Sashe 53
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaji belt ɗin ma ba zata masa yanda yake so ba kawai sai ya koma sa ƙafa yana bal da ita yana kai mata kutufo da hannu.
"Wallahi ba ki isa kin kashe min ɗana ba, idan har cikina ya zube da gaske sai na nakasta ki, sai na barki da mummunan tabon da ba zai taɓa gogewa ba a jikin ki, ko ban kasheki ba sai na zama sanadin da za ki daina farin ciki har abada".
Sai da yay mata mugun duka tukunna ya barta yana huci ba don ya gaji ba ko kuma hakan yay masa. Hankalinsa ne ya tattara ya kaÉ—a yay asibiti wurin Iyam.
Ita kuma ta miƙe da ƙyar cikin wahala tana faɗin,"Kuma wallahi baka duki banza ba, sai ka san ni ka yiwa wannan dukan Nazifi, mugu azzalumi, Allah ya isana da ka cuce ni ka aure ni".
"Dilla can rufe min ba ki, ni da ke wa ya kamata yay Allah ya isa, ban da ƙaddara me zai sa na aure ki, auren bagidajiya mara ilimin addini, kuma Allah ya isa da kika zama sanadiyar da na rasa matata, matar arziƙi...Tun da na aure ki ban huta ba, kullum cikin ganin masifu na ke iri iri, mene a cikin auren na ki banda tarin takaici da nadama, ai tuni na fahimci ba don Allah kika aure ni ba sai saboda dukiyata, kuma kije na sake ki saki ɗaya, kar kuma ki sake ki tafi da ko tsinke da na mallakawa yarinyata, ki aje min yarinya da duk abin da na mallaka mata".
Ya faɗa yana hanzarin shiga banɗaki jikinsa sai rawa yake yi, haka zuciyarsa tamkar zata fito waje saboda ɓacin rai.
"Allah ya isana tun da ka mayar da ni bazawara, wallahi ba zan yafe maka ba sai mahaifina ya É—auka min fansa".
Tana ta surutanta ya shiga bandaƙi, ko minti biyar bai yi ba cikakke ya fito, shi kansa ya san ba wanka kirki yay ba. Jallabiyar da ya cire ya mayar ya kwashi wayarsa da maƙullai ya fita falo.
Can ya sameta tana aikin zage zage tana faɗawa Babanta wai Nazifi yay mata duka har sai da cikin jikinta ya zube, Daddy ayi ƙararsa kotu ba zan yarda ba sai alƙali yabi min hakkina.
Iman tana hannunta ya fizge ƴarsa da ke ta kuka. Sai da yaje bakin ƙofa sannan ya tsaya ya juyo yana kallonta da cewa,"Idan kika bari na dawo gidan nan na same ki ban san illar da zan yi miki ba".
Ya fice a fusace, yacca yake tuƙi kuwa kana gani kasan na cikin motar ba lafiya ƙalau ba akwai matsala ta tashin hankali, ga kukan Iman duk ya daɗa ɗaga hankalinsa wacca tuni ya fara tunanin wacca uwar zai nema mata? Wacece zata kula da yarinyarsa bisa ruƙo na gaskiya da amana? Wace zata bata ingantacciyar tarbiyar da yake fatan yaransa su samu? Wacece zata yi duk iyaka ƙoƙarin wajen ganin sun wadatu da ilimi ta kowanne fanni musamman na addini?
Wayarsa tana ta ƙara yaƙi ɗagawa sai da yaji kiran yay yawa tukunna, ganin likitan Iyam ne sai ya ɗaga da sauri, likitan yace masa zai bar asibiti ne ga result ɗin gwajin da aka masa ya fito, kwanaki ne yay fama da wani azababben ciwon ciki da mara a haɗe har sai da ya saddaƙar mutuwa zai yi.
Da ƙosawar yaji menene ya shiga tambayar likitan sakamakon, saboda ko a lokacin likitan yace masa kamar matsalar babba ce amma dai sai result ya fito za su tabbatar.
Likitan yace masa ya ƙaraso ɗin dai tukunna amma ya zo da sauri don zai fita ya bar asibitin saboda akwai wani asibitin da zai je zai yi aikin tiyata yanzu.
Kashe wayar yay ya ƙarawa motar gudu, yana shiga asibitin ya miƙawa Fati Iman yace ta goyata, duk ganin yanayinsa kamar ba shi ba a wani rikiɗe suka tafi ruuu suna tambayarsa lafiya. Kai tsaye yace da Yaya,"Zahra'u ta zubar min da ciki, na mata dukan fitar hayyaci na kuma saketa, Yaya ki kirata ki shaida matta kar na koma gidana na sameta idan ba haka ba wallahi ko ban kasheta ba sai na kusa kasheta".
Yana faÉ—in hakan ya faÉ—a ofishin Doctor, Yaya ta kama salati tana sallallami, ce take mun shiga uku an ta sake saken aure kenan, Nazifi me yasa ka kasa sarrafa zuciyarka kai kuwa. Yanzu wanne hali Iyam zata shiga idan taji wannan zancen.
Shi kuwa yana can gaban likita zaune ya fito da takardun cikin file É—insa yana yi masa bayanin cewa.
"Akwai abin da muke kira da Disruptions in hormonal levels, ma'ana dai ka samu low testosterone, sperm production ya ragu sosai wanda dalilin hakan haihuwa ta ɗauke maka, baya ga haka ma still akwai Hormonal Imbalances wato rashin daidaituwar ƙwan halittarka...".
Gaba ɗaya ma sai ya daina ji da gane bayanan da likitan ke masa, to me yay saura da zai ji? Duk sauran bayanin dai akan cutar ne, gundarin ciwon kuma an faɗa masa, kalma ɗaya ya riƙe haihuwa ta tsaya maka ba zaka kuma haihuwa ba! Wannan Kalmar me ɗacin ɗanɗano daga ina haka! Garin ma ya hakan zata faru da shi? Daga ƴar karamar cuta sai binkicensu na ƙarya ya bada sakamakon daina haihuwa?
Bai san wanna tunani zai yi ba kuma bai san me zan iya cewa da danganta maganar likitan akai ba, abu É—aya ya sani ya É—aga hannu ya dakatar da likita daga bayanansa, sannan kuma hannunsa na rawa ya zaro wayarsa a aljihu ya danna kiran mahaifin Zahra'u yace masa,"Na mayar da aurenmu Daddy".
Daga wannan maganar kuma sai ya dafe ƙirjinsa da yake jin zuciyarsa na barazanar fitowa waje, har ta kai ga ya faɗo a saman kujera bai sani ba, haka kuma ba tare da sanin nasa ba likita yaji yana ambaton,"Hasbunallahu wani'imal wakil, Astagfirullah ya Allah, tabbas na maka wani laifin da ban sa ni da na ke amsar hukunci ka yafe min Allah na".
Sai ya koma cewa da likitan ya taimaka masa zuciyarsa zata fito.
_________________
₦500
07018098175
*B2ƘR25FT5*
Likita ya taso da sauri yayo kansa, ya kama shi ya mayar da shi kan kujerar ya zauna.wani irin numfashi ya ke saukewa me wahala, likitan na ta jera masa tambayar,"Dama baka da lafiya baka min bayani ba, ai you should have let me know, me ka ke ji a ƙirjin naka?".
Bai iya ce masa komai ba kuma ba zai iya cewa da shi komai ɗin ba, likitan yay ƙoƙarin ɗora Stethoscope ya dakatar da shi da cewa,"Bar ni likita bana buƙatan komai, na gode".
Yana faɗin hakan ya kifa kansa kan table, shin me ya aikata a rayuwarsa ne haka da abubuwa marasa daɗi ke ta ƙwallo da shi? A tarihin rayuwarsa yau ita ce rana ta biyu da zai iya cewa ya shiga tashin hankalin da yake jin zai iya haɗiyar zuciya ya mutu ya huta.
Kusan mintuna goma yana zaune a hakan yana ta biyo innalillahi a bakinsa, natsuwarsa ma da yake so ya samu ya kasa samunta, kansa yay masa bala'in nauyi wanda in da za'a cire masa tabbas zai so hakan matuƙa.
Bayanin likita ne ke ta faman tariya a cikin kansa, yayin da hoton Zahra'u ke ta haskawa a cikin ƙwayar idonsa san da take shan maganin zubar da ciki, shikenan ta gama da shi, ta cuce shi, kuma ba zai taɓa yafe mata ba, yanzu shikenan kuma shi da wata haihuwar har mutuwa, kawai sai Noor ta faɗo masa, a hankali ya furta Allah ya isa tsakanina da ke Sa'ida da kika raba ni da yarinyata.
Dafa kujerar yay ya miƙe da ƙyar, ya dubi likitan da ƙwayar idanuwansa masu nauyi waɗanda ɓacin rai, tashin hankali, da gangamin damuwa sukawa ƙawanya.
Fita yay a office ɗin a daddafe, likita na ta ce masa ya tsaya ya karɓi takardunsa bai ko masa magana ba kawai ya buɗe ƙofa ya fice.
Can ya iske su Yaya zazzaune, tana ganinsa ta shiga tambayarsa lafiya duba da yanayinsa da ya kasa ɓoye halin da yake ciki.
"Iyam ta tashi?". Ya faɗa da ƙyar da amon muryar da ya zama tamkar ba nasa ba.
"Bata tashi ba, wai wani abu ne ke faruwa? Me likitan yace maka?".
Ya rumtse idonsa ya girgiza shi, sannan yasa hannu ya shafo kansa.
"Ina Lubabatu?".
"Basu jima da fita ba Iman taƙi shiru, taje siyo mata biscuite".
Bai ce komai ba ya nufi ɗakin da Iyam take ya buɗa ya shiga, tana bacci har yanzu, babu wanda zai ga tsohuwar nan bai ji ƙwalla ta taru a idonsa ba, saboda yanda ta rame ta yamutse, ƙasusuwan jikinta na ko'ina ya fito tamkar zasu yi magana, ya ilahi wannan rayuwa Allah ka mana da sauƙi.
Gaban gadon yaje ya zauna akan kujera, ya daɗe yana kallon fuskarta, ya kai yatsu ya kara a ƙasan hancinta saboda wani motsi da zuciyarsa tayi na tsoro gani yake kamar bata numfashi.
Sai da yaji numfashinta na fita ya sauke doguwar ajiyar zuciya, ya kama hannunta ya ruƙo ya ɗora a saman kansa. "Na sani a ko da yaushe adu'arki na tare da ni, Allah ya ba ki lafiya ya tashi kafaɗunki".
Da haka ya miƙe ya fita cikin matuƙar sanyin jiki, lissafinsa guda ɗaya ne kawai a yanzu wanda zuciyarsa ta yanke masa shawaran ya siyar da gidansa kawai ya biya kuɗin aikin mahaifiyarsa, wannan ɓata lokacin da jiran tsammanin da yake ko saboda shi sai Allah ya hukunta shi, tana ta shan wuya kullum, ga shi yanzu ma dubu sittin ɗin da suke ci a kullum nema take ta gagara don a yanzu bai da kuɗin na yau da zai tura, sai dai kuma ko me za'ai yau sai Zahra'u ta fito da duk wasu abubuwa da ya mallakawa ƴarsa.