← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 113

Sashe 107

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abu me sauƙi kenan, ƙarƙari ka fito da kuɗi, zan haɗa maka maganin da sai ka shekara kana min surutan da yafi wanda ka ke yi, maimakon Myy zan mutu sai dai ka koma cewa Myy na mutu daɗinki ya kashe ni".

Na faɗi hakan muna dariyan jin daɗi da shi. Zaunar da shi na yi kan stool na shiga shirya abina, ba na taɓa ƙosawa da yi masa wanka da shirya shi. Ina gyara masa gashi yake min zancen komawata makaranta, duk da ba'a son ransa zan koma ba ɗin, babu yanda bai yi da ni ba akan na bari sai na haihu na koma har fushi yay, ni kuwa ban ga amfanin zaman ba tunda dai lafiya na ke, me zan jira kuma haka kawai sai na fara tara yara kuma karatun ya zo yana min wahala, duk da shekara uku ne na gama.

"Myy; Mommi(Kakarsu) ta ce to ba zai yiwu a barki ki tafi ke É—aya ba, Anty Adamma zata zo sai ku wuce tare, ita zata zauna da ke saboda taimakawa da kulawa".

Nayi knooding kaina da gamsuwar hukuncin da Mommi ta yanke na ce,"Ba damuwa ai Mahbub, ina yiwa Mommi godiya da kulawanta".

"To yanzu kin gama haÉ—a komai? Flight É—in 9 za ku bi".

Na ce,"Ni kam na gama duk shirina". Sai na marairaice na zauna saman cinyarsa na shiga roƙonsa. "To Mahbub don Allah kaga tunda ba ni ɗaya zan koma ba har da Aunty Adamma ka bari na tafi da Rofi'a, kaga dai ba kyau raba uwa da ƴa, Allah baka san irin ciwon da na ke ji ba a zuciyata idan na tafi na barta nima har kuka na ke yi, kana kallo idan na tafi duk ramewa take yi".

Ido ya zuba min yana kallona kawai, sai na ƙara marairaice masa kaman zan yi kuka ina faman roƙo. Gira ya sosa kana yace,"Shikenan ku tafi ɗin, amma ai kin san dai this session za'a sakata school, yanzu idan kika tafi...".

Bakinsa na toshe da kisss, sai da na tsotsi abina son raina kafin na barsa ina murza kunnensa na ce,"Kai dai ba ka yarda mu tafi taren ba?".

Yana kallona da idanunsa da suka canja kala saboda tsokano shi da nayi ya ɗaga min kai kawai. Na miƙe akan cinyar tasa ina cewa,"To idan munje can zan saka ƴata a school nima dama na ƙagara ta fara zuwa makaranta, bakinta ya ƙarasa buɗewa a can".

Fizgo ni yay sai kan gado,"Ki tsokano ni sannan ki nemi hanyar ficewa".

"Mahbub to zan haÉ—a kayan Rofi'a ne fa".
"Tab idan kunje can kya siya mata wasu, amma yanzu madara za ki bani, anjima fa za ki tafi ki barni".

"Za ka takurawa BabynBaby fa".
"In ji wa? Abinda zan yi lafiya zai ƙara masa ai kin fini sani".

Soyayyarmu muka dirza ni da shi, haka muka yini cirr a ɗaki ni har kunya ma naji, don Aunty Adamma ta zo tana ta kiran waya amma mutumin nan ya hana ni fita wai bai ƙoshi ba na ƙyale shi, Baby yasa na ƙara yin daɗi ji yake kamar zai zauce.
Ƙarfe takwas na dare Mahbub ya kaimu airpot, da Rofi'a na tafi ƴan uwanta na ta jin ba daɗi, musamman Isioma da ita ma ke ta roƙonsa Paapa nima a tafi da ni please.

Komawata America can ni ɗin ma haka aka samu ƙwararran likitan da ke bani kulawa wanda har gida yake zuwa, na faɗa musu ni yanzu bana jin ciwon komai, sun ƙi yarda a haka Dr ke ta cin kuɗinsu, tunda na tafin kuma Salim bai da natsuwa akai akai yake zuwa, ya zo yay ta ririta ni cike da so da ƙaunata a gare shi, haka kuma ya daki bidirinsa, ni kam ban hana shi abinda yake so.
Cikina na da wata bakwai ya bayyana sosai, don har ya kai wata shida ba zaka taɓa cewa ina da ciki ba, anata cewa ƙaramin ciki garen, wanda ba su sani ba ma cewa suke tumbi ne, amma ikon Allah shigarsa wata bakwai sai ka rantse ina cikin watan haihuwar ne.

Kuma babu wani ciwo da na ɗinka fama da shi tun farkon ciwon da nayi, kawai dai na kumbura ne kamar an zuba min yeast, har bana son kallon kaina a madubi wallahi saboda munin da nayi, Safiyya sai tayi ta kunna ni wai ai ance idan mace tayi muni idan tana da ciki to mummuna take haifa, ai kuwa nabi na damu da maganar, yo wake son haifar mummuna, sai da Salim ya kirata yaci ƙaniyarta tukunna ta shafa min lafiya. Sai dai shi kansa tsokanata yake da girman cikin, idan ya zo America yaje school ɗakko ni haka zai ta min vedio yana daga cikin mota, ni kuwa ina tafe ciki a gaba wurjanjan har kunya na ke ji, don dai ba yanda zan yi ne karatun ya zama dole amma da babu inda zan ke fita har sai na haihu.

Yau ya zo ɗaukana, ban san ya sauka a ƙasar ba, don bai faɗa min ba, mun dai yi waya yake cewa tunda mun kusa dawowa ba lallai ya ƙara zuwa ba shima suna bakin wani babban aiki ne, na fito daga gate ɗin makarantan ina tsaye ina jiran taxi, sai gani nayi mutum ya leƙo yana,"Madam turtsitsi shigo na rage miki hanya".

Ban mamakin ganin nasa ba don dama na san ba zai iya haƙurin ɗaukan lokacin da ya faɗa ba bai zo ya ganni ba. Na shiga motan ina cewa,"Mijin turtsitsi ya da zuwa ba sanarwa".

"To a kora ni mana ace ba'a son ganina ba'ai murna ba".

Cikin shauƙi na sarƙafo hannuna a nasa ina kwantar da kaina a kafaɗansa na ce,"Ni a wa na ce ban murna da ganin miji na gari ba, ina sonka mijina idan na ganka sai in rasa kalar farin cikin da na ke riskan kaina a ciki, banda ƴar uwata ma kaima ai ka san ba zan ke barinka ba".

"Umm matata nima kasa sukuni na ke idan bana tare da ke, shiyasa za ki ga bini bini na taho gareki, ba takura miki na ke ba wallahi ƙaunarki ce tayi min yawa, ina sonki mace ta gari me ladabi da biyayya, Allah ya ba ki aljannah ko don biyayyan da kike ma mijinki".

Na ƙanƙame shi ina amsawa da,"Amin ya Rahman".
Sai yace,"Rofi'a fa?".
Na ce,"Ai akwai school bus, yanzun ma na san an maida ita".

"Weldone Hajiyar Doller, ki zuba uban kuÉ—i kisata a wannan makarantan me tsada, ni da Kudrat ta faÉ—i mani fa ban yarda ba".

"Amfanin kuɗin uwa tayiwa ƴaƴanta hidima musamman ta ɓangaren ilimi".
"Haka ne, Allah ƙaro miki masu albarka, yanzu ban aron dubu ɗari biyu".

Ina dariya sosai na ce,"ÆŠari biyu jal".
"Madam ai ba a naira ba, ina nufin dala dubu É—ari biyu".
"To ka sha kuruminka Sadauki, tunda ka ba da wannan ajiyar mene ba za'a maka ba, ka san mu hausawa mun ce yaba kyauta tukwici, so ba bashi za'a baka ba, kyauta ma za'a baka".

"Lallai na kusa in zamar miki ɗan maraya kiyi ta jiƙani da doller, Madallah da ke Hajiyan doller Allah ƙara lafiya da buɗi, aci gaba da taimakon marayu".

Da jin daÉ—i mara misaltuwa na amsa da,"AMIN Hubbi nah, ba ni É—aya ba har da kai".

Kiss yay min a gishi sannan yace,"So'ida wallahi nayi matuƙar jin daɗin yanda kika so ƴaƴana, wallahi ban san ta yanda zan misalta miki daɗin da na ke ji ba akan ɗaukan yarana matsayin na ki da kika yi, haƙiƙa kin ƙara samun fada a zuciyata, kin ƙara samun gurbi me girma a raina, Allah yay miki albarka".

Satinsa uku da tafiya muka yi hutu, washe garin ranar da na dawo gida na fara naƙuda a tsaitsaye a tsaitsaye, ni ban ma ɗauka itan ba ce nayi zaton dai ciwon mara ne haka tunda ina ɗan taɓawa. Sai da na faɗawa Kudrat yanda na ke ji tukunna tace ai naƙuda ce. A ranar kuwa aka turo mana wata dattijuwa a cikin matan uncles ɗin Salim, da yake da muka sauka direct Aunty Adamma Anambra ta wuce.
Suka yi suka yi mu tafi asibiti na ce su bari ba haihuwar ba ce, Kudrat har taji haushina wai zan nuna musu ni likita ce kenan na san aikina.

Kwanana uku ina naƙuda a asibiti kafin Allah yasa na sulluɓo ƙaton Jaririna, yo ba dole ciki yay girma ba, kunga yaron kuwa masha Allah, godiya sai ga lillahi domin kuwa lafiya lau da ga ni har yarona, wayyo dama haka ake ji? Ni dai da aka bani yaron ji nayi kamar na tsaga ƙirjina na ɓoye shi a ciki, shi da mahaifinsa kamar an tsaga kara saboda tsananin kama, naji daɗi kuwa domin burina ne haihuwan kyakykyawa, bakin yaron ɗan ƙarami gashin ido har saman fuskarsa, take kuwa na shiga tofe abinda da ayoyin ubangiji, na tauna dabino a baki na zuba masa ruwan a bakinsa.
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR18FT5*
Zo kuga murna wurin Salim, Yana Abuja lokacin aka kirasa ƙarfe uku na dare, amma bayan asuba sai ga shi ya sauka.
Runguma babu kalar wadda ban sha ba a wajensa, kiss kamar zai cinye ko'ina na jikina, farin cikin da yake nunawa zaka ce ko don saboda haihuwar daga gare ni ne, a'a shi haka yake yau ko da Kudrat ce zata ƙara haihuwa iyaka farin cikin da zai nuna kenan da kuma kulawar da zai bada.

Ina kwance kan gadon shi yana gefe zaune da Babyn a hannunsa, da na motsa zai ce,"BabynBaby menene? Me kike so? Wani wurin ke miki ciwo? Faɗa min menene me kike so kin ji matata ta gari abar ƙaunata".

Sai dai kawai nayi murmushi na kaÉ—a masa kai in ce,"Babu komai Paapa, lafiya lau na ke, kai kawai na ke so kuma gaka a tare da ni".

Hannuna ya daɗa haɗewa da nasa da Babyn, ba zan iya ce masa ina jin ciwon mara sosai ba don sai ya bi ya tashi hankalinsa, ni kuwa ba na son ganin mijina a wannan yanayin, na fi son ganinsa a irin wannan yanayin da na ke ganinsa a yanzu riƙe da ɗansa na tsantsar farin ciki da annashuwa.
Chapter 107 · 0% Book details