Sashe 19
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗa yana sumbatarta a gefen baki, tayi murmushi kawai tana kallonsa, ya kamo hannunta suka isa bakin gado ya zaunar da ita, har ta zauna sai kuma tayi saurin dafa shi ta miƙe jin kamar an tsikareta, nan ta kama yi masa ƙorafin irin ciwon da take ji a jikinta, shi kuma sai faman lallashinta yake kamar zai ciro cikin ya mayar jikinsa.
Hankalinsa ya tashi ganin ta kasa zama, ya fita a ruÉ—e ya kira Inna wadda tana zuwa ta dubi Zahra'u tace da shi,"Ka kwantar da hankalinka kai kam, ba haihuwar ba ce kawai dai alamominta ne na ana kan hanya. Itama dai don raguwa ce".
Innar ta ƙarasa maganar da zolaya, Zahra'u tace,"Ai ko dai Inna a irin wahalar da Babyn nan ke bani Allah ni ba ƙaramar jaruma ba ce".
Innar ta fita tana murmushi, shi kuma ya riƙe hannunta sunata kaiwa da komowa a ɗakin da yake ƙato ne gari guda, kaf ɗakunan gidan albarka, a hankali kuma sai ta fara jin daɗi har da kanta ta buƙaci zama. Ta zauna tana sauke numfarfashi, shi kuma ya duƙa a gabanta yana ta shafa cikin yana kallon fuskarta.
"Sannu Sweety".
Hararar masoya tayi masa, ya kama hannunta ya ruƙo cikin nasa sai zuba yake mata. Idonsa ƙyam kan cikin yake cewa,"Yanzu Sweety da gaske ƴaƴa biyu ne a nan?".
"Ummm kuma duk masu kama da kai ba".
"A'a ai dole a samu É—aya me kama da ke, ni nafi so ma suyo kamanninki, amma dai shi abokina kar yay gajarta irin taki".
Dariya tayi tana faÉ—in,"Ohh ji son kai, kana jin irin zagin da Æ´an gidanmu ke min akan rashin tsayi kuma shine zaka so princess ta biyo ni. Aa itama gwara tayi tsayi kaman naka kasan fa ance doguwar mace rabin kyau. Kuma sannan ma ina so tayo irin idonka kaga ai ka fini manyan ido naka sexy eyes ne suna da kyau a wurin mace".
Dogon numfashi ya sauke yace,"Sweety kinga ni ban samu nayi karatun boko ba, wanda kuma hakan ke damuna. Sam ba zan yi saken da za'a ce Muhammad bai yi karatun boko ba, dama na addini wannan kam gidan suka tarar zan ɗora shi akai Sweety, zai gaje ni in sha Allahu, sai dai ina roƙonki da ki taimaka min wajen tsayawa akansa kiga boko ta kafu akansa".
"Honey son kai? Komai sai kace shi baka saka Pricess".
"Ai har da ita na ke nufi. Kinga tun yanzu ma ya kamata muga irin makarantar da ta dace a sa su".
Wayarsa ya zaro a aljihu ya bata yana cewa,"Shiga goggle ki dudduba mana tsadaddun makaratun ƙasar nan, amma wanda ake karatu haiƙan. Ɗazu na gwada yi to ban san me zan rubuta ba, ko ana rubutawa da hausa?".
"Hmm Honey turancin nan fa babu wahala. Ka dai ƙara dagewa akan Jammaje Academy ɗin nan zaka gani har sai kazo ka fini, turanci ai yare ne kana sa kanka zaka koya. Kuma Honey batun school na su ai da ka bari sun zo duniyar tukunna ko".
Fuskarsa ya shafo yana cewa,"Kin san wani abu ma. Ki binciko ƙasar da kike so na kaiki ki sami hutu kamar na shekara guda, kina buƙatar hutawa Sweety saboda ɗaukar cikin yara biyu ba wasa ba ne".
Haka fa suka zauna suna ta lissafi da tsarawa akan rayuwarsu da yaran da za'a haifa, shaf ya mance yana da wata matar ma a gefe, wadda ko tunanin ma Allah ya iya kawo mata haihuwar bai yi, idan ta haifa É—in kuma bai da wani abu da zai É—aga yace ya bawa yaran wajenta don komai ya tattara ya baiwa Zahra'u, har ATM ya É—auko ya bata yace ta ajiye a wajenta na Muhammad ne, duk wata zai dinga saka masa kuÉ—aÉ—e a ciki, ba ya so É—ansa yay irin rayuwar wahalar da yay a baya.
Ita dai sai dai tace to, sai ita ta ankare da tafiyar lokaci ma tace da shi lokacin sallar isha'i yayi, ya fita kamar ba zai fitan ba, lokacin da ya dawo ya sameta tana waya da Iyam.
Dama da zai wuce masallaci ta kira shi ya haɗata da ita sai yace mata yaje masallaci, shine ita kuma ta kasa haƙurin jiran ya dawo ta ciyo bashin kamfani ta kirata, don ko iya jiran a zo a saka mata kati ma ba zata iya ba, tunda ta kira take ta tambayarta jikin nata tana faɗa mata ai ta kusa dawowa cikin satin nan ma kuwa saboda ta karɓi haihuwar jikanta.
A ƙasan zuciyar Zahra'u tace mahaukaciya ce ta haifan zan yi irin haihuwarku ta marasa ilimi, ke har tunanin ma zan haihu a gida kike da kika fara lissafin za ki karɓi haihuwata, ai wallahi ko da wasa. Dawowarki ma ni bana so don dama ba son zamanki na ke a gidan ba, lokaci ma na ke jira ki koma matsuguninki.
Bayan gama wayar tasu ta ankarar da Nazifi tafiyar lokaci, ɗan tsaki yay ɓacin rai na ƙara wanzuwa a fuskarsa ya ce,"Sweety ba na son matsawa daga kusa da ke. Ko na tafi ma gangar jikina ce kawai acan, Ko in kira Sa'ida in tambayeta ta bar mana kwananta? Kinga tana da sauƙin kai zata amince".
Ta ware ido tana kallonsa, cikin ranta ta ayyano idan ita Nazifi kewa wannan ɗibar albarka ai tuni ta zagwanyar masa da fatar jiki. Ko ranar da ya mari Sa'ida a gabanta sai da taji lamarin har ƙasan zuciyarta don sosai ta bata tausayi, Sai dai a nata ganin Sa'idan ce tayi saken da har yake mata abubuwan da yaga dama, da ace tun fari tana taka masa burki wataƙila ya raga mata, wai ma har yana faɗin zai iya tunkararta ya tambayeta ta bar masa kwana akan kishiya? To ba rashin haihuwa ba ko rashin me take yi ya isa ya gwada mata haka in bata masa ɗanyan kai ba.
Hure mata iska a ido yay da ƙara cewa,"Ko kin fi so na tafi ɗin? Amma dai ki sani farin cikina da duk jin daɗina anan yake, can wallahi takura kawai na ke yi. Ni dai kima bari na kirata na nemi izininta za kiji da tace da ni to".
Tayi saurin dakatar da shi da danna kiran da yake shirin yi a waya tace,"Amma Honey zamu yi hurting ɗinta ai, kayi haƙuri kaje kar mu ke shiga hakkinta. In dai Babynka ne idan ya zo ma sai kake tafiya da shi can, nima don babu yanda zan yi ne da na maƙale a jikinka mun tafi tare domin bana son rashin jin daɗin da kake yi. Kaga yanzu ita sai ta ƙullace ni take zaton ni ce na ke hanaka zuwa wajenta, kuma zuciya bata da ƙashi sai ta iya ɗarsa mata ta cutar da ni kuma ga Twins tare da ni".
Ta faɗa da nuna damuwa sosai, ai ko ya shiga jijjiga kai yana faɗin,"Ta cutar da ku? Ai kuwa da zaman duniyar nan ya gagareta wallahi, akanki da Ƴaƴana?".
Sai da ƙyar dai Nazifi ya iya tashi ya tafi ransa duk a dagule. Har sai da yaje ya faɗawa Inna kome ake ciki ayi gaggawar kiransa komin dare.
Zaune muke ni da Saudatu da Rumana muna ta hira, sosai zamanta kam ke ɗebe min kewa har bana son ma lokacin komawarta yayi, shiyasa idan aka kira ni daga gida sai na ƙara narkar da murya don su shaida sauƙi fa babu shi, don haka suma bar kiran ta dawo.
Agogo na kalla naga har ƙarfe goma, na jijjiga kaina haɗe da yin murmushin takaici. sai ga kiransa ya shigo, haushi yasa nayi biris da kiran naƙi ɗagawa, ban da ya raina min hankali sai yanzu ƙarfe goma tukunna zai baro wajenta, ko da akai magriba naje ɗakin nasa ban gansa ba tsammanina ya tsaya masallaci ne , haka nayi ta zaryan hawa da sauka wai sai can dawowan da zanyi na jiyo muryarsa acan ɗakin nata yana faɗa mata shi fa yana ganin za'a ƙara yawan kwana domin gaskiya kwana biyu nayi masa kaɗan a wajen kasancewa tare da ita, ita kuma me ta faɗa masa Allah masani sai jinsa nayi yana ƙara cewa to ai ita akwai yaronsa tare da ita zama da ita yafi zaman wajena muhimmanci.
Irin wulaƙantanin da yake da nuna mata rashin darajata a wurinta sai dai Allah ya saka min kawai. Don ko satin baya sai da ta yaɓa min magana kan ai yanzu ita ce matar so a gidan, miji bai taɓa ɗaga mata murya ba balle yasa hannu ya mareta ko yay mata gorin haihuwa, idan ina taƙama da Uwar gida ai suna ne kawai domin yanzu ita ce da gida, ranar maganganunta sun ƙona min rai sosai sai dai ban bi ta kanta ba, Saboda banga laifinta ba kome ta gaya min shi yaja min, shi ya bata ƙofa.
Rumana tana dubana tace,"Abba yana kiran waya".
Ban amsa mata ba na miƙe na shiga banɗaki, lokacin da na fito sai ga shi ya turo ƙofa ya shigo yana kiran sunana, ban amsa ba rai a haɗe kamar hadari. Saudatu ta gaida shi ya amsa yana tambayarta ina ina, ta kallo ni sannan ta kallesa tace,"Dama ta shiga banɗaki ne amma gata nan ta fito".
Niko na tako kamar ban san da zuwan nasa ba ina goge ruwan fuskata na nufi wadrobe, Cikin muryar ɓacin rai yace,"Ba ki lura da ni ba ne?".
Ciki ciki na ce,"Na ganka mana".
Hakan sai ya ƙara ƙona ransa ya hau bambami, zuciyata ta sosu na ɗora idona kansa, na lura yanzu idan zai yi min faɗa yaci mutuncina idan bai ɗaga muryar da matarsa zata ji ba hakan sam bai masa daɗi ba, ko kuma yayi a gabanta shine kwanciyar hankalinsa. Ko bama ita ba aganina ba dacewa ba ne ya ke min faɗa gaban Saudatu.
Sauri sauri nayi wajen zarar kaya, jikina har rawa yake ban ma iya rufe murfin ba na tafi da sauri na fice a É—akin na barsa nayi É—akinsa, duk da cewar ba'a son raina ba don da niyyata idan ya neme ni zan faÉ—a masa ya koma can inda ya baro zai fi masa dan acan aka damu da shi ni bai gabana.