← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 113

Sashe 80

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi saurin girgiza da cewa,"Ban gane ki ba, kuma ban san ma akan abinda kike magana".
Ina faɗin haka nasa kai na fice ina murmushi. Maɗaukakin mamaki yasa Zahra'u kama ƙugu baki sake tana bin bayan Sa'ida da kallo, kafin tace,"Kutmar amma yarinyar nan ta mugun manna min hauka".

Ƙanwar Babansu tace,"To ke kin santa ne? Ƙila kamannin kika gani".

Ta juyo tana dubansu tace,"Wallahi ƙarya take yi ta san akan abinda na ke magana, rainin hankali ne kawai da son ci min fuska, amma ta sanni sarai, Kishiyata ce fa".

Wata cikinsu ta waro ido waje,"Kishiyarki kuma? Kishiyarki ta gaske?".

"Hmmm". Ta faÉ—a tana wucewa ta zauna kan kujera tana jijjiga kai.
"Kun san Allah kishiyata ce ada, ba fa wulaƙancin da ta min ne ya damen ba, mamakina ɗaya matsayin da na ganta akai, yaushe Sa'ida tayi gogewar da har ta taka matakin zama ma'aikaciyar lafiya?".

Ta kusa da ita tace,"Wai kina nufin kishiyarki É—in nan da tayi sanadin mutuwar yarinyarki?".

"Ita fa! Kin san ai tun lokacin shari'ar nan suka rabu bata dawo gidan ba, to yanzu ace cikin shekaru shidda ta zama haka? Ƴar talakawa ce fa ina taje tayi karatun da har ta zo babban asibiti irin wannan aiki? Ke fa lokacin da muke tare na rantse miki da huwallahu ko turancin kirki bata ji, yo ina ma ilimin bokon, batta dai akwai ilimin addini ni kaina ba ƙaramin burge ni take ba a ɓangaren nan, Samiha na rantse da Allah na girgiza, Samiha asibitin nan fa sai waɗanda suka yi karatu a ƙasar waje ko kuma a makarantun kuɗi na cikin ƙasar nan suma sai manya manyan makarantun, kuma ko hanya za'a maka sai ka biyo ta babbar hanya, Daddy kansa ba ya cin alfarmar asibitin nan kina kallo duk nacin Naja'atu haƙura tayi, Samiha ta ina ta shiga ta fita ta zo nan? Albashinta fa yaci uwar nawa Samiha".

Wadda take kira da Samiha tayi dariya da cewa,"Yo ba bazawara ba ce, ke har kya yi mamaki, kika san manyan mutanen da ta ke bi".

Zahra'u tasha mur tace,"Ban son iskanci wanna irin furuci ne wannan, ku babu dama mace taci gaba sai kuce ai bazawara ce ga yanda akayi ga yanda aka yi, lallai duka zaurawa Æ´an iska ne?". Tayi maganar cike da jin haushi har da su tsaki.

Samiha ta dafa kafaɗarta tace,"Maida wuƙar mene abin ɗaukan zafi, kema kin san dai tsakani da Allah akwai zaurawan da ke siyar da mutuncinsu ke majority ɗin su ma haka suke, kuma ina da tabbacin yarinyar nan na ɗaya daga ciki don haka ɗaya dai ƴar talakawa ba zata zo aiki wannan asibitin ba. To ke mene na ki a ciki don na faɗi haka? Ke ko iskancin ma kika yi ai ba za'a ce kin yi ba tunda ansan ƴar waye kuma dama tuni kina da aikin yi, cikin kuɗi kika taso cikinsa kike, to wa ya isa kuwa yace kina sahun zaurawa masu siyar da mutunci, ni ita ɗin dai na ke maganar shiga hotel da fitarsa ce ta kawota nan".

Zahra'u ta sauke numfashi kafin ta tuntsire da dariya. Duk suka kama kallonta. "Wallahi Allah Nazifi na hango! Idan ba yaga Sa'ida sai ya yanke jiki ya faɗi ba, kun san yanda ya wulaƙanta yarinyar nan kuwa shi da ƴan uwansa, ranar farko da ya fara haɗuwa da ni cewa yake matarsa bagidajiya ce, bata da wayewa, babu boko kwata kwata, babu aikin yi, mummuna shi kawai yana zaman dole da ita ne". Sai ta ƙara sakin dariya da cewa,"Allah ka haɗa Nazifi da Sa'ida, shegen Ƙwallo yaga yanda rayuwarta ta sauya".

Ƙanwar Babanta tace,"Du Allah ke rabamu da zancen nan, kamar fa muna cin namansu ne dukka. Kema kuma ya kamata ki yiwa kan ki faɗa ki koma gidan mijinki".

Tuni tasha mur tana faɗin,"Allah ya kiyaye ya tsare, haba Anty Amina ko maƙiyina ai ba ya min fatan na koma gidan Nazifi ba, mutumin da bai da ko sisi ina zan iya zama da shi, me yaci me ya ban naci balle ƴaƴa?".

"Yo ba da kuÉ—insa kika auresa ba, me yasa ba za ki tawakkali ki zauna da shi cikin jarabawar da ubangiji ya aiko masa ba, ko don Æ´aÆ´anki ma ai kya koma".

Ta cuno baki ta ce,"Komawa to sai dai ko wata Zahra'un amma ba dai ni ba, ƴaƴa kuwa ai na rantse ba zan taɓa ba shi ba, alƙalin ma kansa ya rattaba hannu ba zan basa yara ba za suke zuwa dai su gansa jefi jefi shima don ba yanda na iya ne ubansu ne dole, amma ina yarana ina rayuwar karkara kuma cikin talauci Allah kiyaye".

Ƙanwar Baban na su ta sake cewa,"To aikuwa dai ba ki kyauta ba".

Zahra'u ta jingina kanta da bango abinda Sa'ida tayi mata na tsayawa a ranta, Idanuwanta suka rufe hoton shekaru biyu baya na haskawa cikin idonta bayan haihuwar Mardiyya da ta ƙara yi don lokacin da ta sha maganin zub da cikin nan Allah bai nufa ya zube ba.
Kwayar idonta ta haska mata hoto tarrr lokacin da hukuma suka zo tafiya da Nazifi da sunan yaci bashin banki bai biya ba, tana tunawa haka ya tsuguna gabanta yana roƙonta Allah Annabi har da hawaye akan ta taimaka masa da takardun gida ya siyar ya rage wani abu, tayi mirsisi taƙi lamarin har kotu tsakaninta da shi aka je, tace ita babu wani abu nasa da ya mallakawa yara ƙarya yake mata, haka aka yi ta bincike aka duba aka ga kaf wasu kadarori da yake faɗa yana da su duk mallakin zahra'u ne ba nasa ba, dole haka aka tasa ƙeyarsa gidan ɗan kande sai da ya shafe watanni bakwai a prison kafin ya fito.
Itama fitowar tasa ba don an biya kuɗin ba ne an dai rage wani abu a ciki, kuma tasirin adu'a ne ma yay ƙarfin da har aka bayar da shi, mahaifinsa ne ya siyar da gidan da suke zaune sai ya nema musu gidan ƙasa wanda gaba ɗaya bai wuce dubu ɗari ba, gidan ɗaki biyu ne jal amma haka duk suka ruguntsuma suka koma.
Sannan itama Zahra'u tayi imani darajar Iman da kullum ke kuka tana kiran Daddy, shi ne ta yarda aka siyar da gidan da suke ciki miliyan tamanin da biyar ta bayar da miliyan hamsin, aka haÉ—a aka bayar da miliyan casa'in, da yarjejeniyar duk wata zai dinga ba da dubu hamsin.

Ranar da ya fito kuwa daga kurku ta maka ƙararsa a kotu kan cewar ba zata iya ci gaba da zama da wanda bai haihuwa ba, kuma ba zata zauna da wanda bai da muhallin zama ba, bai da akin yi sannan bai da abin da zai ci da su don haka ya zama dole ya saketa, ta gama zama da shi har abada, haka akai ta daburwa tsakaninta da shi, duk taurin kan Nazifi kan ba zai saketa ba sai da ya sallama yay mata saki ukun da suka nema, domin shari'a da me kuɗi wahala ce, ya sha wulaƙanci kuwa a gun mahaifinta, kuma ko wata guda ba'ai da sakin ba sai ga sabon sammaci sun kuma kawo masa, sun kai ƙararsa gaban alƙali wai ya ce lallai sai ta ba shi yara alhalin ƙarya suka masa, tunda ta bar gidan bai waiwayeta ba duk da yana so yaga yaransa kuma wulaƙanci yasa yake danne zuciyarsa bai neme su ba, ga halin masifar da yake ciki na kai kuɗi da aka saka masa duk wata shi kuma babu sana'ar yi ko da ta ihu ce, haka dole ya rattaba hannu kan takardar da alƙali ya ba shi kan cewa Yara wurin mahaifiyarsu za su zauna ba za'a ba shi ba ko guda ɗaya.

Ya damu amma damuwar da yake ciki tafi wannan, don lokacin yana tsaka da tashin hankali, fitowarsa a bursun da ya zo ya tarar da gidansu faɗuwa yay, matan Babansa uku ace ɗaki biyu jal a cikin gida? Ga uban yara? Wai sai da dare yayi yaga kawai Malam yayi shimfiɗa a tsakar gida da shi da yaran maza, ɗaki ɗaya ƴan matan ke kwana a ciki ɗayan kuma Iyam da Amarya, don ita Ummaa tuni ta tafi gidansu, manyan samarin kuwa duka a ƙofar gida suke kwana, a lokacin kawai sai ya kama hawaye ya rasa dalilin wannan masifar, a barsa ma da lalurar mahaifiyarsa na rashin ƙafa da na magani kaɗai ya isa yay hauka, amma sam Zahra'u bata tausaya masa ba haka tace lallai sai ya ke tura kuɗin abincin yara da kuɗin makarantar Iman rabi, to ita yanzu ma bata san a halin da yake ciki ba.

****Ƙarfe uku na tashi daga aiki, akan hanya na yanke shawaran wucewa gidan Safiyya, ban ma kirata na sanar mata da zuwan nawa ba, kwana biyu bamu yi ko chart ba balle waya, sai fushi take yi da ni shine yau zanje na lallashi abata mu shirya, duk da wanda ma take fushin da ni akansa na mance da shi da babinsa, rabona da shi tun zuwan da yay, ni kuma wannan rashin neman nawa ya tabbatar min da ba son gaskiya yake min ba dama yaudara ce tsantsa, to Allah yasa ban faɗawa tarkonsa ba, zaluncinsa ya ƙare masa.

Falon Safiyya idan zaka kwana kana kwaÉ—a sallama babu me jinka, kuma ni na saba duk sanda na zo kaina tsaye na ke hayewa samanta, dama kuma bana zuwa ranar da mijinta yake gari, ba mazauni ba ne shi zaman kwana uku yake yi a sati.
Na zare mayafina nayi cilli da shi saman kujera tare da jakata, kaina kansa ji nayi yay min mugun nauyi saboda haka na cire hular itama na jefar, na cire after dress ɗin ma, ribon ɗin ma na cire gashi ya baje a kafaɗa, Allah ya gani nayi mugun gajiya ga uwar yunwa da ke ƙwaƙwalar cikina.
Chapter 80 · 0% Book details