← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 113

Sashe 33

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan dukan ba komai na yi miki ba, ki jira yi dawowata, ba aai burinki raba ni da farin ciki ba, to Sa'ida daga ranar yau na dinƙa dukanki kenan a cikin gidan nan har mutuwarki, sakin ki ba zan yi ba, ba zan taɓa sakin ki ba, yanda kika ƙuntata min kika kashe min yarinya wallahi nima sai na kashe ki da irin salon wuyar da zan dinga gana miki a cikin gidan nan daga ranar yau, za ki ƙwammaci ba ki taɓa sanina ba a rayuwarki".

"Wayyooooo". Na kurma wata gigitacciyar ƙara ina saurin miƙewa daga kan katifar da na ke kwance. Ƙirjina bugawa yake yana dukan uku uku, zufa kuwa tuni ta wanke min jiki, jiki na rawa nayi ƙofa ina girgiza kaina.
Sai ga Ummani da saurinta tana tambayata,"Ke lafiyarki".

Numfashi kawai na ke saukewa kamar wadda ta sheƙa mugun gudu, na faɗa jikinta ina faɗin,"Ba zan koma ba Ummani, don Allah ku ƙyale ni ba zan koma ba, wallahi na koma kashe ni za su yi".

Bayana take shafawa tana faÉ—in,"Ke me kike faÉ—i ne haka? Ko mafarki kika yi ne?".

Shiru nayi ina haɗiye yawu a busashshen maƙogorona, a hankali na ke sauke ajiyar zuciya, na janye a jikinta sannan na bi ɗakina da kallo, kafin na ɗaga labule ina kallon tsakar gidanmu. Sai kuma na fara tunanin ashe fa daga kotu gida muka yo ba gidan Nazifi na koma ba, na hasko lokacin da muka fito daga cikin kotun Kaka yake maganar to ya za'ai da ni, Abbaa yay saurin cewa da shi ai gida zamu wuce da ita.

Kuma muna dawowa gidan Ummani ta ɗora min ruwan zafi nayi wanka, ta bani abinci da kanta na ci na ƙoshi, ta mulke min jikina da maganin ciwon jiki, Abbaa ya fita chemist ya siyo maganin ciwon jiki ya ɓallo ya bani na sha, da kansa yace na shiga ɗaki na kwanta nayi bacci sosai, a lokacin kallonsu kawai na ke tayi a raina ina ayyana ko me ke zuciyoyinsu? Shin abin da ke raina shi yake ransu na game da zaman gidan Nazifi? Ko kuwa akasin hakan ne?

Sai da Ummani ta zungureni ta kama min faɗan bata son ina nisan tunani irin haka, kafin nan na miƙe na shigo ɗaki na kwanta, ina kwanciyar sai bacci, baccin da ya haddasa min mummunan mafarkin ina maimaita rayuwa a cikin gidan Nazifi.
Numfashi na ja na sauke na ce da Ummani,"Mafarki nayi ne".

"To mafarki da zaka yi adu'a sai ka ƙwala ihu haka, kin ji yanda ƙararki ta bani tsoro kuwa. Kai haba Sa'ida ban san ki da haka ba, To me kika gani a mafarkin?".

Ido na ɗaga ina kallonta sai nayi ƙasa da kaina ban ce komai ba.
"Ko ganinki kika yi a can bursun ɗin? To ya kamata ki cire tunanin hakan a ranki, Allah ba zai kuma kawo miki ƙaddarar hakan ba, ki yi ƙoƙarin mantawa ma gaba ɗaya tun da dai har Allah ya fidda ke, Ko kuwa me kika gani dama?".

Na girgiza kai ban ce komai ba. "A'a fa baki za ki buÉ—e ki min bayani".

"Ummani a gidan Nazifi na ganni, wai na koma can".
"A'a to kuma shi ne sai aka yi me? Mene da can É—in?".

Ba shiri na ware idanuna akanta ina cewa,"Ummani sai na soma komawa to?".

"Banda ta cewa sai abin da Kakanki da Abbaanku suka yanke. Amma dai ki zama cikin shiri kin san duk dare suna iya cewa ki tafi. Mafarki kuma daga yau kar ki ƙara ihu irin haka adu'oi ne iri daban daban akanki kin san su, irin haka ba sai ki janyowa kanki matsala ba idan ma wani sharrin ake nufarki da shi ya sameki".

Tana gama faÉ—in hakan ta fita ta barni. Ai a wurin na silale na zauna ina hawaye, wai komin dare zan koma gidan Nazifi?
Ba ni na miƙe ba sai da aka yi kiran magriba tukunna naji muryan Ummani na faɗin,"Ki fito kiyi alwala ga ruwan ɗumi nan na zuba miki kar ya huce".

Tashi nayi cikin mutuwar jiki na fita, ina alwala ina lissafi, matsawar aka ce na koma gidan Nazifi to wallahi sai dai ko na tsaya a titi mota ta bige ni, ko kuma nayi tafiyata ƙauye, ai ni da Nazifi kuma har abada, mun gama zama da shi haka kuma na gama ganinsa, ko a lahira bana fatan ƙara ganin ko da inuwarsa, a yanzu haka na san ba zai taɓa waiwayata da sunan cewa na koma gidansa ba, to nima haka ba zai taɓa jin motsina ba, idan naga take taken su Abbaa na in koma ne to zan nemi wani wajan, shi kuma duk sanda ya gaji ya aiko min takarda ta.

Muna zaune ne tsakar gida muna cin abinci Abbaa ya dawo, muka yi masa sannu da zuwa ya zauna. Walida ta taho da gudunta ta faÉ—a jikinsa tana faÉ—in,"Abbaa sannu da dawowa, an dawo lafiya?".

"Na dawo lafiya lau ƴar albarka, me kika ci haka duk kika ɓata bakin ki?".

Kunnensa ta kama ta raɗa masa magana, Sai kuma ta ɗora yatsa a leɓenta tana cewa,"Amma fa kar kayi magana ta ji".

Dariya nayi Abbaa ma yay dariya. Ummani ta fito daga kitchen tana cewa,"Babanki zai shigo gidan ne ai biyana kayana zai yi. Yarinyar nema kike ki ɓalla min jari ta ƙarfi da yaji".

"To ai Abbaa yace shi ya ba ki jarin".
Ta faɗa tana ƙara maƙalewa jikin Abbaa. Shi kuma yana tayata Ummani dai na mita akan shanye mata alawar yaran da take siyarwa, ta sauya wajen ajiya yafi sau nawa amma sai Walida ta bi ta ɗauko. Bayan gama cin abincin Abbaa ya dube ni yace,"Ke ya jikin na ki?".

Fitar amon muryarsa kamar na me fushi da ni hakan yasa na ɗaga ido na ɗan dube shi kafin na ce,"Da sauƙi Abbaa".

"Babu wani waje da kike jin ciwo?".

"Ehh Abbaa". Na faɗa kawai amma ba wai don hakan ba ne, a zahiri cikin ƙashina ciwo na ke ji sosai.

Muna nan dai zaune ita jiran naji Abbaa yay min maganar Nazifi ko maganar tafiya amma naji shiru bai yi ba. sai na ɗan fara jin tsoro don ban san ko yana so ya gwada hankalin yakamata na ba ne. Ummani ma da muke tare muna magana jefi jefi saboda shirin da take ji a radiyo itama ban ji tayi min wani zance ba. Da Kaka ya kira ni kuwa ba ƙaramin kaɗawa ƴaƴan hanjina suka yi ba, na yi hanzarin miƙewa ƙafafu a sanyaye nayi ɗakinsa, ya gama cin abinci lokacin na raɓe daga can gefe ina ce masa gani.

"Ya jikin ki É—in". Ya tambaya ba tare da ya dubi in da na ke ba.
"Da sauƙi". Na faɗa a hankali.

"Allah ya sauƙe, an siyo miki magungunan?".
"Ehh Abaa ya kawo min tun da rana".
"To shikenan tashi kije. Ko akwai wata matsala?".
"A'a babu Kaka".
"To Allah yay albarka".
"Amin Kaka sai da safe, Allah ya ƙara lafiya". Na faɗa ina tashi na fita.

Da Abbaa ya dawo ya shigo ɗakin Ummani, ina kwance kan gadonta na miƙe ina masa sannu da dawowa, ya amsa yana cewa,"Ungo maganin sauro, ko an samu net ɗin?".

"Ehh an samu amma ya ɓuɓɓule Anty Khairi tace zata aiko a kawo wani to ban sani ba ko sai zuwa anjima idan Yaya Imam zai shigo".

"Imam ai ba zai zo ba ƙarfe tara yanzu, saka maganin dai ɗayan ai zai isa har gari ya waye ko?".

"Ehh Abba, an gode".

Na karɓa ina miƙewa na fita na basu wuri duk da Ummanin sallah take. Ɗakina nayi na kaɗo sauro waje, na manta ma ɗazu da suka kawo wuta na bawa Hindatu wayata ta saka min caji, ko da yake ban gama dawowa hayyacina ba balle hankalin ya kai ga wata waya, sai yanzu da daren yay kuma na ke tunanin haske ga basa kawo wuta cikin dare.
Ummani ce ta miƙo min ashana da ƴar ƙaramar toci, muka yi sallamar sai da safe kafin nan na rufe ƙofa na kwanta.

Washe gari da safe duk yanda na so na taya Ummani aiki ta hana ni, sai ce tayi tun da naci abinci na dai yi wanka na kwanta ba cikakkar lafiya garen ba. Sai bayan ta gama aikinta tas sannan ta zo ta zauna, ina ta jera mata sannu ina cewa ban ji daÉ—i da bata barni nayi aikin ba.

Abbayo yana zaune a ɗakin yake maimaitawa Ummani irin wulaƙancin da suke sha idan suka je ganina a bursun, iya ƴan kwanaki bakwan da nayi a ciki wulaƙancin da suka sha yafi miliyan, yace sau tari sai sun taho sai yaga Abbaa yana share ƙwalla.
Ni dai duk abinda yake faɗa ina jinsu, wani na yi yaƙe wani kuma na buɗe haƙora kamar mai yin dariya amma a zahiri ban san ina yi ba, kawai dai na san ko da yafiyata ce kawai zata ragewa Nazifi ya shiga aljanna bana jin zan yafe masa, a silarsa naga hawayen mahaifina, a silarsa naga hawayen mahaifiyata, a silarsa ya hana kowa nawa kwanciyat hankali.
Kaɗan kaɗan na ke jin ciwo haka, sai na ɗora hannu a kan ƙirjina saboda yadda naji kamar zuciyata zata faɗo ƙasa.

Ummani ta lura da ni tayi saurin tasowa tana cewa da Abbayo,"Buɗe sif ɗin can ka miƙo magungunta, da yake ba sanin ciwon kanta tayi ba bata sha ba ni kuma ina ta zuci zucin nayi mata magana".

"Ta ma ci abinci ne?".
"Eii taci, ai sai da Abbaanku ya sata gaba ta sha shayin da aka kawo daga gidan Yashaik tukunna ya fita, ka santa da gardamar cin abinci".

Sai bayan ya miƙo mata maganin tukunna ta dubi fuskar Sa'ida taga idanunta a rufe.
"Au bacci kika yi saboda kar ki sha maganin, to tashi".

Kaka da ke isowa ƙofar ɗakin ya ɗaga labule, yake tambayar Ummani jikin Sa'idan yaga bata leƙa wajensa ba, tace,"Da sauƙi jikin nata yanzu ne ma naga tana ɗan dafe ƙirjin, maganin zata sha kuma sai bacci ya ɗauketa".
Chapter 33 · 0% Book details