← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 113

Sashe 76

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai kuma sai na fashe da kuka ina ce mata,"Ni fa ban ce masa ina sonsa ba Safiyya, har yau ban yanke decision ba, ni ban san me na ke ji game da shi ba, idan ina sonsa ma ba ke za ki fara sani ba, Safiyya tunanina matarsa taya zata yarda ta zauna da kishiya? Kishiyar ma bahaushiya, bayan naji ana cewa matan Ƙabila mugwaye ne, tarwatsa aure suke yi basa yarda su zauna da kishiya, kuma babu abunda suka iya sai mugun asiri da makirci, a hakan to kike so na aure shi? Ke da kike sona ya kike neman jefa mi cikin rana, me zan yi da auren ƙabila fisabilillahi, kuma ƙabilan ma me mata, Shikenan sai na ƙare a aure ina fitowa ina faman yawon zawarci".

Ina yin shiru tace,"Madallah Na gode Sa'ida, na gode sosai da ci min fuska, ba laifinki ba ne laifina ne da na nace miki, kuma na ɗauke ki ƴar uwa har na ke so ki shigo cikinmu, to Alhamdulillahi duk da muke ƙabilar mu tamu zuciyar a wanke take fesss, ba ma nufar kowa da sharri balle mugunta sai alkhairi, kuma ita kanta Anty Kudrat ɗin da kike ma mummunan zato kin ɗauka hakkinta wallahi, kuma kar ki damu Brother Salim ne bai da matsala zan sanar masa da duk abinda kika faɗa, muma ai da zuciya a ƙirjinmu inda ake son mu nan muke zuwa, saduwar alkhairi...".

Ƙit ta kashe wayanta, ni gaba ɗaya ma ban san nayi wancan katoɓaran zancen ba sai yanzu, na yi ta bin bayan kiranta taƙi ɗagawa. Haka dai na samu na tura mata saƙon ban haƙuri da shaida mata ba yanda ta zata ba na ke nufi.
Maman Yasmin ta shigo ta sameni tana ce min za su tafi, yanayina yasa ta zauna tana tambayana meke faruwa, ni da ya kamata a ganni farin ciki kuma sai a ganni a akasin hakan.

Ganin idan nayi shiru zan cuci kaina nace mata,"Maman Yasmin ni fa bana da buƙatar na sake yin aure, nafi so inyi zamana a haka, zaman gidan iyayena yafi min daɗi da kwanciyar hankali, in je aikina na dawo nayi sana'ata na fi farin ciki da hakan".

Sai ta numfasa tana dafa kafaɗana da cewa,"Sa'ida ya kamata ace kin mance baya kin fuskanci gaba, ke ba ki ga sauyin da Allah yay miki ba ne? Kin taɓa tsammanin za ki taka wannan matakin ne? Ba fa iyayenki da na ki ba kawai hatta wasu mora suke daga jikinki, to ko wannan ba ya isa ki kyautatawa sabuwar rayuwar auren da za kiyi zato me kyau ba, kuma ki kalla fa wanda Allah ya aiko miki, wallahi Abbaan Yasmin ce yay da Abbaa ya tura su bincike kar kiji yabo da kyakykyawan shaidar da ake yi masa".

Sai tayi shiru kafin ta sake cewa,"Kuma fa bacin haka kefa macece me lafiya, ina za ki iya riƙe kanki? Dole kina da buƙatar abokin rayuwa, wallahi wallahi zaman aure shi yakamace ki shine mutuncinki da ƙimarki da darajarki".

Na goge hawaye na ce,"Na sani Maman Yasmin to amma ni ina gudun matsalolin rayuwar ne, kar lamura su zo su taɓarɓare min kamar wancan, kinga har faɗa masa nayi ina da matsalar rashin haihuwa amma bai ɗauki zancen nawa da muhimmanci ba".

"Kinga yanzu dai magana duka ta ƙare, ba ki ɓoye masa komai ba kin sanar da shi kin fita hakkinsa, kuma magana ma har ta kai ga an saka rana, don haka kawai ki durfafi adu'a ki faɗawa Allah".

Haka dai tayi ta ban shawara tare da kwantar min da hankali sannan daga bisani ta tashi suka tafi don Yashaik nata aikowa akan ta zo ta ba shi maƙulli idan anan zata kwana.

Bayan fitarta naji ƙwala kiran Abbaa, na miƙe da azama na sanya hijabina na fita zuwa ɗakinsa, na sameshi ya gama cin abinci suna zaune suna magana shi da Ummani, daga gefe da su na zauna nayi masa sannu da zuwa, ya amsa yana kai hannu ya rage volume ɗin rediyon da yake ji.

Ƙirjina sai bugawa yake yi kamar wadda ke jiran zartar da hukuncin laifin da ta aikata. Abbaa ya kalle ni yana cewa,"Kun yi magana da Babarki?".

Na ce,"Tace min dai sai ka dawo".

Ya jinjina kai kafin ya ce,"Ɗazu iyayen yaron can da ke neman aurenki sun zo, sun kawo kuɗin aurenki da na kayan sa rana da kuma kuɗin lefe wanda haka suke yi a al'adarsu, sun bada miliyan ɗaya da rabi na kuɗin kayan lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin kayan sa rana da kuɗin aure, gaba ɗaya dai miliyan biyu suka bayar, to na so ma su rage don ba yanda ban yi da su ba suka ce a'a hakan za su bayar, to ga kuɗi nan dai na karɓa, sun kuma yi batun wata guda nace musu a'a muna buƙatar lokaci duba da yanayinmu, to kuma ɗazu Kakanku sai yace wata guda ɗin yayi, nama kira su na sanar musu".

Duk sai naji jikina yay sanyi, da gaske Aure zan ƙara yi bayan alwashin da na sha na ni da aure har mutuwa, yanda na ke jina kamar dai ba ni ba, A hankali ruwan hawaye na kawowa idona nace,"Tom Abbaa Allah ya kaimu".

"Kun yi magana da shi Salim É—in?".
Ina girgiza kai nace,"A'a".
"To yanda ku ka yi sai ki faɗa min amma kar ya wuce zuwa gobe, ga kuɗinki nan zan bawa mahaifiyarki amana bana so a ci musu ko ƙwandala, yanda suka bayar da sunan abinda suka ce haka na ke so ayi amfani da shi, Allah ba zai hana yanda za'ai ayi miki sauran buƙatu ba, sai kuje wajen Saleh kafinta ki duba kayan ɗakin da kike so".

Nace,"Tom Abbaa".

Da haka na miƙe nayi musu sai da safe na wuce ɗaki. Ni dai tun bayan dawowana daga wurin Abbaa kuka na ke yi sosai tamkar wadda aka yiwa mutuwa ko wani abun alhini ya sameta, har Ummani ta shigo ta kore min sauro ta ɗauka abu a firij ta fita ban ɗago ba haka ina ji taja ƙofa ta rufe tana faɗin,"Idan kin gama aikin wahalar sai ki tashi ki saka sakata, ba kya son nasa kika ja baki kika yi shiru saboda gulma, yanzu da kika je ai da sai ki faɗa masa, kina neman ƙaryata kanki akan gaskiya, ni dai Allah ya bamu alkhairi".

Ai kamar ta tunzura ni fa sai kuka, ni fa bana son Salim, kuma bana ganin laifina don naƙi aure, haka kowa ma kar yaga laifina, auren nan na yi banji daɗi ba, na shekara goma har da ƴan kai amma jin daɗi da farin cikin da na tsinta a cikinsa ba za su wuce ƙirgen yatsu ba, nayi bautan aure gwargwadon iko, na kasance irin macen da ake kwaɗayi da fatan samu a gidan aure, amma sai zaman auren nawa ya kasance da wulaƙanci da tozarci, to tsakani da Allah ta ya zan sake sha'awar komawa duniyarsa? Wallah ko da naji cewar ina so ko saboda mahaifiyata da naga ta damu, idan na tuna batun haihuwa duk sai in ji inaaa ta ina zan soma? Ba zan iya ba, wahalar da na sha a baya ma ta isa, ina ni ina kuma auren me kuɗi su ci mutuncina shi da danginsa, balle ma me mata har da ƴaƴa.

Ban gaji da kuka ba har ƙarfe daya, in kukan in saƙe saƙe da babu warwara, a lokacin ne kuma na miƙe na fita na yo alwala na dawo na kulle ɗakin, tun a wancan ranar sai a yau Allah ya nufa zan yi sallar istikara, bayan na idar na jima hannuna sama ina hawaye ina roƙon Allah akan ya shiga lamarin auren nan, idan alkhairi ne ya tabbatar idan babu alkhairi ya kawo sassauƙar hanyar da za'a fasa shi ba tare da anyi nisa ba.

Haka na raya daren da sallah da karatun ƙur'ani tare da tarin adu'oi, bayan nayi sallar asuba ne kuma bacci me daɗi ya zo min, Allah ya so ba morning duty gare ni ba evening ne da ban san ya zanyi da tarin baccin da na ɗauka ba. Cikin bacci naji ƙarar wayata, a firgice na buɗe ido ina saurin miƙewa zaune tare da kai hannu na rarumota.
Na maida kai na kwanta a sa'ilin da kiran ke yankewa, kuma ina lumshe ido da zummar komawa kiran ya daÉ—a shigowa nayi azamar É—auka na kai kunne.

Da kasalalliyar muryana na masu bacci na sauke numfashi tare da yin sallama. Daga can ɓangaren ma naji an sauke numfashi kafin a amsa sallamar.
"Na katse miki bacci, bari na ƙyale ki idan kin tashi ki kira ni".
Kamar a mafarki haka naji muryan nasa cikin turancinsa me daÉ—i, kuma tuni na buÉ—e ido ina saurin dakatar da shi da cewa,"Ai na tashi ma, kai ne?".

"A'a Sa'ida ne".
Murmushi ya suɓuce min me sauti, haka kawai sai naji kamar daɗi na ratsa ni. Ina miƙa nace,"Ina kwana".
"Ba zan amsa ba".
"Saboda me?"
"Ba ki san kin yi laifi ba kenan?".
"Ni ban yi laifi ba, wa nayi wa?".
"No shikenan ai, ban bin baya ni gaba na ke tunkara".

Kawai sai na tsinci bakina da faɗin,"Kayi haƙuri".
Yay shiru na sake cewa,"Kayi haƙuri don Allah".

Sai yace,"Ya isa haka, zan zo gida anjima".
Zuciyata naji ta motsa, sai nayi shiru bance komai ba. "Ba kiji ba ne".

"Zan fita aiki ne by 3".
"Tom shikenan ki shirya sai na zo na kai ki".
"Kaii ai Abbaa ba zai bari ba".
"Zai bari, zan faÉ—a masa".

Na ƙarasa buɗe idanu babu shiri nace,"Kace masa me?".
"Zan kai matata wurin aiki".

Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Ya sake cewa,"Kin yi break fast?".

"A'a yanzun ai ka tashe ni".
"Har eleven kina bacci, kin kwana kina kuka ko?".

Sai nayi ƙasa da murya da shagwaɓewa nace,"To ai kai ne baka yi shawara da ni ba".
"Ai nayi shawara da zuciyarki shiyasa". Ya sauke numfashi kana ya ƙara cewa,"Ki tashi ki ci abinci haka, bana son zama da yunwa".
Chapter 76 · 0% Book details