← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 113

Sashe 110

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na sha wahala fiye da yanda baki zai faɗa da wannan cikin, don sai da ta kai ga mun tattara mun bar ƙasar mun koma America da zama, saboda in samu kulawa me kyau a wajen ƙwararrun likitocinsu na can, wannan lokacin kam da Umman Batula muka tafi Allah sarki da ke mijinta ya rasu satin sunan Ayman da komawarsu.
Ni kam har ina rubutawa Ayman wasiyya a diary, gani na ke kamar ba zan kai ba, bai zama lallai na haife abinda na ke ciki ba, ko da na haife ɗin to wataƙila ƴar uwata Fillo zan bi, in mutu in bar yaran da mahaifinsu, haka duk na karaya shiyasa sai na bi na rame saboda fargaban da ke tare da ni, ai kuwa hawan jini da ya kamani ni kaina da aka faɗan sai da na jijjiga, a matsayina na likita na san irin wannan hawan jinin babbar matsala ce ga rayuwar bawa, haɗari ne babba.

To amma a hankali da ke ina ta samun kalaman kwantar da hankali daga Mahbub, ga kuma iyayena suma da ko da yaushe cikin waya da su muke suna min kalaman ma su wanzar da natsuwa sai na fara daina damuwa da sanya tunani.
Har cikina ya shiga wata bakwai ban daina fama da ciwo ba, wannan cikin kam ɗan ƙarami da shi ana ta cewa mace zan haifa, kuma yana cikin wata na bakwan ne ƙoƙarin shiga na takwas na haife tagwaye na bakwai ni dukka maza, wannan lokacin ma kamar wancan da kaina na haihu kuma lafiya lau, sai dai ban yi dogon naƙuda ba kamar na haihuwan Ayman, wannan yini guda nayi na gama.
Yaran sai a machine aka saka su, saboda yanda aka haife su ɗin ƴan ƙananu da su, ni har tsoro ma suka ba ni, ce na ke ko ba su da kyan halitta ne, sai da aka tabbatar min da lafiyarsu lau tukunna hankalina ya kwanta, in ta kuka tunma da naga an raba ni da su an kai su can wani ɗaki daban acan ake rainon su.

Bamu komo najeriya ba nan muka zauna, Maa suka zo ita da su Kudrat da yaranmu, suka sauka a wani babban apertment, Ayman yana ganina yaron ko inda na ke bai zo ba yana maƙale jikin Kudrat, haka na figo shi bai san ina nan cikin ciwo cike da kewarsa ba, duk motsina tunaninsa na ke, ramar da na yi har da ƙulafucinsa da na saka a raina.

Wannan lokacin ma na ga gata da tarairaya wurin mijina da mahaifiyarsa duk da kasancewar ina kwance a asibiti, basa tafiya sai dare ƙarfe sha biyu, kuma duk inda takwas na safe yake sun tattaro sun taho asibitin, tare da su zamu yi break fast, Tagwayena in aka ciro su a machine aka kawo min haka na ke kwantar da su a ƙirjina cike da tausayin su da ƙaunarsu da ke bin kowacce jijiya ta jikina.
Cikar sati da haifan twins ɗina aka musu raɗin suna, Babban shi ne Abubakar Sadiq wanda ya ci sunan mahaifin Salim za mu ke ce masa Ajmal, ƙaramin kuma Umarul Faruq shi kuma yaci sunan sahabin Annabi ne, sunan yaren su Chidera da Kanayochukwu.

Wannan karan kam babu taron suna sai dai mun yi shagali iyamu yamu. Yo mene maraban ba mutanene kawai babu, amma batun kashe kuÉ—i ina kan gadon an kashe su, asibitin nan babu wanda bai samu rabon ordan snack É—in da aka yi ba, shanu uku Mahbub yasa aka yanka aka soya akai ta rabon nama a asibitin.
Sai da yaran suka cika kwana arba'in kafin aka yi discharging ɗina daga asibiti lokacin sun ƙara ƙwari, kuma wani ikon Allah a lokacin ka gansu ba zaka ce bakwaini ba ne, kamar mu guda da Umarul Faruq komai nawa ya ɗakko, Ayman da Ajmal kuwa zaka tsammaci tagwaye ne saboda tsananin kamansu, kuma sune kana ganinsu kaga kamannin mahaifinsu. Bamu dawo najeriya ba saboda ganin likita da na ke kai yaran, Kudrat da ma bayan suna suka koma da yaran saboda makaranta itama da wurin aikinta, Maa itama sai bayan sun tafi ta tafi, amma Ayman anan aka barsa wajena, sai da muka yi wata takwas a America sannan muka dawo najeriya, ba ƴaƴana kawai ba hatta Umman Batula ta sauya kamar ba ita ba, fata taji canjin yanayi.

Kan gado na ke zaune ina sawa Ajmal kaya, sa kayan da muke ta fama tun ɗazu, ya ƙi tsayawa sai yawo yake da ni, da yake haka yake gagaraf garaf, kwai ƙarfin tsiya, da kuzarinsa shi kam ba irin sauran ba, har cewa ake ko shi ne zai gaji Babansa ya zama soja. Ban isa fa na ajesa ba, tun bai cika wata biyu ba yake mirginawa, yanzu kuwa bana karambanin ma barinsa kan gado in tafi, tsab zai murgina ya wuntsilo daga kan gadon ya barni da ɗora hannu aka, in shiga uku da jaraban Babansa. Shi ɗin ranar yana hannunsa ya kwantar da shi akan kujeran falonsa, wai miƙewar da zai yi ya ɗakko abu kan dispenser sai jin yaronyay ya timo ƙasa, Allah ya so da katifansa a gefe ya faɗo kanta, kuma ko a jikinsa ba kuka, to ranar da a wajena ya faɗo sai nayi kuka saboda ihun faɗan da zan sha.
Umarul Faruq kam ba ruwansa, yanda na kwantar da shi hakan zan zo na samu kayana, idan ba wai bacci yay ba ya juya gefe, yanzu haka yana gefena a kwance salihin bawa in kunji ana cewa, da ace shi na ke sawa kaya muka ɗau lokacin nan da yanzu Ajmal na nan ya ɗagan dubaidar rayuwa da kuka, inaa ai shi bai yarda na barsa, ko bacci zai yo to sai dai fa yayi shi a bayana ko a jikina, shan nonosa kuwa har yay yawa don yafi Ayman, duk ya bi ya zuƙeni yaƙi bari nayi ƙiba, ko saboda shi ba zan bari su shekara biyu ba zan yaye su.

*B3ƘR20FT5*
Mahbub na zaune ƙasa kan carpet ya na gyarawa yara computer ɗin su da ta lallace, Ayman na tare da shi sai ƙiriniya yake masa yaƙi barsa yay aikinsa da kyau. Sai buga masa gwaranci yake yi. Ai ni kam na gode Allah da ya ban Ayman, yay ta haɗa min shirgi ko gajiya bai yi, idan mace ne ai na huta ina ga shekara biyar zan fara sata ɗora tukunya, wuyarta in gama gyara insha Allah kafin in waigo yayo min ɓari, idan kuwa kitchen na shiga duka durowoyin nan sai ya buɗe murafansu.

In ta faman mita ina ni ya ishe ni sai in sa ai masa rubutu ya nutsu, Mahbub yace in ƙyale masa yaro lafiya ce ba zan takura masa ɗa ba, har da shi bai ma ga fitinan da yake yi ba, na ce yo ina zaka gani ka tafi ka barmu da shi. Ile kuwa ranar sai ga shi yay masa ɓarin takardu kuma ya zauna akai ya saki fitsarinsa.
Ranar kuwa na yita ƙunshe dariyata, sai basarwa yay bai faɗa ba dai ya ɗauke shi ya kaiwa Babarsa, itama can ai gata da shi jiki duk manja tana faɗin,"Can kuje ku ƙarata, daga shiga kicin na ɗorasa saman island ya kifo min da manja da kayan miya gaba ɗaya, Babansa na gari ya dawo yanzu in banu yace ina sane na barsa ya kifar, daɗin ma kayan miyan ba su shigar masa ido ba da ina ga jaraban Babansa sai tasa na bar gidan yau".

Ni dai na ta musu dariya, Ayam É—ina idan yay fitinar sai dai kawai in girgiza kai na ce,"Allah ya gyara min kai".

To yanzun ma da Baban nasa ke aikin sai bi ya ke yana kwaso min kayan durowan su Ajmal yana kawo masa, shi kuma ya biye shi suna ta hiran, in ya kawo ya karɓa yace,"Yauwa Ayman ɗina to na gode sannu da aiki".

Tun yana biye masa sai da ya dawo ya koma ce masa,"Je kai wa Mommy". Can da ya ƙara kwaso kayan wankinsu sai ya zauna ya leƙa fuskan shi yana cewa,"Toda".
Ban san lokacin da na tuntsire da dariya ba, shima Mahbub É—in dariya ya saki yana ce masa,"Na'am É—an gidan Soja, Allah yay maka albarka ka ji yaron kirki, sannu da aiki, kwanta ka huta haka ai ka gaji".

Still ina dariyan na ce,"Ka ga idan baka hana shi faÉ—in sunanka haka ba wataran haka zai gatsa maka shi a gaban mutane".

"Ah to mene dan ya faÉ—a ba sunan Babansa ba ne".

Nayi ajiyan zuciya a raina inawa mijina adu'a gami da kyakykyawan fatan alkhairi. Haƙiƙa ina alfahari da tsintata cikin rayuwar wannan bawan nasa, idona naji ya cika da ƙwalla wadda ba ta komai ba ce face farin ciki, a kullum adu'a na ke wa uban ƴaƴana Allah yasa ya gama da duniya lafiya, ya raba shi da iyayensa lafiya, kuma ya sadamu da juna har a aljannah, ya kuma dawwamar da shi cikin farin ciki, ya ba ni ikon saka masa da irin alkhairan da yay min a rayuwa, na san ba zan taɓa iya biyansa ba sai dai na kimanta wajen kyautata masa da dukkan buƙatun da ya zo min da su.

Ba faɗa ko saɓani ya haɗamu fushin na ɗan ƙalilan ɗin lokaci ne, to idan ma faɗan ne dama akan ƴaƴansa ne zaka ji yana yi, ko sun yi ta'adi an musu faɗa sun kama kuka, ko ya zo ya tarar da Oga Soja yay ɓari to fa in ya fara sai ko ina ya amsa a gidan, yace ai muna kallonsa muka barsa yay ɓarnan, sai kuma azo a dame shi da ya siyo ya siyo.

"Myy wannan gyaran yafi ƙarfina, sai dai a barsa zan turo mai gyara ya zo ya duba musu, ko a siyo musu sabuwa dama wannan ɗin ai ta jima, sabuwan ma dai zan siyowa Farida Isioma da Rofi'a sai a gyara musu wannan ɗin, Ni wai garin ya akai ma suka lalata, abar da take saman table ya akai ta kifo".
Chapter 110 · 0% Book details