Sashe 75
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A mota ina ta ganin kiranta na ƙi ɗagawa, nayi jugum kamar wata mara lafiya haka na koma, tsabar nayi nisa a tunani ma me adaidaitar na tambayana canji ne a hannuna amma ina ban san yana yi ba har sai da matar da ta sauka ta taɓo ni, nayi firgigit na buɗe jaka na miƙa masa, su biyun suka ce min ya kamata na rage tunani kar hakan ya zamar min illa, kai kawai na kaɗa musu, to ni ban san ma tunanin me na ke yi ba, na dai san kawai na bar hayyacina ne, amma na rasa dalilin da yasa Salim ya tsaya min a rai, akan me zai wulaƙanta ni? Kuma da ya ɗakko bindiga ya aje mene nufinsa? Barazana zai yi min ko kuwa shima zai min tuhumar da bani da laifi akai? Ba zan so shi ba tabbas, kuma ba zan taɓa auransa ba ko za'a tashi duniya, mene tunaninsa zan kuma bari wani ɗa namiji ya wulakanta ni ne? To shi ya san wani soja ni ban sansa ba, sai kawai na rumtse ido sosai ina jin kamar na buga kaina jikin ƙarfen motar ko na samu hotonsa ya bar haska min a cikin ido.
Ba don me napep ɗin ɗan mutunci ba ne tsaf zai iya fusata yay gaba da ni, ko yanzu sai da yasa aka taɓo ni kafin na ɗago na basa amsar,"Cikin layi zamu shiga".
A ƙofar gida na samu Yashaik zaune suna hira shi da su Anas ɗan wajen Baba Tijjani, na durƙusa na gaida su na wuce ciki.
Hayaniya ce ta fara min maraba a tsakar gida, idona ya kai ƙofar ɗakin Ummani, naga dandazon takalma kamar ana biki, yau su Ummani ansha baƙi kenan, daɗin da naji ba kowa a tsakar gidan sai ƴan yara da ke wasan su can wajen barandar shiga ɓangaren Baba Saminu, ba na jin zan iya shiga in ta faman gaisuwa ana faman yi min tambaya kawai na tsallake na shige ɗakina.
Jaka kawai na rataye amma ko kayan jikina ban cire ba na kwanta, ba wai don bacci ba sai don samun sassaucin abinda na ke ji yana taso min a ƙasan zuciya, a haka kuma har bacci ɓarawo ya sace ni sai can cikin bacci naji ana tashina, na farka a firgice gabana na mugun faɗuwa sai ambaton innalillahi na ke yi, dama illar baccin yamma kenan shiyasa duk abinda aka ce maka babu kyau a musulunce to kawai ka haƙura da shi.
Jikina har wani rawa yake yi Maman Khairi ta ruƙoni tana,"Ke lafiya?".
Na buÉ—e ido na kalleta ina haÉ—iye yawu me wahala na ce,"Maman Khairi na tsorata ne".
"Kema ai kin san baccin yamma babu kyau, wallahi da irin baccin yammar nan wata mata bata farka da idanu a buÉ—e ba sanadiyar makancewarta kenan, baccin yamma har hauka yana sawa, sai kita innalillahi da la'ila ha illa anta".
Miƙewa nayi na fita nayo alwala, duk na ruɗe ma ban san magribar bata ƙarasa ba, sai bayan na yo na dawo zan tayar da sallah take ce min,"To ai ba'ai ko kira ba".
Na sauke gwauron numfashi kana na zauna muka shiga gaisawa da ita, sai naji tana wata magana ta daban da ban san ina ta nufa ba.
"Ai bamu san kin dawo ba ke muke jira tun É—azu da tuni mun wuce, to Allah ya sanya albarka ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma sa rabo ne duniya da lahira".
Ta faɗa da murmushinta gami da nuna murna zuwa gare ni, baki na saki ina bin ta da kallo har ta miƙe tana gyara goyon Sufwan, tayi ƙofa zata fita tana ƙara cewa,"To matar soja mu mun tafi, wai sai yaushe za ki ɗinka min kayan Maama ne, ku fa telolin gida tsiyarku kenan".
ÆŠan guntun murmushi nayi na ce,"Kai Maman Khairi zan bawa Babanta ya kawo mata dai in huta da mita".
Da haka ta fice, nima na miƙe na fita da mutuwar jiki raina duk a dagule, na shiga ɗakin Ummani ganina duk suka zubo min idanu, ashema ba wasu baƙi ba ne kamar yanda na zata, ƴan uwan Ummani ne yayyanta da ƙannenta, sai su Maman Yasmin ita Maman Khairi ta tafi, sai kuma wata ƙanwar su Abbaa da suke uba ɗaya Mama A'i ita yaushe rabona ma da ita.
Hajjo da ke gefen Ummani tace,"A'a likita likita an dawo".
Na shiga daga ciki ina duƙawa na gaida su, duk suka amsa min suna tambayana ya wurin aiki. Na yiwa Ummani sannu da gida ina ƙoƙarin miƙewa sai naji suma suna bina da kalmar Allah tabbatar da alkhairi, kaina ya ɗaure musamman da naji Mama A'i na faɗin,"Kun ga yanzu sai na tsokani duk wanda na ga dama a najeriya tunda dai muna da soja a hannu".
Umman Batula tace,"Ai kuwa dai mijin ƴarki guda soja, ai ki taɓa dukka wanda kika ga dama da hujja".
Suka yi maganan cikin raha ana dariya. Umman Batula ta ƙara cewa,"Yanzu ya kama watan gobe kenan?".
Sai Ummani tace,"Ehh to su da ƙarshen watan nan suka zo, kinga ya kama sati uku, amma dai sun tsaya akan cewar zai yi musu magana daga nan zuwa gobe, yace ai ba gaggawa ake ba".
Na rufe baki na buɗe yafi ƙarfin sau goma, yanda na ke kallon mahaifiyar tawa kuwa tamkar ban taɓa ganinta ba a duniya, me kalamanta suke nufi kenan? Sai kawai naga ta miƙe tana faɗin,"Kin ci abinci?".
Na girgiza mata kai ina bin bayanta wajen ficewa a É—akin, yanda na ke tafiya kamar wadda tayi kashin wando ko wadda ba laka a jikinta. A kitchen na sameta ita dai na kasa gane yanayinta amma da bayyanuwar farin ciki a tare da ita.
"Ko ba ki da lafiya ne?".
Maganarta ta dawo da ni daga gajeran tunanin da na tafi, kamar dai na gama fahimtar komai to amma ba hakan ba ne dole ina buƙatar ƙarin bayani, na kaɗa kai ina cewa,"Lafiyata ƙalau, tun ɗazu ma fa na dawo bacci nayi".
"Kuma ki dawo ba ki leƙa kin ce min kin dawo ba, ko da wata matsalar ne?".
Na sake girgiza mata kai alamun a'a amma a haƙikanin gaskiya tambaya ce fal a bakina. Ta miƙo min kwanon abincin tana cewa,"To ungo idan kuma ba za ki ci shinkafar ba akwai sauran gurasa da Umman Batula ta kawo gata can ɗaki ki ɗakko ki kwaɗanta ko ki ci da miya".
Na É—an kalleta na ce,"Gurasar zan ci, amma Ummani to naji kuna yin wata magana ne".
Tayi min wani duba kafin tace,"Maganar me?".
Sai nayi ƙasa da kai ina wasa da yatsu na ce,"Kaman maganar aure kuke yi".
Ta ce,"Ehhh mana, da safe bayan tafiyarki Alhaji Babangida suka kawo kuÉ—in aure da sa rana, amma dai zai neme ki ai ki jira ya dawo kiji daga bakinsa".
Sai naji maganartata tamkar saukar aradu, na ɗago ido wanda tuni ya cika da ruwan hawaye na kalleta na ce,"Ummani kawai sai ya kawo kuɗin aure bai ji ta bakina ba, Ummani tun fa ranar da ya zo bai ƙara nemana ba, kuma ni ban ce masa na amince ba, har yau ban ba shi amsa ba, bafa sona ma yake yi da gaske ba Ummani, ta ya Abbaa zai yarda ya karɓi kuɗinsa".
"Yo shi Abbaanki da yaji ba ki tunkare shi da maganar ba ai zatonsa kunya kike ji, shi yasa ya É—auki shirunki a matsayin ehh, idan ya dawo kya masa bayani ba zai ji daga bakina ba".
Tana gama faÉ—in hakan ta wuce ta barni nan tsaye, hannu nasa na goge hawayena, wacca gurasa kuma zan iya ci bayan mugun soja na neman sakani a tsaka me wuya, Haka ake aure dama babu soyayya? Haka ake aure babu fahimtar juna da amincewar juna? Haka ake aure da nuna isa da gadara? Me ya taka kuma me yake shirin aikatawa?
Ɗaki na wuce jiyo wayata na ringing, Hassana Tijjani ce yaushe rabona da ita, kamar ba zan ɗaga ba saboda kar taji yanayin muryata ta kama tambayata menene, sai daga baya kawai na ɗaga ɗin dai, bayan na amsa sallamarta sai ta kama ƙorafin amana bata ce haka ba, bata yi tunanin bare na ɗauketa ba, yanzu zan yi aure shi ne ban faɗa mata ba, to taga invitation a status ɗin Safiyya kuma ta gode, ba zata ɓoye min ba zancen gaskiya bata ji daɗi ba.
Ba ta jira cewata ba kawai ta kashe wayarta, ni kuwa ina zan iya bin bayanta in bata haƙuri alhalin ni kaina ba cikin jin daɗin na ke ba, bata san nima rashin kyautawa aka min ba, sai kace wata ƙaramar yarinya za'a nemi ayi min auren dole. Tunawa da Safiyya raina ya ƙara tugunzuma na ɗauka wayar na danna mata kira, tana ɗagawa ban jira cewarta ba cikin masifa na ce mata.
"Yanzu abinda ku ka yi min ke da Yayan na ki kun kyauta kenan? Ke tsabar zaƙewa ma har da su zuwa kina faɗawa duniya, yaushe nace masa na amince zan aure shi da har ya iya rawan jikin kawo kuɗin aure? to ni ba zan aure shi ba ki faɗa masa, ba zan auri wanda bai da kulawa ba, idan ma ya aure ni to ya tabbata gangar jikina zai aura ba zai samu soyayya daga gare ni ba kamar yanda nima ba zan yarda da soyayyar dole ba, kuma ina faɗa miki tsakani da Allah banji daɗin abinda kika min ba kuma ba ki kyauta min ba, wannan ai shiga rayuwata ne".