← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 113

Sashe 78

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar dai wata zautacciya haka nayi wankan nan na fito sai aikin imagination na ke ina ta murmushi, yau ɗin dai kana ganina kasan cikin farin ciki na ke sosai, kamar ma ranar ɗaurin auren, annurin fuskata sam yaƙi ɗaukewa duk murnar zuwan Salim ne, kwanana tara kenan ban gansa ba, na riga na saba duk kwana uku yake zuwa, waya ma bama samun damar yi sosai, idan ya tasheni da safe sai zan kwanta zai ƙara kira, nan ma ba zamu jima ba 2-3mints ne zai ce naje na kwanta yana cikin aiki ne.

Sun je taro ne can garin Ekiti, suna tare da shugaban ƙasa sun masa rakiya, kuma a can ɗin suna tattaunawa ne akan matsalar tsaro na ƙasar nan, to duk basu da wani isashshen lokaci, a hakan ma yau ɗin sato hanya zai yi ya taho, yace shima ya gaji da missing ɗina, ƙwayar idonsa kullum zafin rashin ganina take yi, kuma idan yay kuka duk bai da me lallashinsa.
Ina zancen zuci sai ga kiransa ya shigo, naji ƙirjina yay duka, wani sanyayyan abu ya ratsa jikina, da azarɓaɓina kuwa na ɗaga.

"Myyyy". Ya kira sunan da wani irin salo da ya saukar min da kasala. Na lumshe ido kana na amsa,"Na'am Salim". Sautin murmushinsa ya fito, yayi yayi na canja masa suna nace ni haka zan ke faÉ—i, da haka kuma sai ya koma cewa nafi kowa iya faÉ—in sunan, kamar ni na raÉ—a yafi daÉ—i a bakina.

"My mun dawo fa, gani a ƙofar gida".
Basarwa nayi irin ban damun nan ba na ce,"Ah dama yau zaku dawo, amma kun yi sauri, ai ce na ke sai kun yi good one month".

Na tabbata sai da ya tsotsi leɓensa kafin yace da ni,"My abu ɗaya yasa na ke ɗaga miki ƙafa, ni za ki munafurta ki nuna min ba kiji daɗin dawowana ba, to fito da sauri kafin na kasa jurewa na shigo gidan da kaina".

Idona a waje na ce,"Kuma sai ka iya?".
"Kina mamaki? Ki ƙara five minutes kika ga ni sai dai ki tsince ni ina tsallake mutane, kuma a gaban kowa zan kamo hannunki na fito da ke".

Dariya nayi sosai nace,"Yi haƙuri Sojansu kar ka bani kunya".

Aje wayan nayi na leƙa na ƙwalawa Yasmin kira na ce taje ta buɗe masa ɗakin Yaya Al'amin. Na dawo daga ciki na shiga shiryawa, kamar wanda zata je gasar kyau, ba fa wani makeup na tsaya yi ba, powder kawai da kwalli sai lip bam shikenan amma kamar a sace ni a gudu, ni kaina ba ƙaramin kyau na yiwa kaina ba.
Na fito ina wani takun ɗaiɗai, na leƙa ɗakin Ummani bata nan na bita ɓangaren Ummansu Hindatu, wanda bai sonka dai har a bada ba zai so ka ba, tunda aka fara hidiman bikin nan ƙala Umma bata ce da mu ba, kamar ma bata san da za'ai biki a gidan ba, ranar da aka buɗe lefe ma Sha'awanatu ƴarta ce kawai ta zo taga kayan, amma har yau Allah sanya alkhairi bata ce da Ummani ba, ni kuwa idan taga gimlawata sai da ta harare ni, nima kuwa na koyi shareta ko gaida ita bana yi, me zaka yi da mutumin da bai gamin mahaifiyarka da mutunci.

"Ummani zan tafi". Suna awon masarar da za'a kai niƙa ayi tuwon dare na yau saboda baƙi, ta ɗago tana kallona tace,"Kika ce kin ɗau hutu".

Umman su Hindatu tace,"A'a Æ´ata irin wannan kyau haka, ko dai sirikin nawa ne ya zo".

Nayi murmushi ina cewa da Ummani,"Bana faɗa miki zan je karɓo sauran ɗinkuna ba".

"Ohh haka ne, to ke da wa zaku tafi? Ko ta gidan Safiyya za ki biya".

Na ɗan yi ƙasa da kaina ina sosa gira cike da kunya na ce,"Salim ya zo shi zai kai ni".

Ta ɗan shiru kafin tace,"To sai kun dawo Allah ya kiyaye ya tsare hanya, kinga idan ki samu dama ki biya asibitin ki duba ƴar gidan Baaba mai ƙosai".

"Ai kuwa gwara da kika tuna mini, wallahi na manta kuma fa ko jiya sai da ta kira ni tace ko da nurse É—in da zan taimaka na haÉ—a su".

"To inda hali sai ki ƙoƙarta musu, yarinyar naji ance sai an ƙara yi mata wankin ƙunar".

Ina jinjina kai da tausayawa nace,"Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bari na tafi".

"To sai kun dawo Allah ya tsare, a kula don Allah Sa'ida".
Ni wai sai kace wata ƙaramar yarinya, indai zan je wurin Salim ko zance zai ne Ummani ta dinƙa a kula a kula, balle kuma idan na ce zamu fita tare ai sai an ja kusan rabin awa ana min wa'azi da nasiha, yau ɗin ma don tana cikin hidiman aiki ne da tana nan tana min nasihar yau da kullum, ni duk idan tana haka sai nayi ta tsarguwa ina cewa ko bata yarda da ni ba ne.

Umman su Hindatu tace,"Ƴar uwar taki dai sai gobe zata samu shigowa".

"Ai ki rabu da ni da ita Umma, duk rashin mutuncin da zan mata kar kusa baki".

Suna dariya duk ɗin su na wuce Umma na faɗin mun fi kusa, a tsakar gidanmu su Gwaggo Talatu na ta faman yabon kyan da nayi, wata Kakarmu ta ɓangaren su Ummani na zolayata da cewa ko dai gasar kyau zan tafi, wata ƙawar Ummani kuwa na faɗin gaskiya wadda tayi min gyaran jiki tayi mugun iyawa, fatata sai sheƙi take yi na zama kamar ƙwanduwar ƙwai, ko da madara da kankana ake wanke ni kullum ai sai haka, ga ƙamshi na tashin hankali tun daga nesa, su Juwairiyya gulmammu na tsokanata wai ai nan dai da jibi ne in kwantar da hankalina sunga ina ta rawan ƙafa, dama tunda suka ga mota a waje suka san shine ya zo, Mubaraka na bada labari wai ya zo da kakin soja ya fito duk ya tsorata ƴan unguwa, yara har da masu gudu.

Zuwana soro ƙamshin turarensa ya dakeni na lumshe ido, har ga Allah ƙamshin nan shi ne ke rikitani na kasa sarrafa kaina a duk sanda na ke tare da shi. Ina tsaye Maman Khairi ta zo wucewa zasu kai buhun fulawa gidan da za'ai kayan gara, ta mintsine ni da cewa kar dai in kai kaina in yi haƙuri in bari su kaini, kunya ta rufe ni nayi saurin rufe fuska ina saurin shigewa ɗakin Yaya Al'amin.
Yana zaune gefen katifar Yaya Al'amin, dama ya saba duk sanda ya zo anan yake zama, na ce me yasa bai son zama kan kujeran, sai ce yay gwara ya ke zama kan abu me taushi da ɗumi kar sanyi ya shige shi in zo ina cika shi da mita a shimfiɗa, haka ya saki baki yana ta zuba maganganun da suka sa har ya tafi ban ƙara kallonsa ba saboda mugun kunya, mamaki ya bani sosai sam ban san haka yake ba, hmmm dama namiji ka gansa kawai sai in bai samu wuri ba, duk da na san komai amma haka yasa naji kalaman suna neman su fi ƙarfin kaina.

Ni dai ko da na shiga sai na kasa motsi, na maƙale a wuri ɗaya shauƙin ganinsa duk ya game min ilahirin tsoka da jinin jikina, har wani abu na ke ji yana tsikarina a yatsan ƙafa, ƙafafuwana suka yi bala'in sanyi saboda kallon da ya kafe ni da shi wanda ke neman kassara gaɓɓaina gaba ɗaya, ya lumshe ido yana sauke wani wawiyan ajiyan zuciya da yasa na ɗago babu shiri na ƙura masa ido.

Yau ne ranar farko da na gansa cikin shigar uniform complete, ashe haka kayan suke masa bala'in kyau, har ga Allah sai da naji ina ma ya zama halalina in ƙarasa gare shi da sauri in rungume shi cikin shauƙin soyayyarsa da ƙaunarsa, ai ko kamar ya san me ke raina sai gani nayi ya buɗen hannaye wai in zo in hugging nasa, ina murmushi na maƙe kafaɗa ina a'a.

Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na ware ido ina cewa,"Kayii". Sai kuwa ce yay,"Ai yaronki ne ni, nan gaba kaɗan ma breast feeding ɗina za ki ke yi". Ya faɗin hakan yana kashe min ido guda, nace,"Ban hanaka ba irin wannan maganan ba".

Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni.
Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage".

Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape".

Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba".

Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido.

Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari".
Chapter 78 · 0% Book details