← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 113

Sashe 91

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka baro gidanmu muka shiga nan maƙotanmu gidan wata Umman Habu, nan muka yi zaman mu da mutanena, don ko gidan Maman Yasmin ma ba wajen zama, gidanmu cike itama gidanta a cike, Hassana Tijjani ta kwaso duk abubuwan buƙatana daga gidan Maman Yasmin ɗin ta kawon nan, Safiyya kuma ta tafi ɗakko me min kwalliya duk da nace mata ni bana so, abun da ba dinner ko party ba tace wallahi sai anyi.
Ƙarfe sha ɗaya na ranar lahadi, cikin watan ƙarshe na shekarar dubu biyu da ashirin da uku, dubban mutane suka Shaida ɗaurin auran Lieutenant Salim Sadiq Oluwa da Amaryarsa RN Sa'ida Salman Madobi akan sadaki dubu ɗari biyu lakadan. Masha Allahu ɗaurin auren ya tara dubban mutane, don gaba ɗaya kan titin layin kashe shi aka yi sai zagaye aka koma yi, duk wanda ya zo kuwa sai ya tambayi ɗaurin auren wa ake yi haka. Abbaa har sai da yayi mamakin irin jama'ar da wasu ma zai ce bai san daga ina ba, taro kamar da aljanu, kowa kuma ya zo sai ya miƙo masa hannu an gaisa, tawagar mahaifin Salim kuwa ba zai iya cewa ga adadin su ba, motar sojoji kamar tayi magana jiniya kawai kake ji na tashi a faɗin unguwar.

Ni dai tunda aka shigo ana ce min an ɗaura aure naji jikina ya mutu, ban san sanda hawaye ya sakko min ba. An gama min kwalliya a sa'ilin sai ga kiran Salim wanda rabona da shi tun shekaran jiya, sai sannan hankalina ya kwanta da naji muryarsa, duk da fushi na ke tayi da shi, fushin nawa ya gushe dalilin jinsa da nayi cikin farin ciki mara misaltuwa, tunda na ke da shi ban taɓa jinsa a irin yanayin murna da annushuwa ba irin haka, yana ta ce min nima in godewa Allah da ya nuna mana wannan rana. Yace ga shi ya yakice da ƙyar ya shiga mota in kunna data muyi vedio call ya ganni, nima ɗin kuma son ganinsa na ke nace ya kira a ta Safiyya nawa babu data.

Wani kallo da ya kafe ni da shi ta cikin vedio call ɗin kamar zai fizgo ni, yana ta faɗin nayi kyau ina ma yanzu zai tafi da ni, shi duk ya ƙosa akai masa ni, na ce bayan kana bakin aiki, yace ai sai mu kwana a otel ɗin da suke, na ce a'a ni na fi so mu raya darenmu a cikin gidanmu kan gadonmu na sunnah ba na otel ba. Shima ina ta faɗa masa yayi kyau sosai a babban rigan da yasa, ya cire hulan yana nuna min askin su na sojaji da bana sonsa, ba ranar da bana ƙorafi akai, yace ya so yayi irin wanda na ke so to ba yanda zai yi da Emeka ne. mutane anata kiransa, Sir ma yana nemansa za'ai hotuna, da abokansa haka dole ya yanke kiran, bayan ya sanar min cewa ya bawa Khalid Yayan Safiyya Ticket ɗinmu, can garinsu za'a fara kai ni Anambra wajen iyayensa, zan kwana acan washe gari akwai igbo day da Kakarsa ta haɗa za'a yi, da daddare kuma sai a wuce da ni can Delta gidana, abokansa kuma sun haɗa masa dinner na sojoji da za'ayi ranar da aka kai ni.

Cikin gidanmu kuwa sai guɗa ake yi anata taya ni murna, na so ace Salim ya samu shigowa an mana hoto tare da mahaifana to sai bai samu dama ba suna ta sauri za su koma can Abuja fadar shugaban ƙasa. Taron da aka yi a gidanmu sai wanda ya gani, Alhamdulillahi taro yayi masha Allah, ni kaina na fi farin ciki a wannan ranar sama da wancan lokacin, kowa ya shigo adu'a da fatan alkhairi yake min, abinci kuwa shiga da fita da shi kawai ake yi, ba wanda zai ce bai ci ya ƙoshi ba.

Bayan dawowar Æ´an É—aurin aure Abbaa yace na shirya nan da awa guda za'a zo a tafi da ni, yace da Ummani kuma a samu mutum biyar da zamu tafi tare da su. Yaya Al'amin ya shigo yake cewa Salim É—in ya kira shi idan da kayan da za'a tafi da su akwai mota da zata tafi can garin na su yanzu. Aka shiga aka fito da akwatunan lefe na da kayayyakina dukka wadanda zan tafi da su, sai kayan gudunmawa da aka bar bani da na wajen Ummani dukka aka haÉ—a aka tafi da su, kayan gara kuma Ummani tace a bari sai zamu tafi sai a tafi da su.

Ƙarfe Ɗaya na gama shiryawa cikin wani swizz less maroon colour me tsadar gaske, ga shi Habibu yay min ɗinki na garari, Anty Saim ta ɗaura min lafaya milk colour akai, aka fito da ni daga gidan Maman Yasmin zuwa gidanmu, ƙamshi ne kawai ke tashi duk ta inda na gimla, muna shiga muka wuce ɗakin Abbaa ni da Safiyya, yana zaune bisa dardumar sallah a sa'ilin, da rediyonsa a kunne sabuwa wadda na siya masa babu jimawa, na zauna gabansa Safiyya ma na zaune a kusa da ni, muka gaida shi lokacin itama Ummani ke shigowa.

Yanda na ke jina tamkar yau ne karon farko da nayi aure a rayuwata, musamman jin irin nasihar da Abbaa ya shiga yi min kamar a auren farko. Duk yanda naso riƙe kukana kasa riƙe shi nayi, hawaye kamar an kunna fanfo sai sauka yake a kuncina, gaba ɗaya yanayina ya canja jikina yayi sanyi kamar sabuwar amaryar da bata taɓa zuwa gidan miji ba.
Ummani ta amshe maganar Abbaa tana kallona tace,"Nasan duk kinji abinda mahaifinki ya faɗa, mun amince da hankalinki da nutsuwarki, auren farko ma da kike da ƙarancin shekaru da wayo da kuma ƙarancin ilimi kinyi ƙoƙari wajan riƙe sirrin ki da na mijinki duk da wahalar da kika sha, balle kuma yanzu da kika daɗa hankali, kika ƙara gogewa da ilimi da sanin rayuwa, To ba ma yi miki fatan sake maimaita kwatankwacin abinda ya gabata Sa'ida, amma kamar yanda kika sa ni dole sai an saɓa yau da gobe ta gaji haka, ita zamantakewa haka take, ba sai a aure kawai ba duk da wanda zaka zauna yau da gobe wataran sai an saɓa. Abokiyar zamanki kuma dan girman Allah Sa'ida ki zauna da ita da zuciya ɗaya, kar ki zama cikin matan da burinsu in sun shiga gidan mai mata su kori wacce suka je suka tarar ko su muzguna mata, mijinta kika aura in ma kishin ne ita zata fiki jinsa domin tana zaman zamanta ita da ƴaƴanta kika shiga rayuwarsu. Dan Allah Sa'ida ki riƙe ta kamar ƴar uwarki, kinga mun samu labarin halayenta na gari dan Allah karki lalata tarbiyar da muka yi miki wajan ganin kin ɓata zamanku".

Ni dai hawaye nake a hankali wani iri nake ji a jikina, wai yau ni ce nayi aure a karo na biyu wanda ban taɓa hasaso hakan a rayuwata ba, kullum tunanina Nazifi shi ne mijina na farko kuma na ƙarshe har na bar duniya ina tare da shi, ko da na rabu da shi kuwa ban taɓa tsammanin zan sauka akan bakana na cewa ba zan ƙara yin aure ba, ashe ba haka Allah ya tsarawa rayuwar tawa ba.

Abbaa ya numfasa kafin ya daɗa cewa,"Ko bayan raina Sa'ida kar ki watsi ki sauka daga kan nasiharmu gare ki, ruƙo da ita shi zai sa kiji daɗin rayuwarki a duk inda kika tsinci kan ki, a wannan karan ba zan ta maimaita miki kalmar haƙuri don kije kiyi ta cutar kanki ba, ba fata na ke ba kuma bana so ranar da zata zo ki kawo ƙorafin mijinki, amma kar kiyi zurfin cikin da za ki zauna ana cutar da ke, kina da mu kina da ƴan uwanki, ki kira mu duk lokacin da kike da wata matsala, wataran zamu zo ni da mahaifiyarki insha Allahu. Ku tashi kuje mota tana jiran ku, Allah ya bada zaman lafiya, yasa kin shiga kenan sai mutuwa ce zata raba ku, idan akwai rabo ina roƙon Allah ya ba ki zuriyya ɗayyiba, Allah yay muku albarka gaba ɗayanku".

Safiyya ta miƙe, ta kamo ni na tashi da ƙyar saboda yacca ƙafafuna suka yi bala'in sanyi, Ummani ta miƙe na faɗa jikinta, tana shafa bayana take lallashina, ita ta kama hannuna muka fita, ina jin Abbaa na tambayar Safiyya tare zamu tafi tace masa ehh sai ta kai ni har gidana ma, Abbaa yay aduan Allah ya bar mana zumuncinmu ya ƙara haɗa kawunanmu.

Ummani ta kai ni ɗakin Kaka, shima yay min nasa nasihan, Baba Tijjani da Baba Sabi'u dama su tun dawowa daga ɗaurin aure suka kira ni suka min nasu nasiha da faɗan. Yayyuna ma haka duk mun yi sallama da su tun dawowan ɗaurin aure. Ba'a yi wasu motoci da yawa ba, duk da Salim ɗin yace babu matsala ko mutum nawa suke son zuwa za'a tafi da su, tunda ba motan haya ba ne motoci ne na gida kuma duk za'a dawo da su, ni ba da shi ma muka yi maganan ba da Yashaik suka yi, Abbaa dai ya hana yace da mutum biyar za'a tafi, Hajjo, Umman su Batula, Mama A'i, Mama ta kurna, sai Anty Ziyada, sai da ƙyar Ummani ta lallame shi ya yarda za'a tafi da Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Bibalo da Juwairiyya wa'anda duk suke sa'anni na ne.
Chapter 91 · 0% Book details