Sashe 20
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina cikin saka kaya sai ga shi ya shigo É—akin har lokacin faÉ—an yake yi.
"Ban san me kika taka ba Sa'ida da rashin mutunciki na raina ni ya hauhawa, har ina miki magana za ki banza da ni alhalin kina jina, kuma saboda tsabar rashin sanin darajar miji da rashin ilimi ina miki faɗa zaki fito ki barni wato ga kare na haushi ko, kin yi laifi ba zaki iya bada haƙuri ba saboda girman kai".
"Ka gane finka sanin ya kamata nayi da aiki da ilimin shiyasa na baro cikin yara, kai a ganinka kana faɗa gabansu hakan na maka daɗi ba burgewa da cinyewa ba ne, domin kuwa zasu daina ganin girman da kake da shi a idonsu ko da ace ɗan da ka haifa da cikinka ne, hakan ma ba tarbiyya ba ne, ƴaƴa mata aka baka kuma wataran aurar da su zaka yi ka kai wa wani...kuma kana ƙara daga murya ne saboda matarka taji, ai gani a ɗakin da gani sai kai kana iya kiranta tazo nan ɗin ba sai ta tsaya iya ji ba, gani da ido ai ya kori ji. Sannan kar ka ƙara alaƙanta ni da kalmar girman kai don ni ƴar Aljanna ce kaima ka sani".
Wai Æ´ar wannan maganar da nayi sai ta zama ciwo, har yana nuna ni da yatsa yana cewa,"Wato kin yi bakin da ba zan faÉ—a ba sai kin faÉ—a kema, to na rantse da Allah zan koya miki hankali, zan baki mamaki dan na lura har yanzu ba ki gama sanina ba".
Nace,"Ina kuwa zan gama saninka Nazifi, ai har yanzu ma ban sanka ba domin kasha gaban tunanina. Kuma duk wannan Bala'in dai da kake akan ka baro wajenta ne, to ka koma mana ai ban riƙe ka ba, ƙarƙarina nayi kallo ranar ƙiyama, wanda ya shiga kwanan wata ai ya san makomarsa Nazifi Mai Kalwa".
Hankaɗa ƙofar yay ya rufe har sai da na tsorata, ya wuce ni fuuu zuwa banɗaki. Na taɓe baki na zauna kan kafet, ai yanzu kam sam bana tsoronsa bana shakkarsa, na daina masa shiru ina ƙyale shi yay duk bala'insa da zai yi, barazana ce kawai na ke jira ya fara kafin itama ya aiwatar. na ɗauko wayata na kunna data, kai tsaye group na ajin koyar da english na shiga don ni yanzu ya fiye min komai da ke cikin gidan nan. Hasalima ina mancewa da ɓacin rai muddin na shiga ina karatuna.
Sai bayan ya fito a wanka yay shigar bacci kana ya zauna yana ce min,"Abincina fa?".
Kamar ba zan tanka shi ba can kuma na ce,"Ina naga lafiyar da zan iya wani girki".
"Kamar ya? Ba kin ji sauƙi ba".
"Da na ji sauƙin ban gama hutawa ba ne shiyasa".
"Duk ba abin da ku ka ci kenan?".
"Mun ci mana".
"Kuma sai wanda za'a dafa min ya gagara ba? Da ban kawo na ajiye ba kuma a kira ni da azzalumin miji".
Wani kallo na masa sai kawai na aje wayata na miƙe na fita, ba jimawa na dawo riƙe da ɗan ƙaramin flask na miya da cokali duk a hannu, kan teburin da ke gabansa na ajiye na ce,"Ga sauran da muka rage". Na faɗa yayin da na ke buɗe masa flask ɗin, wata ƴar guntuwar shinkafa ce bata fi cokali huɗu ba, ko ƙaramin yaro yaci ba ƙoshi zai yi ba, ta ƙandashe sanyi ƙalau, Saudatu ce da ƙiwa yau tayi jallof babu cikakken mai da kayan miya, su kaɗai suka ci abinsu don ko ni sai indomie na dafa.
Miƙewa yay bayan yaja tsaki ya fice a ɗakin, nayi guntuwar dariya ina rufe murfin. Sai kusan minti biyar ya dawo da ƙatuwar leda hannunsa, Biredi ne ya fita ya siyo babu shiri, in banda haka sai da sassafe yake aikawa gidan biredi a siyo sabon yi me zafi, ina kallonsa ya buɗe friedge ya ɗauko lemu.
Kallona yay nayi saurin É—auke ido don na san saboda yaji babu sanyi ne, kamar ba zai magana ba sai kuma ce min yay,"Me ya samu firij É—in?". Ya faÉ—a yana duba socket.
Ni kuwa ina sane na kashe yau da safe, ai na rantse sai na guma masa a kwanaki biyun nan da zai yi, abinci sai dai ya siyo na waje amma na bar yi masa girki ko yaje can ya karɓo a wajenta. Duk da naga kamar bai jin daɗin girkinta, don ranar nan tana min baƙaƙen maganganu wai idan ma asiri nayi akan ya daina jin daɗin girkinta to nayi kaɗan na rabata da shi. Ni dai ban kulata ba don nafi ga na bawa banza ajiyarta, wayewartata da ake ta faɗa a banza a iska tunda har tana iya faɗa da kishiya, a wannan zamanin wa ke wannan shirmen? Bokon nata ma ai na banza da wofi ne.
Shi kuma sai ya tsiri cewa irin girkin ranar kaza zan yi, don kam dai Alhamdulillah naji daÉ—in koyon girkin Leemars Mandi, kuma koyon yay min rana sosai.
Waya naji yana yi yana cewa da me gadi ya siyo masa leku me sanyi, shi kuma yace masa ai masu shaguna duk sun rufe yanzu.
Haka nan bai iya shan lemun ba don ba ya iya shan abu mara sanyi. Naga ya buÉ—e wadrobe ya É—auko jakar takardunsa ya zo ya bajesu yana dube dube, nan dai na barsa har na kwanta ma. Sai can cikin barcina naji ya tashe ni, ina farkawa na dube shi da tausayin yanayin fuskarsa na ce,"lafiya?".
Yay ɗan jim kafin yace,"Ko za ki taimaka ki soya min wainar ƙwai don Allah".
Agogo na kalla naga ƙarfe uku da rabi, sai naji ya ban tausayi don duk me imani dai ya san illar yunwa balle shi da ba ya jure mata. Na sauka na fita naje babu daɗewa na dawo da soyayyar wainar ƙwai ƙatuwa har da ɗauko masa lemu me sanyi a ɗakina. Amma saboda mutumin nan baida imani babu Allah a ransa ashe Zahra'u ce ta kirasa a lokacin wai tana son cin wainar ƙwai, ina kallo ya ɗauka ya fita cikin rawar jiki da sassarfa, ji nayi kamar na tashi na iske shi na kifar da wainar ayi duk bala'in da za'ai, amma sai ɗayan ɓarin zuciyata ya hane ni da cewa,"Kauda kai lokaci ne".
Haka nan na kwanta riƙe da gefen zuciyata ina hana kaina kukan da ke son ƙwace min. Ban san san da ɓarawon bacci ya ɗauke ni ba kuma.
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR10FT5*
Tsawon kwanaki muna ta fama da jikin Abbaa, Asibitin Aminu Kano suka bamu gado da taimakon Baba Tijjani da wani mutum da ke siyan kaya wurin Abbaa aka samu na biyan gado da sauran abubuwan da likitoci suka nema.
Abinci kuwa na kullum Ummansu Hindatu ita ke dafowa ana kawo mana na safe, Maman Yasmin tayi na rana, Anty Khairi tayo na dare, ni da Ummani da Abbayo mu ke kwana a asibitin, ba kullum muke zuwa gida ba saboda yanayin kuÉ—in mota. Idan ba Yaya Imam ko Yashaik ba ne suke da kuÉ—i a hannu sosai shine zasu ce muje muyi wanka sai mu dawo.
Ba Abbaa kaɗai da yake ciwon ba hatta mu da muke jinyarsa duk mun rame mun fita a hayyacinmu, don abun biyu ya haɗe mana, shima Kaka jikinsa ya tsananta sosai duk da shi nasa ciwo na tsufa ne. Su Yaya Imam na ta in koma gida abun zai zama da hauka har kwana shida, gwara in ke zuwa ko bayan kwana ɗaya ne, Babanmu ya ce ai tun da mijin ya barni su ƙyale ni, cacar kuɗin mota ma aiki ne. Sannan idan ina gida zan fi damuwa har wani ciwon yazo ya iya kamani. Ba su san ma ni rashin dama ce dama tasa na ke zaune acan ɗin ba, a hakan dai da hankali ba a kwance yake ba nafi jin daɗin zaman akan na koma wancan kurkukun.
Ni dai ban iya cewa da su komai, don na san idan suka yanke magana akaina ko Ummani ba ta iya cewa ba haka ba. Nazifi ya zo sau biyu ya duba Abbaa da jiki, haka wani sa'in da daddare zai kira ya tambaye ni ya me jiki yana magana kamar na tursasa shi. Uhmm sai yanzu ai na ƙara yarda da ake cewa idan iyayenki basu da kuɗi miji ba ya musu kallon daraja musamman in ace shi bana arziƙi ba ne, ga dai shi na gani kan Nazifi yana ganin bamu da komai, wanda kamata yay ace ko bai zo kullum ba ya ke kirana kullum yaji yanda jikin mahaifin nawa yake, haka ma ya taimaka mana da ko na magani ne tun da ai yasan halin da muke ciki, amma duk ba ɗaya tun zuwan dai da yay a gida ya bada dubu goma ɗin nan bai ƙara zuwa ma ko da ruwa ba yace ga shi. Ranar ƙarshe da ya zo yana faɗa min itama Zahra'un sun koma gida wai haihuwar ba yanzu ba sai nan da sati ɗaya, idan bata haihu da kanta ba zasu yi mata aiki.
Iyam ma naji ta dawo amma bata ko kira ni balle zuwa dubiya, gidansu Nazifin ma dai kaf babu wanda yazo min sai jiya ne Lubabatu da Yayan Shago da Amarya suka zo, naji daÉ—in zuwan na su sosai da kayan dubiyarsu da zasu tafi har dubu biyu Yayan Shago ya bawa Ummani. Da muka yi waya da Safiyya Babansu ya haÉ—amu da wani babban likita a asibitin, ita ma Ummar tasu ta turawa Ummani dubu biyar tace basa Nigeria da sun zo dubiya.