Sashe 21
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau da muka tashi jikin Abbaan da sauƙi, haka yana ɗan magana yace ayi masa kaza, ko kuma yana son kasa. Har ma da yaji maganata yake cewa har yanzu ban tafi gida ba, Ummani ranta a dagule tace,"Kai dai kaji da ciwon da ke damunka".
Ummani kam yanzu haushin Nazifi take yi sosai, haushin da na san ba lallai ta taɓa daina ganinsa da abubuwan da yake min ba, don ita tana da ruƙo, na faɗa muku a baya tana da tsananin haƙuri amma idan ta ƙullaci mutum akan abin da yaywa ƴaƴanta tofa sai ta Allah. Balle yanzu da ya ƙara nuna mata su ɗin ba komai ba ne du da suna iyayen matarsa.
Yau É—in da Abbaa yaji daÉ—in jikinsa sai ga Æ´an dubiya nata zuwa, wannan ya shigo wannan ya fita, kowanne ya zo da É—an alherinsa. Dama ciwon nasa na damuwa ne kwana biyu kasuwa shiru idan ya fita haka yake dawowa, shi kuma ba ya iya fitowa yace da Æ´aÆ´ansa su taimaka masa ko ya faÉ—a musu ga halin da yake ciki, a bikina kawai aka yi hakan, amma Ummani ce min tayi sun sha yini da yunwa sai idan Maman Yasmin ta kawo abincin rana da ke kullum sai ta aika, to shine suke tattala shi aci har dare.
Dukanmu ba ƙaramin daɗi muka ji ba da har yace a tayar da shi ya zauna, na saka masa pillow a baya ya jingina da shi. Ya buƙaci na zuba masa tuwon masara da miyar kuɓewa ɗanya da Anty Khairi ta zo da shi.
Da kaina na ba shi yana ci ya kuma ci sosai dan Æ´ar kaÉ—an ya rage malmalar, yasa Abbayo ya kama shi ya taimaka masa zuwa banÉ—aki yayo alwala, haka yazo a lokacin nan yay ta ramakon sallolin da ke kansa, bai tsagaita ba sai da ya rama sallolin kwana shidan da yay a kwance.
Ummani dai sai ta kalle shi in ga ta kaɗa kai ta faki idonmu tasa hannu ta share ƙwallarta, cuta ba mutuwa ba amma ni kaina har na sallama da Abbaa, don ko yanzu irin abubuwan da yake tamkar mai yi mana bankwana. A hankali na ke sa gefen hijabina na goge hawayena.
Abbaan da kansa yake jan mu da magana har dai muka saki jikinmu saboda yacca yaga duk mun ƙara damuwa jikkunanmu sun yi laƙwas.
Da zolaya yake cewa da Ummani,"Hajiyar Salman ana tsoron zaman takaba ne".
Tace da shi,"Kaga ni dai rabani da wannan zancen. Naga alamun ma ka samu lafiya bara na yiwa likita magana ya zo ya bamu takardar sallama".
"Ehh fa dai kirawo shi ɗin su bar cin kuɗin Ƴaƴana haka. Amma kafin nan kunto kuɗaɗen da ke bakin zaninki".
"Ehh lallai kaji sauƙi tun da har ka iya saka ido. Mutum duk ya ɗagawa mutane hankali, ga ƴarka nan duk ka ramar da ita, ko da yaushe a kuka take abinci bata iya ci".
Abbaa ya zuba idanuwansa akaina ko ƙiftawa bai yi, ni kuma ina ta ƙoƙarin gusar da tsantsar damuwar saman fuskata ta dole, don bana so ya hangi abin da zai ɗaga hankalinsa tun da gaskiya rabon da nace na zauna irin haka gabansa yay min kallon ƙurilla da fahimta irin wanda yake min yanzu anfi shekara uku, kuma don dai yaji daɗi sai na ɗago ido ina kallonsa da murmushi na ce,"Sannu Abbaana Allah ya ƙara maka lafiya".
Ya amsa da amin yana saka min albarka gaba ɗayanmu da su Anty Khairi. Ya kalli Ummani yana ce mata,"Kinga da Sa'ida ta zama likita irin wahalhalun asibitin da muka sha da duk mun samu sauƙi, to Allah bai nufa ba".
Ummani tace,"Umm Kana naka Allah na nasa, bai rubuta faruwan hakan a kundinta ba ne".
Nasa hannu na goge hawayen da ya zubo min. A hankali naji Abbaa na cewa,"Shi fa gidan aure gida ne na yaƙin neman Aljanna, sai mace ta yi haƙuri bana wasa ba kana take iya jin daɗinsa har ta iya samun Aljannarta. Na jima ban miki kallo irin wannan ba Sa'ida, sai dai yau ɗin fuskarki ta shaida min kina cikin wani hali a matsuguninki, wannan ramar taki ba ta sauƙi ba ce, na tsorata da ita ƙwarai, ina ga ba kiga yanda kika ƙare ba ne ko? Na san mahaifiyarki na sane da duk irin halin da kike ciki, nima kuma daga baya duk na fuskanta, na san kin san waye mahaifinki a ɓangaren iya takun yin bincike. To kamar yanda na ke faɗa miki ko da yaushe a baya yanzun ma zan ƙara nanata miki. Ki ƙara haƙuri akan wanda na san kina yi, kiyi haƙuri kiyi adu'a sune kawai jin daɗinki, haƙuri ba ya yawa ba ya janyo danasani da nadama, haka adu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza, Sa'ida babu wanda ya yake nasara ba tare da yay haƙuri da juriya ba, don haka ki zama me tawakkali da duk halin da kika tsinci kanki kin ji. Sauƙi a wurin ubangiji ya ke, tsanani da akasinsa basa dawwama, da sannu labarin zai canja komai ya shuɗe".
Ina hawaye sosai na ce,"To Abbaa ka yafe min, don Allah ka yafe min akan...".
"Ni ai tuni na yafe miki. Amma a dinga kulawa, a dinga kai zuciya nesa, a daina ɗaukar huɗubar shaiɗan, in ka cutar kaima za'a cuceka. Allah yay miki albarka, Allah yay miki albarka ya lulluɓe dukkan rayuwaki da farin ciki mara yankewa".
Na ce,"Tom Abba, na gode Allah ƙara lafiya yaja kwana".
Shiru na ɗan sakanni ya ƙara cewa,"Ya wajen abokiyar zaman na ki, kuna dai zaune lafiya ko?".
Na kasa riƙe kukan da ke maƙale, ina fitar da shi na ce,"lafiya muke Abbaa".
Sai naga ya É—an murmusa yana jijjaga kai kafin yace,"Ma sha Allah, sai aci gaba da zama lafiya kin ji".
Da magriba sai ga Nazifi ya zo duba Abbaa, ni na fita na shigo da shi. Ummani dai babu sakin fuska ta amsa gaisuwarsa sama sama, Abba yace da shi ya zauna. Yanda yake yi dai irin a gurguje yake don ina lure da shi, tun da yake zuwa bai taɓa zaman minti biyar ba, da ya zo an gaisa yace ya me jiki aka ce da sauƙi zai ce to ya tafi.
Abbaa ya shiga tambayarsa akan zancen plazarsa yace ai Alhamdulillahi adu'arsu ta amsu komai yanzu ya daidaita, Abbaa na nuna jin daÉ—insa yake ta jero masa adu'a da fatan alkhairi.
Yana daÉ—a dubansa yace da shi,"Amma dai baka samun wata hatsaniya daga wurinta ko? Yanzu ba ita kaÉ—ai ba ce kuma nasan lamarin Æ´aÆ´anmu a zama irin haka".
Kansa a ƙasa yana juya muƙullin hannunsa, wani abu yake so yace da dukkan alama, to ƙila sharrin ne bai gama haɗuwa a ran nasa ba shiyasa yay murmushi kawai bai ce komai ba.
Abba ya ƙara cewa,"Hakan ya shaida min akwai matsalar kenan, dama na san dai kana haƙuri ne, to ai na faɗa maka duk san da tayi maka laifi ka zo ka sameni hakan umarni ne ba ƙararta ka kawo ba, idan tana ganin tafi ƙarfinka ai mu bata fi ƙarfinmu ba. Allah yay maka albarka, haƙurin da ake Allah ya bada lada, sannan ayi ƙoƙarin kwatanta adalci nauyin da ke kanka yanzu yafi na baya, tsakiyar mata biyu kake don haka sai kayi da gaskiya saboda lahirarka".
Kansa na ƙasa yake cewa da Abbaa zai wuce. Ba dan idon Abbaa ba da bai isa na bi bayansa da kallo ba, ba da son raina ba ha na miƙe na fita raka shi, ko ƙofar ward ban ƙarasa ba na juyowata dama yana gaba ne ina bayansa kuma da nisan tazara tsakaninmu. Ina komowa Abbaa yace da ni,"Ba tare zaku wuce ba?".
Maƙot na haɗiye dunƙulen yawu na ce,"A'a Abbaa, ai da yake gidan ma babu kowa itama an kwantar da ita a asibiti zata haihu".
Ashe tsautsayi ne ya ɗebe ni nayi wannan maganar, Ummani nata min sigina ban lura ba. Sai ce yay to ai wannan rashin hankali ne ace abokiyar zamana na asibiti zata haihu ban je na dubata ba kwata kwata, ban da abuna ma ai sai ace baƙin ciki na ke da haihuwartata. Saboda haka na tattara abin da zan tattara na bi bayan mijina shi kam ya yafe zaman kula da shi ai yaji sauƙi. Idona ya cika da tarin hawaye, babu abin da zan ɗauka dama, Ummani na kallona da tausayawa tace,"Abbansu da ka barta sai ta tafi da safe. Ko abinci ma bata ci ba".
Ai fa nan Abbaa ya hauta da faÉ—a sosai akan me yasa ita bata san abun da ya dace ba, dama su iyaye mata sune ke É—aurewa Æ´aÆ´a gindin yin abin da suka ga dama a gidan aure, kuma sai auren ya mutu su zo suna kuka ana ganin laifin miji. FaÉ—a fa kamar ba majinyacin da ke kan gadon asibiti ba.
Ni dai ina ta kuka na ce,"Ummani sai an bani kuÉ—in mota na san yanzu ya rigada tafiya. Kuma ma ban san asibitin da suke ba wayata babu kuÉ—in da zan kira shi na tambaye shi".
Ana haka Abbayo ya shigo, Abbaa ya kalle shi yace,"Kai da kuÉ—i a hannunka?".
Yace,"Ehh akwai". Ya faÉ—a yana saka hannu a aljihu ya É—ebo kuÉ—i.
Abbaan yace da shi,"Nawa ne?".
Ya shiga ƙirgawa kafin ya ce,"Dubu ɗaya da ɗari uku ne".
Abbaa yace,"To ara min ka bawa wannan yarinyar. In wayarka da kuÉ—i kira mata mijinta".
Abbayo yace,"Ai da zan shigo na gansa bakin motarsa, ina ce ma ko ita yake jira".
"Ehh kira mata shi É—in dai".
Abbayo ya miƙo min wayarsa na saka lambar na kira, kamar me jiran kiran kuwa bugu ɗaya ya ɗauka duk da na san baida lambar, ya ɗaga yana sallama, na amsa ina cewa da shi,"Ka tafi ne?".
Jin muryata munafuki sai ce yay,"Ya za'ai na tafi kema ai kin san jiranki na ke yi. Kin san an kusa shiga da ita É—akin tiyatar ya kamata muje da sauri".
Ƙit na kashe wayar kafin ya ƙara karanto abin da zai haɗa ni da mahaifina, na miƙawa Abbayo wayar hannuna na karkarwa ganin kallon da Abbaa ke watso mini. Nayi msu sallama zan wuce ina maidawa da Abbayo kuɗinsa sai Abbaa ce yay.