← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 113

Sashe 13

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iyam ta dube shi tana faɗin,"Kaga ɗauko maƙullin mota mu wuce asibiti kawai, ai bamu ga ta zama ba, shi dama ciki in ya shiga wata bakwai ai ana iya haifarsa. Bamu san ko Allah ne ya kawo haihuwar yanzu ba. wannan susutacciyar matar taka ma kaɗai ta isa tasa a haihu babu shiri. Ban da rashin imani ma na juya ana zancen ciwo kina ke ina ruwanki, da ike bata san zafin ɗaukar cikin da rainonsa ba. Allah ne ma ya san manufar jaki da bai ba shi ƙaho ba, Allah ya baka matar da zata cika maka gida da iyali tana baƙin ciki da hassada saboda ita bata haihuwar wata ba zata haihu ba, to aniyarki ta koma miki duk baƙin cikinki sai naga jikina jinin Shalele".

A wannan furucin na Iyam kam tuni idanuna suka ƙara tara ruwan hawayen baƙin ciki, wani rauni ya baibaye ni, raina ya kai ƙololuwar ɓaci har na kasa haƙuri sai da na tanka.
"Ni ba na baƙin ciki da abin da Allah ne ke bawa bawansa, cutar hassada kuma ban ɗorawa kaina ba don Allah kar ki ƙara alaƙanta ni da ita. Kuma idan hakan da kuke ke da ɗanki kuna ganin daidai ne kuci gaba da zaluntata, Allah yana ji yana gani zai saka min".

Tass naji saukar mari a fuskata, na dafe wurin cikin jin raɗaɗin zafin, Nazifi na nuna ni da yatsa ya ce,"Idan mahaifiyata na magana kina yi sai na yi fatali da ke, ƙarya aka yi akan ki ke ba juyar ba ce, idan kin ji haushi ki ɗauki cikin mana ki haife kiga idan ba'a so ki ba, karo na uku da zan ƙara faɗa miki wallahi da na san ba ki haihuwa Sa'ida ba zan taɓa aurenki ba, juyar banza da wofi kawai".

Ƙurii na masa da ido ina kallonsa, da yanda yake maganganunsa cikin kwanciyar hankali, a duk kalaman da yake faɗa min a baya ba su ƙona min rai ba kamar yanda wannan yay min ba, a maimakon zubar hawaye sai na tsinci murmushin da ban shirya masa ba a fuskata, ban ƙara cewa komai ba na juya na koma ɗaki, da shigowar tawa shima ya shigo ya saka jallabiyarsa tare da ɗaukar maƙullan mota ya fita.

Yana fita na saki marayan kukan da nayi dauriyar riƙewa, jikina rawa kawai yake yi, Allah ya sani yau na ƙara jin na daɗa gajiya da zaman auren Nazifi, tabbas aka ci gaba da tafiya a haka zaciyata zata iya bugawa, wanda a yanzu haka yanda na ke jin jinina yay zafi kamar zan shiɗe haka na ke jina.
Wallahi ban da mahaifina ban ga abin da zai hanani tattarawa na bar gidan Nazifi ba a gobe da safe, kuma bari na har abada, ai ban haifa ba balle na tafi da tunani da damuwar barin Æ´aÆ´ana, aure ne dama yama fita gaba É—aya akaina ba iyaka aurensa ba kawai.

Tun daga wannan ranar lamari ya ƙara sauyawa, hankalin Nazifi ya tattara gaba ɗaya ya koma kan Zahra'u da abin da ke cikinta, wai ai likita ya ce tana da buƙatar a kula da ita sosai, don haka ko fita yay bini bini ya dawo, haka idan muna tare bini bini ya tashi ya tafi wajenta ya dubata, kuma da ke muguwa ce ta ƙarshe sai ta koma cewa ita abincina kawai take iya ci ta zauna lafiya, don haka dole na koma girkawa ina bata tana ci, idan naƙi girki kuwa ta dinƙi ciwon ƙarya kuma duk abin da aka bata taci sai tayi amansa, sai taci nawa ne kawai take zama lafiya, a hakan ma duk bai mata ba sai abun da take so na ke dafawa, idan ma na ce zan yi son raina to fa idan raina yayi dubu sai ya ɓaci. Nazifi har da min kashedin kar hakan ya bani lasisin zuba wani abu a abinci da zai cutar masa da mata da yaro, in bar ganin matarsa ce ni yin shari'a da ni abu ne me sauƙi a wurinsa.

Kusan kullum ba ni da aiki sai kiran mahaifiyata ina shaida mata abubuwan da ke faruwa, nayi ta mata kuka ina shaida mata na gaji, banda burin da ya wuce na ganni kusa da ita a ƙalla ko da a kafaɗarta ne na zubar da hawanyen kuma nayi hira da ita naji sanyi, haka zata lallashe ni ta turo min su Hindatu da Ƴaƴan wurin Yashaik su ɗebe min kewa, ita kuma ko da yaushe sai dai tayi ta ƙara jaddada min muhimmancin haƙuri, juriya da ƙara dagewa akan adu'a.
Ga shi har yanzu ban ƙara zuwa gida ba tun wannan case ɗin da akai na su Atika, don ko da Kaka yasha jinya Abbaa ce yay na zo masa gida bai yafe ba. To daɗin ma da nake ta ji dai wata guda ya rage a cika shekara. Amma tabbas ina da buƙatar duk san da na shiga damuwa irin haka naje gidanmu wurin mahaifiyata, don ma dai Allah yasa yanzu makarantar koyon turanci ta online da na shiga karatunta duk ke ɗebe min kewa, haka kuma zan ta ganin Safiyya na live vedio a IG akan harkar lafiya wannan ma duk sai yake sawa ina jin daɗi.

Kar ku so kuga irin kuɗin da Nazifi ke kashewa wajen siyayyar kayan jariri, duk wasu kayan haihuwa ya siya ɗakinsa yay maƙil da akwatuna kamar me haɗa lefe, ko zama muka yi sai ya kama tambayata me zai ƙara siya, ba ɗakinsa kawai ba ita kanta can ɗakinta ya cikata da kaya nata da na jariri, Haka ba dama suyi waya da wani cikin mutanensa da yaji mutum yace bai ƙasar zai ce a taho masa da kayan jarirai masu tsada, gidan kuwa har yasa ana gyaransa wasu wuraren ana sabunta su.
Ana haka Iyam tayi tafiya ƙauye, tana tafiya kuwa na samu damar sararawa, don kwanciya nayi ciwon ƙarya ko motsawa ban yi, ni kam na gaji da bautawa matarsa na ciyar da ita da kula da ita, saboda haka gidanmu nima aka turo min Saudatu ƴar wurin Baba Tijjani wacca da ƙyar uwarta ta barta, itama kuma Zahra'un sai ga shi an turo mata ƙannenta har biyu da wata tsohuwa.

Ƙaton cikin Zahra'u a gaba ya fito turtsetse haihuwa yau ko gobe, a kitchen take tana kaiwa da kacaniya da tukunya, kunnenta sanye da earpod tana magana da alama waya take yi. Ƙanwarta Mubina da ke can gefe tana yanka salad ta dube ta tana faɗin,"Yaya shi kawai za'a yanka?".

Kai ta É—aga mata alamar ehh kana a hankali tace mata,"Je ki sanya turare a É—akin Honey, kuma ki haÉ—a salad É—in kisa a friedge É—in É—akina".

Mubina ta fita ita kuma taci gaba da maganar da take yi. "Ki bari ke dai wani abun ma sai Unborn ya sauka anan zan ƙara ƙwace shi ya zama nawa ni ɗaya".

Sai kuma tayi dariya sosai kafin ta ce,"Kai ƙawata! To ai na faɗa miki nima sai da na gama shishshigewa jikinta na gane sakarya ce sanyinta yay yawa kana na ce to bari in karkata in san yanda nayi na dawo da shi tafin hannuna gaba ɗaya. Kin san ina faɗa miki yarinya ce gaba ɗaya bata da wayewa, da ke ma naga yanzu ta fara baki in anyi tana iya mayarwa, amma tana abu komai irin na ƴan da, kuma like tayi rayuwan ƙauye ne i think so, kin san wani abu ma? Idan fa muna gado sumbatun da yake min haka za kiji yana ta faɗin shi a wajena kawai yake jin daɗi, can ba'a masa komai, bata iya salon komai ba salam takee".

Ta ƙara yin dariya bayan gajeran shirun da tayi tace,"A'a ni ba zan koreta daga gidan ba, ai so nake ta zauna tayi min rainon yara ni kuma naji da aikina. Kin san tana da addini da kuma tarbiyya dan ba ki ga yaran da suke wajenmu ba yanda ɗayar ke da karatun ƙur'ani a baki da ibada".

"Hhhh Allah ko ƙawata to ya kamata dai ki dawo ɗin gaskiya don kam dai ɗanku ya kusa fitowa, a yanzu haka ji na ke kamar zan haihu ƙarfi hali kawai na ke. Kin san na gama wancan wasan na ƙyaleta ta huta kar ɓakin cikina ya kasheta a rubuta min zunubi, amma dai kam har yanzu bana barinta runtsawa idan ya koma wajenta".

Nazifi ya shigo kitchen ɗin a lokacin, daga bakin ƙofa ya tsaya tare da harɗe hannayensa yana ta kallonta, jinta yake har can ƙuryar zuciyarsa, yana mata wani irin so ne da shi kansa bai sani ba, a duk lokacin da yake tare da ita sai ya ciji yatsar rashin samunta tun da daɗewa, ban da zanen ƙaddara ma da me zai kai shi haɗa layi da auren Sa'ida? Sai dai wani ɓari na zuciyarsa kan faɗa masa cewar ko da a wancan lokacin ya samu Zahra'u ba lallai ta aure shi a irin matsayin da yake ba, don a yanzu wataran yana ganin ɓacin ranta idan ƴan gidansu na masa magana da turanci yana kasa mayarwa, ranar nan har magana ta yaɓa masa ya kuma ji zafin maganar amma haka ya shanye saboda yana mutuwar sonta.

Zahra'u kuwa ƙamshinsa tuni ya sanar da ita zuwansa, don haka a hankali tace da ƙawarta ta kashe wayar, sai taci gaba da aikinta tana ta murmushi kamar bata san yazo ba. tana son Nazifi sosai shiyasa take so ta ƙwace shi gaba ɗaya babu boka babu Malam, kuma bata so ta kori Sa'ida tafi so ta zauna ta zamar mata ƴar aiki. Amma Allah ya gani duk ranar da Nazifi bai wajenta ji take tamkar tayi hauka saboda bala'in kishinsa da take yi.

Da sanyayyan muryata ta kira sunansa cikin salo na jan hankali.

"Derling".
Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Shi kuma ya tako ya iskota yana me rungumeta ta baya tare da ɗora haɓarsa bisa kafaɗunta.

"Derling lafiya dai ka dawo da wuri haka?". Lumshe ido yay yana shaƙar ƙamshin da ke fita daga jikinta yace,"Na kasa samun natsuwar yin komai ne Swty, hankalina duk yana kanki ke da Unborn".
Chapter 13 · 0% Book details