← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 113

Sashe 108

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yamma aka sallame mu muka koma gida. Jego na ke me cike da daɗi, gata ta ko'ina an mayar da ni tamkar ƴar gwal, miji yanai ƴan uwansa na yi, nawa dangin na min, kwanana biyu da haihuwan Mama A'i ta ƙara dawowa ita zata min zaman wanka, ni da ta zo ce na ke da kayan fara sana'a ta taho, wai ashe kayan barka da jego ne kawai aka tulumota da su ta kawo min, dama tun kan haihuwar naji Ummani na faɗin an haɗa sabulu wanka, to ashe har dakan yajinta tayi botikin fenti guda biyu.

Ga kayan sanyin jariri na injin saƙa me kyau, set har huɗu don ana zuwa ma da su na cire sky blue colour ɗin na cewa Mama A'i a saka masa kayan Kakarsa. Zannuwan turame kuwa masu sauƙin kuɗi kala shida, abinka da ƴar gidan me siyar da su, banda manyan atamfa da kowacce zata yi dubu bakwai guda huɗu, da sabbin hijabai na ɗinkin zama ni, ga falle falle na wankan jariri guda uku shima, ga zanin goyo na saƙa shima me kauri guda biyu, ko ba'a saka masa kayan sanyi ba aka goya shi da iya shawul ɗin ai ya isa yaji ɗumi, zoben azurfa kuwa ina gani shima na san daga Abbaa ne, takalman jarirai guda uku suma masu kyau haka ya siyawa jikansa. Turarukan wuta kuwa masu bala'in ƙamshi na jego manyan kwalabe huɗu suma, da humran jariri, kai wato ina nan ashe Hajiya Ummanita na can tana shirin saukar jika.
Yashaik da Yaya Imam kuwa kuÉ—i suka tura min, da zolayarsu suka ce,"Duk da ke Hajiya Sa'ida ce amma dai ga wannan a siyawa É—an mu turare, Allah yay masa albarka".

Naji daÉ—in kyautan na su sosai, muka yi waya da Ummanin ina zuba na ce,"Ummani ina zan kai wannan yajin da aka kawo?".

Ta ce,"Yo ai dama na rabo ne ba kawo miki aka yi ki tasa a gaba ki ta ci ba, ki bayar a aika gidan su nasu ne, idan wani zai zo ga na ku ke da Kudrat sai a taho muku da shi. Abbaanku ya ba da rubutu za ki gani ke da jaririn za ku dinƙa sha, wannan baƙin zaren kuma a ɗaura masa a hannu saboda bakin mutane, azurfar ma yace ki saka masa ita ma ta baki ce naji ance jikan nawa kamar balarabe, kinga ba ma zauna ba".

Na kada baki na ce,"Ai Ummani na iya haihuwan ɗa, ki gode Allah na haifa miki jika me kama da larabawa, sai ma dai kin gansa tukunna za ki ji kamar ki riƙe".

Tana murmushi ta ce,"Ina zan riƙe shi uwarsa tayi ƙarata".

kai ni dai ban san haka na ke ƴar gata ba sai da na haihu. Maa bini bini ta kira ni ta ce,"Daughter ya kike da Jikana?". In ce mata muna cikin ƙoshin lafiya.
Ana gobe suna ƴan uwana suka zo, Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Saudatu, Umman Batula, Hajjo, har da ƴaƴan wajen Hajjo Juwan da Safna, ƴaƴan wurin Baba Tijjani kuwa babu ko mutum guda, na rasa ranar da zasu gane duniya ba wurin zama ba ce su daina jin haushinmu suna gaba da mu, amma abin na su gaba gaba ma yake yi, musamman ma da suka ga yanda na koma da irin mijin kece rainin da n ake aure, duk sai suka ƙara ƙullatarmu ni da mahaifiyata, mu kuwa duk basa gabanmu. Ni dai naji daɗin ganin iya wa'annan ma da sua zo matuƙa, ranar har rasa inda zan tsoma raina nayi saboda daɗi.

Har ranar suna ban san da wanne suna Mahbub yaywa jaririn huÉ—uba ba, tunda na haifesa na ke ta tambayansa wanne suna ya saka masa sai yay murmushi yace,"Myy ki bari ai sai ranar suna ake faÉ—a ko".

Na ce,"To ai dai ka san wanda zaka saka tunda ka masa huÉ—uba, ni ba Mamansa ba ce, tsakani da Allah sai ace nima sai ranar da kowa zai ji nima zan ji".

Ya ce,"To me ɗa, ai kaɗai kika yi aikin haihuwan, sunana ne to nasa amma sai ranar naɗin suna kema za ki ji, da ake min gori da ban bayar ba a haifa ne, kima gode min ki ban kyauta na iya jefa ƙwallo a raga".

Dukan wasa kawai na kai masa a ƙirji, duk nacin da na saka masa sai da na haƙura. Ina ɓata fuska na ce,"Kuma ma idan suna mara daɗi ne ka saka masa idan ba sai ka ƙara yanka rago ka sauya masa ba".

Ranar sunan bayan ya dawo daga masallacin asuba, ina É—aki na fito a wanka kenan, sai ga Rofi'a da gudunta ta faÉ—o jikina, na É—auketa ina cewa,"Rofi'a na haneki wannan gudun, tiles É—in nan bai da amana akwai santsi, wa ma ya tasar min ke da wannan farar asubar?".

Cikin gwarancinta tace min,"Paapa yace kije yanzu, Mommy yau a goya min Baby".

Na É—aga mata kai,"Ehh za'a goya miki".

Na ajiyeta, na karɓi jaririn a hannun Mama A'i da ta gama shirya shi, ɗan albarka ba dai kuka ba da tsotso, daga karɓarsa har ya farka a barcin da ya fara zai yi halin kukan. Na yafa babban towel akaina ban tsaya shiryawa ba, ni kam ban ɓata lokaci wajen amsa kiran mijina, na fita a ɗakin ina ta yiwa yarona wasa duk da uban kukan da yake tsalawa, ni dai hakan ma daɗi yake min, ina kallonsa da murmushi ina shaƙe ƙamshin turaren da aka fesa ma kayansa masu kyau.

Yana zaune kan carpet ya baje alawan suna da biscuite na same shi, hannu ya miƙa ya ɗakko filo yasa min na zauna akai, ina gaida shi bai amsa ba ya hauni da faɗan bar masa yaro da nayi yana kuka.
Ni kam ban jin daɗin wannan faɗan nasa wallahi, yana gani fa duk yaron ya ruɗa ni amma ce yake ina ɗaukar hakkin yaro. Ina gyara zan ba shi nace,"Mahbub ka fa san halinsa da kuka, yanzu na fito a wanka na karɓe shi hannun Mama A'i, kuma wallahi bacci ma yake yi fa, na taho zan zame zani ne a hanya ina ba shi".

Wani kallo yay min da cewa,"A waje kike, ba cikin gidanki ba ne, zanen ai ba duka za ki kunce ba ko".

Ni dai ganin ya hasala na shiga ba shi haƙuri, kuma a hakan saboda yaron yaƙi kama nono nan ma ban tsira ba laifina ne. "Myy ba na son irin haka, bana jin daɗin kukan yaron nan wallahi, ke idan ni ina da nonon basa ma kya ga ina miki faɗan ne balle har kike cin magani kina turo ba ki gaba".

Kamar zan kuka na ce,"To kaga fa yaƙi kamawa".

"Ta ina zai kama dama, har yanzu kin kasa koyar yanda za ki dinƙa ba shi, wannan rashin imani ne kawai, na rantse miki idan ɗana ya samu matsala akan rashin samun ruwan nono idan ranki yay dubu sai ya ɓaci".

Idona ya ciko da ruwa kawai na saki nonon ina ce masa,"Ai sai ka basa da kanka tunda kai ka fini iyawan".

Ya galla min harara yana kama nonon ya saka masa a baki, kuma da gasken ne ya fini iyawa, ni ko da yaushe haka muke fama wajen saka masa a bakin, kuma idan na tashi in rufe masa hanci, ko bai niyyan kukan ba sai ya tsanyare dalilin hakan, Mama A'i tayi ta faÉ—a kamar zata buge ni.

Ina aikin ɓata fuska kan faɗan da yay min ina kallon yanda ya riƙe nonon da kyau ya saita yaron na ta sha abinsa, na jisa yana cewa,"Suna yaci, me zamu dinga ce masa?".

Lokaci guda na bar fushin, na bar kallona daga kan jaririna na dube shi ina murmushi na ce,"Sunan wa yaci?".

"Ke dai ina ruwanki, laƙabi kawai na tambaye ki".

Na san ba zai wuce sunan mahaifinsa ya saka ba, na dubi yaron ina kallonsa cike da wannan soyayyar da take daban da kowacce soyayya wato soyayyar uwa, na shafo sumar kansa ina cewa,"Ayman yayi?".

Sai shima ya É—ora nasa hannun saman nawa muna shafa kan yaron a hankali yace,"Da yare kuma muce masa Emeka".

Nace,"Wow, to Mahbub baka faÉ—a min ainihin sunansa ba ai".
Ya manna gefen fuskarsa da tawa cikin kunnena ya raÉ—a min,"Sunan Abbaa".

Ban san sanda na juyo gaba É—aya ina sakin Ayman ba in fuskanci mahaifinsa. "Mahbub sunan Abbaa nah ka saka?".

Ya jijjiga min kai yana shafa fuskana, na rungume mijina cikin hawayen farin ciki da jin daɗin da suka shiga sakko min. Godiya na ke masa ina kwarara masa adu'a iri iri. Wallahi sai na ƙara jin sabuwar ƙaunarsa ta kama ni, darajarsa da kimarsa da mutuncinsa sun daɗa hauhawa a idona, ina ƙara alfaharin samunsa a rayuwata, ta kai ga har na fashe da kuka wanda ba na komai ba ne sai tsantsan farin ciki.
Ban ma iya tashi naje É—akina É—akko wayata ba, da wayarsa na kira Abbaa na shaida masa Salim yay masa takwara, Abbaa shima yaji daÉ—i sosai.

Cewa yake,"Da gaske Salman yay takwara Salman, ai kuwa mun gode da wannan kara da aka yi mana, Allah ya albarkaci rayuwan Salman yasa ya zama mahaddacin alqur'ani".

Na haÉ—a su a waya Abbaa na ta saka masa albarka da adu'a, irin adu'an da har sai da jikin Salim yay sanyi.

Nima ɗin adu'a na ke daɗa masa ina cewa,"Allah yasa ƴaƴanka su zama masu jin ƙanka".
Ƙarfe goma muka shirya muka tafi can gidansu Anambra, da ke a can ne za'a yi taron sunan, gida ya cika maƙil da jama'a, kuma iyaka familyn su ne ba wasu ba, sai abokan wajen aikina, to sai jama'ar Kudrat ma da ta yo gayya guda ita uwar ɗa, sai ƴan uwana da ba su wuce ƙirgen yatsun hannu ba.
Ranar dai anyi shagalin suna iya shagali, taro na gani a fada na a buga a jarida, kuma an buga É—in kuwa, yau an wayi gari Sa'ida Salman da yarona Salman sun kafa tarihin shiga jaridar duniya.
Chapter 108 · 0% Book details