Sashe 35
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sabon kukan da ke zuwar min na ce,"Abbaa ba na son komawa gidansa, Abbaa Nazifi ya zalunce ni da yawa, tun da na aure shi ban huta ba Abbaa, ina jin tsoro kar yaƙi bani takardata".
Yanda amon muryan Abbaa ya fita ni kaina sai da na tsorata musamman da naji furucin da bai taɓa yunƙurin yi ba.
"Malama daina kuka ki share hawayenki, ki kuma kwantar da hankalinki, saki ne kamar yayi shi ya gama, ko da zan yanke hannun Nazifi ne sai na yanke ya rubutu sakin ki...".
"Subhanallah". Ummani tayi saurin katse shi. "Abbaansu don Allah ka sanyayawa zuciyarka ruwan sanyi, ai duk ba sai ta kai ga an fusata irin haka ba, shi kansa ai ya gaji da ita ko ba'a tursasa shi ba dolensa ne ma zai bata takardarta, amma ka daina batu irin haka".
Kansa kawai ya jijjiga yana ƙurawa waje ɗaya ido ba tare da yace da ita komai ba. Ummani ta zame kaina a bisa cinyarta ta miƙe tana faɗin,"Bara naje na ɗora girki, Me za'a dafa?".
"Kar ki girka da ni sai naga yanda hali ya yiwu".
"To Allah ya kyauta".
Fita tayi, ni kuma ina nan zaune hankalina duk yaƙi kwanciya, tsorona Allah tsorona Nazifi yaƙi sakina, Abbaa yace na tashi na tafi kuma in ban daina kukan ba sai ya saɓa min ya mayar da ni can gidan da kansa tunda ya lura kukan na ke so, to gwara na koma inda zan ke yi kullum da hujja.
Ko da Ummani ta sauke abincin rana kasa ci nayi, babu yanda bata yi da ni ba na ce mata na ƙoshi, Abbaa kuwa yanda ta aje kwanonta bai kalli inda yake ba, sallar azhar kawai naga ya fita, tunda ya dawo kuma ya zauna ban da jijjiga kai da girgiza ƙafa ba abin da yake yi. Sun yi waya da Yaya Imam yafi sau ƙirgen yatsu, shi kuma yana can office ɗin Nazifin wai ba ya nan amma ya tsaya jiransa ya dawo, Abbaa dai yace to karka dawo min gida sai da takardar sakin ƙanwarka. Ana haka Yashaik ya dawo shima ya ce ai yaje har can gidansa bai same shi ba, Abbaa bai ce komai ba sai Kaka ne ma yace,"Lallai yaron nan ya wuce tunaninmu a rashin mutunci, ƙila sai mun ɗauka hukuma mun masa shigar dare".
Ni dai ina kallon fuskar Abbaa yay wani irin murmushi da shi kaÉ—ai ya san ma'anarsa. Ganin yanda na takura kaina Ummani ta ce,"Ke zo ki kitse min kaina".
Tare muka fita da ita daga ɗakin Abbaan, muna kitson tana faɗa min na kwantar da hankali na saki raina nayi walwalata, na riga na san waye mahaifina tunda har ya furta yau to sai in ba ya numfashi ne abin da ya faɗa ba zai aiwatu ba, kuma na san su waye Yayyena su kan yi duk iya ƙoƙarinsu akaina wajen ganin sun nema min ƴan ci sun kuma faranta min.
Ta shiga bani labarin ai lokacin da na kirata na shaida masu abin da ke faruwa ta zayyanewa Abbaa komai, shi ne ya fusata yace yana raye bai ga wanda zai wulaƙanta masa ƴa ba sai Nazifi ya sake ni kuma sai ya kai ƙararsa kotu an bi min hakkina, kuma in sha Allah Nazifi na raye zai ga ƴaƴana da ɗaukakata.
Gama kitsonmu kenan yaro yay sallama yace ana kiran Sa'ida a waje, da mamaki ni da Ummani muka maimaida abin da ya faÉ—a, sai Ummani tace da shi,"Kaje ka ce waye".
Yaron ya koma sai ga shi ya dawo yana faɗin wai mijinta ne ya zo, ta shiryo za su tafi. Kusan tare da Ummani muka girgiza kai a raina ina faɗin lallai Nazifi ya raina ni ya raina gidanmu. Ummani bata ce komai ba ni kuwa na miƙe na fita, ɗakina na shiga na yafo mayafina na nufi hanyar fita sai Abbaa ya fito yana cewa da ni,"Ina za ki?".
Kaina ƙasa Ummani ta fito tana ce masa,"Wai Nazifi ne ya zo ya ce taje su tafi".
Abbaa yace,"Madallah da ɗan marasa kunya, to kije ki same shi ki karanta masa duk wasu shiƙa shiƙan cin mutunci da ke cikin kanki sannan ki juyo ki dawo, ki tabbatar kin gusar da ɓacin ran saman fuskarki da maganganu masu zafi da tsayawa a rai".
Ina fita na same shi daga cikin mota ya hakimce, yana ganina yay biris yana jiran na ƙarasa, minti ɗaya, biyu kawai sai na juya zan koma cikin gida sai ji nayi yana,"Malama dakata". Amon muryarsa ya fito tamau.
Na waigo lokacin da yake isowa inda na ke. Yana faman haɗe rai yace,"Ɗan aiken bai faɗa miki saƙon cewa ki fito tafiya zamu yi ba".
"Shi ne ai na fito naga wanne mara zuciyar ne, ashe kai ne Nazifi, me ya kawo ka ƙofar gidanmu?".
Bai expecting furucin hakan daga gareni ba don haka ya tsaya kallona kafin ya ce,"Saboda ba ki da hankali kin baro gidan aurenki kin zo kin nemi wuri kin zauna, tukunna ma bisa izinin wa kika taho nan É—in?".
"Bisa izinin waɗanda suka isa da ni, ka san ai ni ban gama watsewa ba ina jin maganar mahaifina. rashin hankali kuma ai yana wajen wanda babu zuciya a ƙirjinsa. Kai Nazifi ban da ma baka da kunya har ka iya tako ƙafa ka zo ƙofar gidanmu kace na koma gidanka, gidan da babu arziƙi babu mutanen arziƙi a cikinsa, gidan butulu rainon butulu, To bari kaji na faɗa maka sai dai wata Sa'idan a gidanka amma ba dai ni ba, babu abin da zai maida ni gidan mutumin da bai tsotsi arziƙi ba sai tsiya, mun rabu rabuwa ta har gaban abada, sai ka jira haɗuwarmu a kotun Allah. Yanzu miƙo min takardata da ka kawo min sannan ka juya ka bar mana ƙofar gida bana son sake ganinka idan ba haka ba sai nasa yara sun maka cin kashin da kare ba zai shinshina ba".
Wani kallo yake min da ke nuna tsantsar ɓacin ransa da takaici. "Ni kike faɗawa magana haka?".
"An faɗa maka, an faɗa maka shayinka na ke yi, ai ko a ba ya darajar biyayya wa iyayena yasa na rangwanta maka, ban da haka abin da zan maka dabba aka nuna maka aka ce ka wulaƙantata Nazifi ba zaka soma ba. Kuma gidanka ne na baro shi kenan ko ba tsayawar ahalina, sakina ya zamar maka dole balle kuma sun tsaya min, zaka bani takardata ko kuwa zaka nuna min kare ya cinye zuciyarka?".
Duk maganar da na ke yi ina yi ne cikin rawar murya da taruwar hawaye a idona wanda ban san na menene ba, sai dai sam na hana bayyana duk wata faka da zata nuna rauni a tare da ni.
Yana jijjiga kai kaman ƙadangare yace,"Ko za ki mutu ba zan sake ki ba Sa'ida".
"Haka nima ko zaka hauka ce ka bi bola Nazifi sai ka sake ni, ai ba ma sai na rantse ba don ayau zaka san an isa da kai a gidan da ka raina mutanan cikinsa. Ban da ma ƙaddara da jarabawa ina ni ina zama matar illiterate irinka, talaka irinka da ko ubangijinsa da yay masa ni'ima bai iya gode masa ba balle ya godewa wacca da kuɗin gumin mahaifinta aka samu ceto rayuwar uwarsa, a lokacin da ƴaƴan da ta haifa su kasa yi mata komai...Ai kin banza ƙwaƙwalwa babu komai sai tarin jahilci, yo jahilci mana tun da an karanta ba'a anfani da shi, matacce mai matacciyar zuciya, babu komai a tare da kai sai tsiya, wallahi na godewa ubangijina da bai sa na haɗa zuri'a da ƙaramin mutum irinka ba, kuma dama ubangiji ba azzalumin bawansa ba ne shiyasa ya hana ni haihuwa tare da mutum mara daraja irinka, don abin jaje ne ga duk ɗan da zai nuna Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin uba, haka abun kunya ne ga macen da zata nuna Nazifi a matsayin miji, ni kuwa yanzu tsakanina da kai tamkar nisan sama da ƙasa ne...".
A zafafe ya kawo hannu zai wanke ni da mari yay rashin sa'a tawa zuciyar tafi tasa kusa, aikuwa bai farga ba na damƙe hannunsa na ɗauke shi da marin da sai da ya kifa ƙasa.
Na ƙyasata yatsu ina nu na shi na ce,"Somin taɓi na maka, idan ka ƙara kuskuren ɗaga hannunka a gabana wallahi sai na maka wanda yafi wannan muni...kuma ka bani takardata na ce kafin na ƙarasa yaga maka rigar mutunci".
Yana dafe da kuncinsa Yashaik ya iso wajen. ya duben yace,"Me ya fito da ke wajensa?".
"Zan faɗa masa ne ya kwashe ƙazaman ƙafafunsa masu dattin zunubi ya bar mana ƙofar gida, wadda ya ke tunanin zata koma masa ba ƙaramar mutum ba ce ita kamar shi ƙasƙantacce kuma wulaƙantacce mara ilimi".
"Shiga cikin gida". Yashaik yace da ni.
Na watsawa Nazifi wata muguwar harara naja dogon tsaki da cewar,"Ka jira lokacin da zaka yi ƙuncin da yafi na saman fuskarka a yanzu, ka kuma jirayi lokacin da zaka burkice da nemana akan na yafe maka, itama ta gida ka faɗa mata hakkina ba zai barta ba gwara ta zo tunda wuri ta duƙa ta nemi yafiyata kafin duniya ta fara ƙwallo da kai da ita da magoya bayanku".
Na shiga cikin gida ina jin Yashaik na ce masa ya ba da takarda kawai ya tafi babu wanda ke son ganinsa takarda kawai su ke so, ba su da lokacin ɓatawa da shi.
Murmushi Nazifi yay me kama da na yaƙe yana sosa gemu, yaywa Yashaik kallon wulaƙanci kana yace,"Kuna ta in saketa in saketa, ban ga fa wanda ya isa ya tilasta min ba, yin kaina na ke babu me saka ni yin abin da ban niyya ba, idan kuma kuna da karfin ƙwata sai ku ƙwata...kuma ka shiga ka faɗa mata ta fito mu tafi don ban gama wahalar da rayuwarta ba".
Yashaik ya girgiza kai yace,"To shikenan kar ka bayar, idan mu ka je gaban Alƙali ka maimaita hakan, zamu haɗu a kotu a karo na biyu".
"Hhhh to shikenan muje zuwa, in dai kuna da kuÉ—in yin shari'a ku buga da ni".