayi É—an jim sai can na ce,"ohh Bayya ko?".

Ta gyaɗa kanta,"ehh shi, yaƙi shigowa gidan kin san bai da sakewa kamarsu".

Na koma ɗaki na sanyo ƙaramin gyalena na zo na karɓi ɗan ƙaramin farantin robar hannunta, wanda aka sanya pure water masu sanyi guda biyu akai, fita nayi inda na tarar motar bata ƙofar gidanmu kamar ɗazu, nayi leƙe leƙena ban ganta ba hakan yasa na juya domin komawa sai kuma sai naji anyi fakin, na waigo naga motar ce ta dawo. ƴan sakanni kana na taka na ƙarasa ɓangaren mazaunin direba na ƙwanƙwasa gilashin. A hankali aka zuge gilashin, tsammanina ma Bayya ne ashe Na-Madam ne sarkin tsokana. Yana kallona da murmushi ya kira ni da sunnan da kaf gidan na su ke faɗa min.

"Dimple".

Murmushi nayi inda malotsan gefen bakina suka lume ciki, na rissinar da kaina ƙasa ina cewa da shi. "Ina wuni".

Ya amsa min da fara'arsa,"lafiya lau Dimple, ya su Ummani da Abbaa".

"Lafiya ƙalau. Ga ruwa ta ce in kawo maka".

Ya kalli farantin hannuna wanda har naji wani iri saboda na roba ne kuma duk yasha jiki. Ya miƙo hannu ya ɗauka ruwan cikin tare da faɗin an gode. Sallama na masa zan wuce nan yake ce min,"ba ku gaisa da Bayya ba".

Sai sannan ma idona ya kai cikin motar in da na hango shi zaune idonsa zagaye da baƙin gilashin da bai rabo da shi, da ƙananun kaya a jikinsa kamar ko da yaushe don ni dai ban taɓa ganinsa da manya ba, yay kyau sosai p-cap na ɗaukar fuskarsa, shi irin masu kyan da ake kallo ne aji kamar a sace a gudu. haka ɗaya sai naji gabana yay mugun faɗuwa nayi saurin ɗauke ido daga barin kallonsa, a hankali kuma na ce,"Ina wuni Bayya".

A kaikaice ya dube ni ta cikin gilashin, kamar ba zai amsa ba saboda yanda yaja lokaci can kuma sai ya ce,"lafiya lau, ya kike ya mutanen gida?".

Yay maganar cikin birkitacciyar hausarsa da bankinsa bai gama ƙwarewa da ita ba, don ba ya dogon zance ba tare da ya saka faransanci a ciki ba, har sha'awar hakan na ke ni kam, sai naji ina ma ni ce na iya wani yaren bayan hausa.

Ina gyara gyalena da ke neman zamewa na ce masa,"duk suna lafiya ƙalau, Ummani ta ce a gaishe ka".

Kansa ya gyaɗa wajen amsa min. Na-Madam cikin zolaya ya ce da ni,"Hajiya Dimple sanyi ƙalau, ke dai sam ba ki son magana, yanzu idan na ce ki tayani hira fa sai ya zamar miki jan aiki. To ai shikenan ki gaida mutan gidan".

Ina murmushi na wuce, ina gab da sanya ƙafata cikin soro maganar SJ ta dakatar da ni, haka kawai kuma sai naji kiran sunan nawa da yay a karo na farko ya amsa a gaba ɗaya ilahirin jikina, haka kuma naji tamkar sunan a bakinsa aka raɗa shi tun usuli duk da cewar kana jin yanda ya faɗi Sa'ida ba muryar bahaushe ba ne.

Ni kam ban san dalili ba amma tabbas na kan tsinci kaina cikin wani yanayi da na ke kasa fassara shi balle gane masa in har na ga SJ ko naji ƙamshinsa, don hatta ƙafafuna kan yi rawa a irin wannan lokacin hakazalika in rasa natsuwata. A hankali na juyo hannayena na karkarwa riƙe da farantin na kai ƙwayar idona kansa, ya cire gilashin idanuwansa, idanun a ƙanƙance kamar basa gani da kyau, ganin na tsaya yay min alama da kansa na in zo. Na tafi sannu a hankali ina jin kamar zan faɗi ba tare da sanin dalilin wanzuwar hakan ba.

"Ya wuyan na ki?". Idona a ƙasa na haɗiye yawu kafin na iya cewa,"Da sauƙi".

"Es-tu sûr?". Ɗago ido nayi na dube shi, ganin na tsare shi da ido sai ya kulle ido ya kaɗa kansa kaɗan kafin ya ƙara buɗe baki da ƙyar ya ce min,"kin tabbata?".

Na ɗaga kai da cewar,"Ehh yay sauƙi ba kamar da ba".

"Zan iya gani?". Gyalena na ɗaga ina yaye wajen tare da nuna masa, ina ga ganin sacewar kumburin wuyan yasa ya kai hannu ya taɓa babu shiri na wani zabura ina ja da baya saboda yanda zafin ciwon gun ya ratsani da kuma jin hannunsa kamar shokin na wutar lantarki. Ƙwayar idonsa akaina bayan wucewar ƴan sakanni ya ƙara cewa,"kina iya zuwa school?".

Na sauke numfashi tare da cewa,"Ehh yanzu ma daga islamiya na dawo".

Kallona ya tsaya yana yi, wucewar minti ɗaya yay min alama da hannu na in matso kusa, na matso kusa da ƙofar motar da ya buɗe ya ziro ƙafafunsa waje. Ya kai hannu ya ware idanuwana yana duddubawa irin yanda likita yake min, sai da ya gama bincikensa matsayinsa na likitan da ya ajiye aiki saboda saɓanin da ke tsakaninsa da mahaifinsa kana ya ce min.

"Jinin ya É—auke gaba É—aya, kar kina wasa da magani please".
Chapter 1 · 0% Book details