← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 113

Sashe 44

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uzuri yay musu domin kuwa zuri'arsu na da ƙarancin ilmin addini, kwata kwata basa martaba aure sai suke nunawa ƴaƴansu ai mijinsu ma bai isa da su ba, kuma ubansu ne jagoran nuna musu yin rashin mutuncin da suka ga dama a gidan aure, shi sai dai ƴarsa ta mulki gidanta ba mijinta ba, da ƴarsa ta ɗan yi complain sai ya kira mijinta ya kama cin mutuncinsa yana faɗa masa bai kai ba, bai kuma isa ba, idan zai iya zama da ƴarsa a yacca ta tsara zaman rayuwar gidanta to ya zauna da ita, kuma babu me sakar masa yarinya ta zama bazawara in har ka auri ƴaƴansa ka aura kenan.
To balle dama ita Zahra'u a gidan na su duk ita ce ilimin addini bai wadace ta ba sam, tafi ƙarfi a boko da koyarwar arna rabin rayuwarta duk a ƙasar turai tayi.

Fitowarsa kenan a wanka, bakin madubi ya ƙarasa yana goge sumar kansa da towel, ta cikin madubi yana bin ɗakin da ido, ɗakin kaca kaca babu gyara, kan kujera ma wankin kayansa ne na kwana huɗu da ya cire bata ɗauke su ba kuma ta da niyyar ɗaukewar. Zuciyarsa ta ƙuntata sosai, zai iya rantsewa ɗakinsa yafi sati bai ga tsintsiya ba, ƙamshi kuwa idan ba na jikinsa ba ko na jikinta to ba zai iya tuna rabon da ayi ma ɗakin turare ba, shi abun ma ɗaure kansa yake yi, bai taɓa tunanin mace na sauyawa har haka ba, abun Zahra'u yay yawa kuma ya fara isar sa.

Ransa duk a dagule ya gama shirinsa cikin sky blue É—in boyel, zagewa yay da kansa ya gyara É—akin yay fes fes, abun sai ya masa bambarakwai namiji da suna hajara, wai shi ne da da gyara É—aki yau, rabonsa da hakan tun samartaka. Yana gamawa ya kulle ya fita zuwa É—akinta, kwance ya sameta tana baccin asarar da ta saba da yake yau weekend babu aiki, ya kai hannu yana tashinta, ta jisa ba wai bata jisa ba ya sani, amma idan zai awa guda yana tashin nata ba fa zata motsa ba balle ta buÉ—e ido ta san yana yi.
Yau kam bata isa yay mata yanda ya saba ba na zaman jiranta har lokacin da ta ga damar tashi, don haka ya buÉ—e toilet ya É—ebo ruwa yana zuwa ya fetsa mata a fuska, ta tashi a firgice tana faÉ—i,"Mene haka? Akan me zaka watsa min ruwa? Idan na tashi É—in me zan baka ne?". Ta faÉ—a cikin masifa da hargagi.

"Amma ai na faɗa miki tun da sassafe ki shirya zamu tafi asibiti, shi ne za ki zo ki nemi wuri ki kwanta ke da bacci ba ya taɓa isarki, dun kin bi kin zama malalaciya ɗakin mijinki ma ba zaki iya tsaftace shi ba".

Wani kallo ta watsa masa tare da cewa,"Na dai fi ƙarfin ka ce min ƙazama, ɗakinka kuma ba ce kayi baka so ƴan aiki suke gyara maka ba, ni kuwa na faɗa maka ba zan iya stressing kaina da aiki ba, da wanne zan ji ga aikin office ga na gida, kai ko tausaywa mutum baka yi, idan kaga ba zaka iya zama da ɗakin naka a haka ma ka gyara da kanka mana".

Ta faÉ—i hakan tana neman komawa ta kwanta ya dakatar da ita,"Ke dalla malama mene hakan wai, zaman jiranki zan ta yi sai lokacin da kika ga damar shiryawa tukunna".

"To wai Nazifi idan na sakko nayi maka mene don Allah, me zai kaimu asibiti alhalin lafiyata ƙalau kaima lafiyarka ƙalau haka ma ƴarmu lafiyarta ƙalau".

"Amma ai na faɗa miki cewar yau da asuba an kwantar da Iyam ko, ke kwata kwata ba ki san abin da ya dace ba, me yasa kika zama mara mutunci ne, na ki iyayen kawai ke da daraja da ƙima a wurinki nawa kuma kin raina su kin mayar da su mutanen banza".

"Ni dai kar ka ce zaka zagi mahaifana, kuma kar ka ƙara ce min ban da mutunci, asibiti ne ba zanje ba a yanzu kayi tafiyarka kawai, idan na tashi na biyo bayanka, ni kenan kullum ina kan hanyar asibiti zaman jinyar suruka".

Tayi maganar tana komawa ta kwanta.
"Ke ba fa zai yiwu ba, na rantse da Allah Zahra'u idan ba ki sakko kin shirya mun tafi ba in ranki yay dubu sai ya ɓaci, Me kika mayar da ni ne, sakaran miji shashasha wanda sai yadda matarsa tayi da shi, to wallahi ba zan ci gaba da ɗaukar halin iskancinkin nan ba, ni ke aurenki saboda haka dole ki bi umarni na kuma ya zamar miki dole ki girmama min iyaye, yanda sauran matan ƴan uwana ke zuwa su zauna a asibiti tare da mahaifiyarmu haka kema, ki sakko ki shirya mu tafi"

Yay maganar cikin tsawa da ɗaga murya na gaske, wanda har sai da ita kanta ta tsorata da yanayin da ya ke neman rikiɗe mata. Tana ƙunƙuni ta sakko a gadon ta shiga toilet wai sai ta sake yin wanka du dai don ta ɓata masa lokaci. Shi kuma ya fita yana ɗaga kiran waya. Bayan kusan minti goma sha biyar ya leƙo tsammaninsa ta gama shiryawa sai gani yay a sannan ne ma take wa Iman wanka, gajeran tsaki yay na takaici kafin yace da ita,"Kuma na ce ki bani ATM ko".

Tayi kamar bata jisa ba sai da ya ƙara yin magana tukunna tace,"Wai wanne ATM?".

"Ban sani ba, ke dalla na gaji da rainin hankalinki, zan tambaye ki ATM É—inki ne uban me zan a shi".

"Amma ai na faɗa maka babu ko sisi a ciki ko, duk na kwashe kuɗin na siya mata kadarori, dama kaima ai ba naka ba ne na ƴaƴana ne to mene kuma abin zuwa ka dinga takura min da cewa na baka. To ni duk na siya musu kadarori don babu amfanin aje kuɗin kawai ana zuba musu ido, kuma ni ATM ɗin ma tuni ya ɓata nayi duban duk ban gansa ba, sai blocking nayi".

"To me ya hana kiyi shawara da ni kafin yanke hukuncin hakan, ko Æ´ar taki ce ke É—aya".

Shiru tayi masa taƙi cewa komai. Sai da ta gama shiryawa tukunna ya sake ce mata. "To ki tura min kuɗin da na saka a ciki jiya don da sune za'ai amfanin asibitin Iyam".

Ta buÉ—e baki da cewa,"Amma to Daddyn Iman baka faÉ—a min ba tun lokacin da ka tura, ai ni suna shigowa na turawa Mami su nace a siyawa Iman zoben gwal, naga ba account É—inka ba ne ban tsammaci kuÉ—inka ka saka ba".

Kallon ba ki da hankali yay mata kamin yace,"Zoben gwal? Da duka miliyan ɗayan? Zahra'u wai me yasa ba ki san ciwon kuɗi ba ne, ba fa zuwa na ke na tsinko kuɗin nan ba, ko tsinkowar na ke ai da wahala, akan wanne dalili za ki siyawa ƙaramar yarinya zoben gwal mene fa'idar hakan, anya kina da hankali kuwa, kuma ban faɗa miki cewa na samu matsalar account ba sai naje nayi babban gyara".

Ta ɓata fuska tana mitar. "Ni don Allah Daddyn Iman ka daina yawan min faɗa akan irin haka, mecece miliyan ɗaya a wurinka Allah na tuba, cikin dukiyarka aka taɓa miliyan ɗaya me aka cira, amma a kwanakin nan sai wasu abubuwa ka ke yi akan kuɗi kamar wanda bai da su".

Ƙugu ya kama da hannu ɗaya yana jijjiga ƙafa, ya fara zirga zirga ya rasa me ke masa daɗi. Ita dai tsayawa tayi tana kallonsa kafin tace,"Wai lafiya?".

Nunfashi ya sauke me nauyi yace,"Wuce muje".

Gaba tayi yana biye da ita a baya, har suka shiga mota bai daina mita ba akan kuɗin da ta taɓa, da yacca take ɓarnatar masa da dukiya saboda bata san zafin nemansu ba. Earpice tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da faɗan da yake ta mata tunda suka taho, kuma ba zata iya ci gaba da jin maganarsa da yake na zata basa takardun filayen da duk tace ta siya ai ba hauka ake a iya waɗanda ya mallaka musu ma ya ishe su, ko kuma ta basa na Noor tun da ita ta mutu.

Har dai suka je asibitin bata ƙara ce masa kanzil ba tun bayan ce masa da tayi Daddyn Iman ka koyi son kuɗi yanzu ko baka da shi sai haka.

Zuwansu aka fara bari a shiga É—akin da Iyam ke kwance, Zahra'u ya bari ya tafi can office É—in likita shi da Yaya Babba da Yayan Shago.
Su Yaya duk suna nan zaune bakin ƙofa an zabga tagumi, Zahra'u ta miƙe ta shiga ciki, babu wanda ta kula a cikinsu tun da ta zo, Jamila matar Yaya Babba ma da tayi mata magana shareta tayi.

"Ina wuni". Iyam na kallonta cikin wahalar ciwo tace,"Lafiya lau Zahra'u, kuna nan lafiya".

"Lafiya lau, sannu Allah sawwaƙe".
"Amin na gode Allah yayi muku albarka".
Tana maganar ne tana kallon Iman da Zahra'u kewa wasa tana ta ɓaɓɓaka dariya.

Nazifi ya shigo bayan sun gaisa ya shiga tambayarta yanayin yanda take jin jikin, yana kuma faɗa mata yanda suka yi da likitocin akan wataƙila sai an fita da ita waje acan za'a yi mata aikin ƙashin kwankwasonta, bai dai san yanda zai mata bayanin kuɗin da ake nema ba don duk wanda zai faɗawa cewa bai da adadin kuɗin da aka nema sai an ƙaryata shi.
Sai yay jugum da ka gansa dai ka san yana da tarin damuwa a tare da shi wadda ke neman fin ƙarfinsa, Iyam ta lura da hakan ta tambaye shi ko wata matsalar ce yace ciwon nata ne kawai damuwarsa.
Chapter 44 · 0% Book details