Sashe 8
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga wannan ranar kuma shikenan sai Yaya Nazifi ya ɗauke ƙafa daga gidanmu, zuwa gaida Kaka ma da ya saba duk ya daina, kowa kuma sai cigiyarsa yake yi a gidanmu, da an tashi sai a tambaye ni, nima sai na rasa amsar da zan ke ba su. Abbaa yake cewa ƙila ko yanayin kasuwar tasu ne don ranar nan yaje can wajensa sun gaisa, Wata rana ma sai Yaya Al'amin ya ce mana ai sun haɗu can shagon yake ya faɗa masa yanzu ba ya samun lokaci shiyasa bai leƙowa, amma ya gaidar masa da kowa.
Ni dai duk sai na takura kullum cikin tunani, kawai abin da zuciyata ta gama yankewa shine zan sanarwa da su Abbaa a mayarwa da Salim kuɗinsa, domin a kaf nazarin da na zauna nayi Salim shine zai yanke alaƙata da Yaya Nazifi, ni kuma ko kusa bana son abunda zai raba zumuncinmu domin kallo ɗaya na ke masa da yayyena maza waɗanda muka fito ciki ɗaya, don haka zan sanarwa da Salim tun wuri Yaya Nazifi, idan yaga zai iya ɗaukar alaƙarmu da shi ko bayan aure shikenan, idan bai iyawa to ni bai isa ya raba ni da shi ba.
Bayan watanni sai ga Salim ya zo gidanmu, ranar da ƙyar Abbaa ya amince na fita wajensa domin cewa yay ai ba haka aka yi da shi ba, yanda aka yi ko da zai fara zuwa muna gaisawa sai nayi candy tukunna, Abbaa yay ta faɗa sosai yana cewa shi baya son irin haka dalilin da yasa yaƙi karɓar kuɗinsa kenan amma Kaka ya matsa.
Ranar kuwa na sami damar nunawa Salim duk wata shaidar da zai fahimci ba na sonsa ko kaɗan balle sha'awar zaman aure da shi, ban fito da baki na faɗa masa cewa bana sonsa ba, amma in dai shi me hankali ne zai gane inda na dosa, haka ya zo da manyan ledojinsa na sahad store guda biyu amma naƙi karɓa.
Kuma ban san ya akai ba bayan kwana biyu da zuwan nasa sai Ummani ke ce min Iyayen Salim sun zo sun karɓi kuɗinsu, wai shi yana so yay aure yanzu don haka idan ni matarsa ce komin daɗewa zai mallake ni amma a yanzu ya samu wata yarinyar da iyayenta suka shirya aurar da ita.
Ranar kamar nayi me don farin ciki, dama ni har ga Allah ko ba don Yaya ba zan aure shi ne kawai saboda zaɓin mahaifina.
Washe gari da muka je makaranta Safiyya ƙememe taƙi kula ni, na damu da fushinta sosai, kuma ko da na takura da roƙonta akan me na mata sai tace bata yi zaton zanƙi wani ɗan uwanta ba, na ce ai ba ƙinsa nayi ba shi yace ya sami wata matar, tace ƙarya ne dama akan me ba zai ce haka ba tunda na nuna masa bana ƙaunarsa. haka dai tayi ta maganganun rashin jin daɗin abin da nayi, tace kuma ta san ba kowa ne sila ba sai Yaya Nazifi don haka wallahi ta tsane shi, ba don ya shigo rayuwata ba tana da tabbacin babu dalilin da zai sa in ƙi Yayanta ko don amintar da ke tsakaninmu, ta san zan so shi ko saboda ita.
Ni dai nayi ta bata haƙuri da ƙoƙarin fahimtar da ita amma taƙi saurare na sam, har da cewa ni munafuka ce dama can son Nazifin na ke yi kuma ba zan burgeta ba sai na aure shi. Sai ma ta bani dariya, ni dai abin da na sani tsakanina da Allah bayan son ƴan uwantaka da nake masa bana masa irin son da suke tunani, amma kowa ya gagara fahimtata, sun kasa ganewa cewa Allah ne ya haɗa jinina da shi, ranar ko da aka tashi makaranta ƙin tsaya ni tayi tai tafiyarta, ni kuma tafiyar nata ma sai yay min daɗi domin kuwa ina son zuwa shagon Yaya Nazifi sai dai in har da ita ban san ya zan yi na je ba.
Na hau adaidaita sahu ya kai ni Jakara kasuwa, da tambaya na je har Shagon Yaya, lokacin yana alwalar azahar na isa ƙofar shagon, tun kallo ɗaya da yay min bai ƙara ba ya ci gaba da alwalarsa, sai dai na san ko bai faɗa ba yay mamakin zuwan nawa domin naga hakan a ƙwayar idonsa a kallon farko da yay min. Ina tsaye gabansa har ya kammala alwalar, ya miƙe ya shiga ciki ya bar ni tsaye, ina jiyosa yana cewa da yaran shagon da suke tare su ɗan ba shi aron wajen yay baƙuwa, sai da suka fito dukansu kana yay min wani duba da cewa.
"Bismillah". Na taka a hankali zuwa ciki, yay min nuni da wata kujerar katako na zauna, yana warware hannun rigarsa da ya naÉ—e ya ce,"Zan je masallaci ina dawowa".
Ina ta kallonsa dai ban ce komai ba ya fita ya turo ƙofan shagon, sai naga duk ya faɗa idanunsa sun yi loko kamar ma yay jinya. Ina zaune shiru ni ɗaya ina ta kallon kayayyakin shagon, ma sha Allah akwai kaya sosai kuma shagon babba ne da alama ana ciniki ba kaɗan ba. Bayan wasu mintuna ya dawo hanunsa da leda baƙa, ya aje kan glass ɗin gabana yana cewa.
"Ga lemu. Akwai pure water a ciki ko za ki alwala". Ya faɗa yana miƙo min wani botiki gabana, a ciki nayi alwalar ya shimfiɗa min sallaya daga ciki nayi sallar, sai yace na zauna anan ba sai na dawo bakin ƙofa ba saboda masu wucewa. Ni dai duk bana jin daɗi saboda rashin sakin fuskarsa, ya kuma nuna bai murna da zuwan nawa.
Nayi shiru shi kuma yana ta karatun ƙur'aninsa, yana cikin yi kuma wata mata ta shigo siyan kaya, bayan ya sallameta ne murya can ƙasan maƙoshi na kira sunansa. Ido ya ɗora akaina ba tare da ya amsa ba, idona ya kawo ruwa ina cewa,"Yaya laifin me na maka?".
Sai ya bagarar da zancen nawa da cewa,"Bamu gaisa ba ma".
"Na gaidaka ai amma sai ka nuna kamar baka ji ba".
"Ki yi haƙuri ban ji ba. Ya su Ummani?".
"Suna lafiya. Ya kasuwa?".
"Kasuwa Alhamdulillah, ga shago nan yau kin gani, sai ai mana adu'a".
"Allah ya bada sa'a Yayana".
"Amin na gode ƙanwata. daga makaranta kika biyo nan?".
Na É—aga masa kai ya ce,"To me yasa?".
"Kawai na zo na ganka ne, ka daina zuwa gidanmu gaba É—aya".
Sai ya shafo gashinsa yana cewa,"gaba É—aya babu wani lokaci ne yanzu amma in sha Allahu ina nan tafe, zan samu wannan lahadin ma in zo ki faÉ—awa Ummani".
Nayi shiru ban ce komai ba. Sai kuma ya ce,"Ƙanwata akwai damuwa ne? Na ga yanayin na ki wani iri".
"Kaima Yaya naga duk ka rame, rashin lafiya ka yi?".
Fuskarsa ta murmusa yana kallona sosai kafin ya ce,"To ƙila ko don kin jima ba ki ganni ba ne, amma ni da na ke jina ma kamar zan fashe saboda ƙiba, yanzu hankali ya kwanta an sami sana'ar yi, mutane basa ta surutun kana zaman banza ba, haka gida ma kullum ana samun wadatuwa da abinci".
Murmushi nayi da sautinsa ya fita kaɗan na ce,"Alhamdulillah Allah ƙara rufa asiri. Ai dama Yaya na faɗa maka komai zai wuce ya zama kamar ba'ai ba.
Kuma Yaya kace kayi ƙiba, kalla fa wuyanka yanda ya ƙara zugewa, wannan sai dai karyewa ba fashewa ba kam".
Hularsa ya cillo min yana faÉ—in,"Za ki fara tsokanar tawa ko".
Kawai sai na tsinci jin daɗi a raina saboda yanda naga fuskarsa ta washe da dariya, ya miƙe yana cewa,"Tashi to na raka ki kar aga kin jima, ko za ki faɗawa Ummanin kin zo?".
Nayi shiru sai ya ƙara cewa,"akwai me wainar fulawa a baya na siyo miki?".
Girgiza masa kai nayi alamun a'a, ji na ke kamar kar na tafi amma haka dole na tashi ina jin kewarsa tana cika ni. Leda ya ɗauko me layi layi shaƙe da kaya ya miƙo min, na karɓa na duba sai naga kayan kwalliya ne a ciki masu yawa da su man shafawa da under skirt, na dube shi cikin jin daɗi ina cewa,"Yaya na waye?".
"Na ki ne, tuntuni na ke ta cewa zan bawa Al'amin ya kawo miki kuma sai bai fiya biyowa ta nan ba. Akwai wata baƙar ledar a ciki wannan na Ummani ne. Wannan kuma ki bawa yaran gidan".
Ya ƙarashe da miƙo min ledar biscuite. Ganin nayi shiru ina kallonsa ya hure min ido da iskar baki. Nayi murmushi ina ta miƙa masa godiya, sai da ya fara fita ya tarar min adaidaita sahu kana ya dawo yace na fito, kuma sai bayan na shiga motar ne yake ce min.
"Ki gaida sirikina, kice inji wani Yayanki na kalen dangi".
Ina murmushi me faÉ—i kamar dama jiran maganar na ke na ce,"Wanne sirikin? Yaya Al'amin bai faÉ—a maka maganar ta rushe ba? Yaya babu maganar aurena akan kowa yanzu".
Sai naga ya waro ido yana kallona da mamaki sosai bayyane a fuskarsa, haka rashin jin daɗin furucin a ƙwayar idonsa, kafin kuma ya sauke numfashi yace min. "Ki gaida gida". Yana faɗin hakan ya juya ya koma shagonsu ina kallonsa.
Bayan kwana biyu na dawo daga makarantar magriba zan shiga gida kawai naji an dakatar da ni, da mamakina kuma Hamisu ne abokin Yaya Nazifi, muka gaisa da shi yana ce min wurina ya zo zamu yi magana amma in shiga gida in fara sanarwa tukunna.