← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 113

Sashe 54

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita Iman da ke hannun Lubabatu tana bata biscuite ta shiga miƙo masa hannu, sai yaji wani sanyi ya ɗan ratsa shi, a ƙalla ubangiji bai jarabce shi ba sai da ya bar masa guda ɗaya.
Miƙa hannu yay ya karɓeta ya saɓa a kafaɗarsa, ƙwarai Zahra'u ta shiga hakkin yarinyar da ta yayeta da wuri, har yanzu ta kasa kama wani abinci da zai ke kama cikinta, yarinyar duk a motse kamar me wata cutar. A mota haka yay ta surutai wa yarinyar yana jin sabuwar ƙaunarta na ratsa shi.

Suna komawa gida ya tarar Zahra'u tayi aika aika da haukan da ta ɗorawa kanta, duk wasu gilasai na falon ta farfashe su, ta hargitsa jeran kujerun. Ciki kawai ya wuce yana takawa a hankali gudun kar ya taka kwalba, yana shiga ɗakinsa ma ya tarar ta warwatso masa da dukka sutturunsa, takardunsa da komai na amfaninsa, yay saurin isa ga kan gado ya ɗakko laptop ɗin yana kunnawa yaga taci screen, ya ambaci ƙalu innalillahi da ƙarfi.

Jiki na ɓari ya aje Iman da ke ta shaƙuwa, kuma kafin yay wani motsi sai gata ta shigo ɗakin tana cewa da shi,"Ashe ma kai ƙaramin ɗan iska ne, ai da baka mayar da ni ba, ai da ka sake ni gaba ɗaya shi ne zaka tabbatar da ka isa ka kai, kuma abin da ka zo ka tarar kaɗan ne, wallahi sai na tabbata ka ɗora hannu saman ka kayi danasanin aurena da hujja, ba dai ni ka duka ba, zaka sha mamaki".

Har ta gama surutanta bai ce mata komai ba, sai da zata fita ne yace da ita,"Ki kwashi muhimman kayanki zamu koma gidanmu da zama, zan siyar da wannan a yau".

Wata iriyar juyowa tayi tana ƙunduma ashariya. "Nazifi ka ce mene? Za mu tashi anan? Mu koma gidanku? Na zauna tare da ƙannenka da matan Babanka ka ke nufi? Nooo impossible, ba a kaina ba sai dai kan wata".

"Ok to idan ba kya son faruwar hakan sai ki tattaro duk abin da mallakawa Æ´ata ki bani na nemawa mahaifiyata lafiya...".

"Kai dakata du Allah! Wai zatonka ni shashasha ce, ka man ce wayayya ka aura ƴar boko me lissafi, to tun da ka bani wannan kadarori na juya komai da nawa sunan Nazifi, kuma kai da kanka ka sanya hannu akai shaidar komai da ka bayar ba naka ba ne ba na ƴarka ba ne nawa ne mallakina ne, baka da iko ba ka da wata hujja a yanzu da zasu karɓa maka, idan ma zaka bar tunaninsu da nemansu zai fiye maka, gida kuma ka siyar ina ruwana, ƙarƙari na koma gidanmu da zama don wallahi ba zan zauna a gidan surukai ba ka zubar min da aji da ƙima".

Ya san dai duk yana jinta da kalamansa, to amma abin da ya kasa ganewa yaushe ya rattaba hannu jikin takardu? Take watarana ta haska masa a cikin ƙwayar idonsa, sun gama gurzar soyayya ko tashi ba suyi akan gadon ba ta miƙo masa takardun tana faɗin takardu ne na neman promotion a wurin aiki, kuma ana neman sanya hannun miji wanda ta hakanne zata iya samu su ƙara mata matsayin da take fata.
Shi kuma da murnarsa da azarɓaɓinsa ya karɓa takardun guda biyar ya rattaba sa hannunsa akai mai kyau da aji. Yana ta shi mata albarka yana faɗin ɗaukakarta ai tasa ce.

Tunaninsa ya tsaya cak jin ta wullo masa abu a jiki, ya kai idonsa kan ATM har guda biyu, ya ɗauka yana juya su kamin ya kalleta ya miƙe cikin hanzari da ƴar guntuwar murnarsa sai kuwa furucinta yay daga daga da guntuwar murnar da ta ziyar ce shi.
"Babu ko sisi a ciki domin kuwa duk na tura su cikin asusuna, wacca hujja zaka nunawa banki na cewar ba kai ka tura ba? Kuma sannan da kake maganar zaka siyar da gida, ka manta da cewa har da shi ka sanya hannu a takardarsa na cewa ka mallakawa Noor? Motarka ita kawai ta maka saura Nazifi baka da wani sauran abu da zaka yi tunƙaho da shi, kuma ban yarda ba saki tsakanina da kai ma ya zama dole, domin kuwa na lura da cewa kamar babu ta kamaka, ni kuma ba zan iya zaman aure da talaka ba, ba kuma zan bar maka ƴata ba dole zan tafi da ita domin ba zan bari rayuwarta ta tagayyara ba a wurin wanda bai da kuɗin ɗawainiyar kansa ma balle ta ƴarsa, ingantacciyar rayuwa na ke sowa ƴata da zata tashi cikin gata da jin daɗi da rayuwar cikin daula kamar yanda na so ba yanda ubanta ya ta so ba, shiyasa na ƙwace komai na ka kafin ma tsautsayi yaja ka ga samun wasu ƴaƴan ba tare da ni ba ya zama an raba dukiyarka da ba da ƴaƴana kawai ba, kuma kamar yanda ka faɗa ne Kuɗinka shi yasa na aureka ban da haka kai kanka ka san idan ba shaye shaye nayi ba nayi rayuwar ƙasar waje da kwalin degree na me aji ace na ɓige da auren namijin da ko satifiket ɗin primary bai da shi".

Kalaminta ya ƙona ransa,"Ki je duk wata cutarwa da kika yi min ke da Allah domin kuwa kin zalunce ni, mayaudariya azzaluma, sannan ki sani ko za ki mutu igiyar aurena ba zata sauka daga kanki ba, kina nan tare da ni, kin zubar da ciki ko? To ki sani ni kuma a yanzu ba zan ƙara haihuwa ba, haihuwa ta tsaya min".

"Na shiga uku, kenan idan ina tare da kai ba zan ƙara haihuwa ba, ina burin haihuwan ɗa namijin da na ke da shi? Na rantse da Allah baka isa ba Nazifi sai ka rabu da ni sai ka sakeni, ba zan zauna da namijin da ba ya haihuwa ba, ga talauci ga rashin ƴaƴa inaaa".

Ta faÉ—i hakan tayo kansa kamar mahaukaciya tana cewa lallai ko ya saketa ko tayi masa rauni, shima yay saurin tashi ya É—aure Iman a bayansa tare da maketa ta faÉ—a gefe ya fita a É—akin yasa makulli ya kulleta.

*BAYAN SHEKARA HUÆŠU*
*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.*

Ƙarar saukar jirgin da ya jiyo na shawagi a ƙasa yay sanadin lumshe idanuwansa, wanda hakan yay nasarar bayyanar da zara-zaran gashin idonsa da kuma motsawar laɓɓansa masu taushi, kaman wanda yay mugun gajiya haka ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, yay saurin mayar da p-cap ɗinsa haɗi da daidaita zaman baƙin gilashin fuskarsa, sai fuskan ya ƙara ɓoyuwa ta yanda ba zaka yi saurin shaida shi ba, kewayyan sajensa me haɗe da gemu kawai kake iya haskowa kaɗan.

Bugawar sakan É—aya, biyu, uku ya buÉ—e idanuwan nasa daga lumshen da suke tare da É—an juyasu yana jin wani sanyayyan abu na biyowa ta babban yatsansa yana shiga jikinsa.
Idonsa ya sauka akan agogon hannunsa, agogon ya buga ƙarfe huɗu da rabi daidai na yamma, kuma lokacin yay daidai da gama shawagin jirgin da ya taso daga ƙasar Germany zuwa ƙasarmu ta nigeria, kansa ya ɗaga ya mayar da dubansa ga inda jirgin ya sauka, idonsa na kalle masa mutanen da ke fitowa daga cikin jirgin sannu a hankali, kallonsu yake yi sosai ya kasa ko da ƙifta ido, duk ya ƙosa yaga fitowar halittar da idanunsa ke jira, haka kuma ya kasa ɗauke ganinsa daga wurin duk da irin yacca yake jin wani taraddadi na fizgarsa, zuciyarsa faɗa masa take kamar ba zaka samu ba ka haƙura kawai.

Bayan fitowar passengers da dama, gabansa ne ya yanke ya faɗi, zuciyarsa ta harba fat fat a lokacin da ƙwayar idonsa ta sauka akan kyakykyawar halittar da ke sakkowa a yanzu, hasken jikinta kaman jini ya tsarto, kai ba ka ce ƴar nigeria ba, sakkowa take yi daga matattakalan a hankali kuma cikin natsuwa, doguwar fuskarta na bayyana baiwar fara'ar da Allah ya bata, fuskar da kana gani kasan babu wata damuwa a tare da ita illa zumuɗi da ƙosawar son kasancewa da mafi muhimmanci wasu mutane a rayuwarta.

Tun fitowanta a jirgin kanta a ƙasa yake, riga da wando ne a jikinta na uniform ɗin nurses ɗin ƙasar germany blue colour, sun matuƙar mata kyau tubarakallah ma sha Allah, a gefe ɗaya kuma tana gyara zaman sarƙar hannunta.
Ta ɗago fuskarta tana kanne ido alamun haske yay masu yawa duk da rana ta ɗanyi ƙasa a lokacin. Cikin takun tafiyar da take me ɗaukar hankali da burgewa trolly ɗin da take jaye da ita ta cije wanda hakan yasa ta gurɗewa tayi saurin duƙawa.

Gurɗewan nata ya taɓa zuciyarsa ya miƙa hannu da sauri da niyyar tareta daga yunƙurin faɗuwar da take neman yi, sai kuma ya ankare da cewar tazarar da ke tsakaninsu me yawa ce, kuma hakan ya haifar da rashin jin daɗi a tare da shi, bai kamata hakan ta kasance ba, alƙawarinsa ne na gyara kuskurensa zai tsaya tare da ita kowanne yanayi da motsinta ba tare da ya bari wani abu ya sameta ba, katanga ya ke so ya zamar mata, katanga ta kariya, hakana zai zame mata madafar da zata kaance ko da yaushe tana dafawa ba tare da kuka ko baƙin ciki ba, nasa alƙawarin ne a wannan karon wanzuwar tabbataccen farin ciki a fuskarta da duniyarta har ranar da zai daina numfashi, ba zai bari wani abu ya taɓata ba, haka ba zai ƙara gangancin maimaita kuskuren da yay a baya ba.

Iskar bakinsa me ɗumi ya furzar, kansa ya sunkuyar ya leƙa cikin motar da yake jingine a jiki, ƴarsa da ƙanwar ne zaune a ciki, sai ya kai ƙwayar idonsa yana duban fuskar ƙanwar tasa, da wani yanayi sirrantacce a saman fuskar tasa, a hankali yace da ita,"Kayan sun mata yawa".

Sai yay shiru for seconds kana ya ƙarasa maganar da cewa,"zan taimaka mata".

Da murmushi me burgewa a fuskarta da ke nuna nata jin daÉ—i da farin cikin da ke neman zarce nasa tayi knooding masa kanta kawai.
"But be carefull Mr Man".
Chapter 54 · 0% Book details