Sashe 3
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da har Abbaa na ya yarda da mu'amalarmu da Yaya Nazifi na san kuwa lallai ya samu lambar yabon shaidawa, ya iya mu'amalantar mutane ga kyautatawa da son taimakawa, haka bai da abokin faÉ—a, shiga shirgin abokai ma bai dameshi ba, indai ba fita neman na kansa ba to yana gida tare da mahaifiyarsa ko kuma yana wajen mahaifinsa É—aukar karatu.
Abbaa da kansa ya yarje min mu'amala da Yaya Nazifi domin yay masa duk wasu jarabawowi sannan kuma ya karance shi sosai, duk da baka ba wa mutum dukkan yardarka kamar yanda ba'a barin ƴa mace sakin jiki da namiji, amma ko da yaushe cikin masiha da ankarar da ni ake. Abbaa har roƙarsa yay da ya ke zuwa gida yana min karatu duk sanda ya samu lokaci, ya damƙa masa amanata domin ya yarda da shi bai da haufi akansa.
Tsakanina da Yaya Nazifi mutunci da girmama juna ne, bama ɓoyewa juna komai, duk wata shawara da ta shafi rayuwarmu da juna mu ke yi, yana matuƙar bani gudunmawa wajen ganin rayuwata ta inganta, bayan mahaifana shine mutum na farko da zan ce yana ɗora ni akan daidaitacciyar hanya, wanda kai tsaye kuma zai faɗa min gaskiya komin ɗacinta, ya kuma tsawatar min da bin hanyar da take ba daidai ba.
Lokaci guda sai ya zamana in har zaka zauna da ni to ba zamu rabu ba sai ka san Yaya Nazifi a bakina, shima ta ɓangarensa duk wanda ya ke tare da shi ya san sunana a bakinsa, haka har ta fara kaiwa ga mutanen da ke kewaye da mu sun fara zargin ko soyayya muke yi, sai dai ko kaɗan babu hakan daga zuciyar kowannemu, ni dai matsayi ɗaya ne a zucciyata Yaya na ɗaukesa kuma aboki, tamkar yanda shima ya ɗauke ni matsayin ƙanwa kuma abokiya, Yaya Nazifi sam ba ya banbanta ni da ƙannensa, ko abun faɗa na yi da gyara zai fito min a matsayin wa na gari yay min faɗa sosai, ina basa girmansa matsayinsa na wanda ya girme min sosai.
Sai dai fa ko kusa an ƙi yarda da cewar babu soyayya a tsakaninmu, tun daga kan ƙawayena har shi kansa ƴan gidansu kan tsokane ni wataran su ce budurwar Yaya Ƙarami ta sirri. Iyam kuwa sau tari idan yana mata hirata sai tace uhmm lokaci dai, Hatta mahaifiyata sai da ta taɓa tambayata anya babu wata alaƙa ta daban tsakaninmu, na tabbatar mata da babu wannan kamar yanda su ke tunani, ta kuma yarda da ni domin ta san bana mata ƙarya bana mata ɓoye ɓoye kuma ta sanya ido akan hakan sosai taga saɓanin zarginta, wasu da basa iya tantance soyayya da mutuntaka ne dai suka kasa gasgata yanda muka ɗauki junanmu.
Lokacin da muka zo term ɗin ƙarshe a SS2 lokacin manema aurena su ka fara fitowa kamar dama jiran lokacin su ke, caaaa wannan ya zo wancan ya zo, daga yamma tayi an fara sintiri kenan a soron gidanmu wai ana sallama da Sa'ida, kuma manyan mutane ba ƙananu ba, duk da ba fita na ke ba idan aka zo amma na kan yi mamakin inda har suka ganni ma suka biyo sawu, haka kuma mafi yawancin masu zuwan sai in tuƙe maƙura a mamakin me suka gani tattare da ni da kamar su masu kuɗi zasu zo neman auren ƴar talaka kamata, yau ace me mota kaza, gobe ace kalar mota kaza, anjima ace wani babban mutum da mota kaza shine babba a wuri kaza, ni ranar da aka ce ma wani ya zo da kaki sai da nayi mugun tsorata ce nake laifi na yi.
Lamarin ya fara bawa Abbaa haushi, da ka ji Abbaa na tsaki to akan hakan ne, har gargaÉ—ina yay akan ya soke min ko zuwa unguwa da Ummani, daga makaranta sai gida.
Shi kam so ya ke ko zai aurar da ni sai nayi nisa a karatun jami'a kamar yanda ya ke fata, don haka duk wanda ya zo da maganar aurena Abbaa zai saita masa hanya da cewar ba yanzu zai aurar da ƴarsa ba domin karatun likita zanyi ba ya so a gurɓata min tunani da soyayya. Ta ɓangaren mahaifiyata ma hakan take don sosai take sanyani gaba da faɗa akan kar na sake in faɗawa tarkon namiji, in tsaya na natsu na tsayar da hankalina wuri guda in yi karatu shine burinsu, kuma shine babban gatan da zasu tafi su barni da shi, wannan ita ce babbar damata in moreta tun da ƙuruciyata kafin girma ya riskeni al'amuran duniya ma su sha kaina.
Na kuma yi masu alƙawarin hakan domin nima banda ra'ayin soyayya ko kaɗan, ko da ina da shi zan ajiye saboda farin cikin iyayena da cikar burinsu, ko son SJ da nayi a baya da ace zuciyata tayi shawara da ni da hakan ba zata soma faruwa ba, to godiyar da na yiwa ubangiji ma har nayi yayin son nasa na gama babu wanda ya sani hatta shi kansa, a yanzu kuma da na ƙara hankali da wayo sai na gane bama sonsa na ke ba burge ni kawai ya ke yi, abin da mutane da dama basa ganewa kenan banbanci tsakanin so da burgewa.
Wata ranar juma'a bayan la'asar muna zaune a tsakar gida ni da Ummani ina tayata tsinkar zogale, muna ta hirarmu ta ƴa da uwa, aka yi sallama daga soro, jin muryar kuma ya saka ni sauke sanyayyen murmushi ina kafe hanyar shigowa da ido, Ummani kuma ta warware ɗaurin ɗan kwalinta ta yafa kafin sannan ta ce,"To shigo mana Nazifi ka tsaya daga nan, gidan ai ba baƙonka ba ne ko".
Har ya sanyo ƙafarsa tsakar gida ban ɗauke idona ba akan hanyar shigowa, shima ɗin shigowar tasa ƙwayar idonsa akaina ta sauka, ya murguɗa min baki da hararar wasa ni kuma sa'adda da na ɗauke kaina zuwa gefe ina murmushi me faɗi don sosai ya bani dariya, yanda mu ke abu da shi kamar ƙawa da ƙawa.
Yau kam yayi kyau sosai cikin farin yadinsa me sauƙin kuɗi, ga shi sai ƙamshi ya ke yi me daɗi, suna gaisawa da Ummani take ce masa.
"Yanzu mu ke maganarka na ce kyan miyar zogalen nan da zan yi ace ka samu kaci. Mutuniyar taka sai ce tayi ai ka daina shan miyar zogale, tuwan ma ka daina ci wai ka zama É—an gayu".
Yana murmushi sosai yace,"Ai Ummani yarinyar nan ƴar adawata ce, buƙulu ne irin nata kawai kuma ko me zata yi sai na ci tunda ba cefanenta ba ne".
Duk sai muka yi dariya ina gaida shi, bai amsa gaisuwar ba yace,"Ke da kike buƙulun na ci tuwo nayi dumurmur kamarki, to alqur'an duk baƙin cikin tanda sai mun ci waina, Yarinya ko za ki bindiga sai nayi ƙibar nan da kike baƙin cikin na yi".
Dariya muka ƙara yi gaba dayanmu ina cewa,"Wallah Yaya kai dai ka min biyayya kawai, don sai abin da na ce da Ummani ka dai sani".
Ummani tace,"Ke asuwa É—an wake a hotel, wacece ke?".
"Autar Ummani mana".
Tace,"Su Autar Ummani manja, to ko da kike Auta ai ba ki samu kwatan son da nake masa ba".
Haƙoransa suka washe yana cewa,"Ahh tou, Auta daban wanda ake so daban, Yarinya ki kumbura ki fashe ni kam nasha gabanki".
Æata fuska nayi ina murguÉ—a baki kaÉ—an kaÉ—an yanda na saba yi masa.
Ummani ta dube shi tace masa,"To ko ƙafa zaka sa ka hankaɗata gefe ta baka wajen zama".
Tashi nayi ina ƴar dariya na ba shi wurin zama akan tabarmar, sai faman dai hararata yake da alama nayi laifin da ban sani ba. Ledar da ya zo da ita ya miƙawa Ummani, haka yake duk lokacin da zai zo sai ya taho mana da wani abun sai in bai da kuɗi kam. haka kuma sai ya zo da alawa duk ranar juma'a ya rabawa yaran gidan da na maƙota, yaran har dakon zuwansa suke ranar juma'a, yanzu ma tuni suka baibaye shi kowa na Yaya Nazifi ba'a bani ba.
Hayaniyarsu duk ta cika ni nayi miƙewar da ban shirya ba, lokacin da na dawo ɗauke da lemu da ruwa har ya sallami yaran, na aje masa farantin a gabansa ina kai hannu cikin tsokana zan ɗauke lemun yay saurin ɗaukewa. Lemun ya fara buɗewa ya sha, daɗin ya ratsa shi har da su rufe ido. Sai da ya sauke yake cewa,"Ummani wai har kin fara lemun?".
Tace,"Au bafa ka zo ba tunda aka fara ko, ai lemu dai in faɗa maka gashi nan yanata jan kasuwa Alhamdulillah, wannan ɗin ma Allah ne yay da rabonka, don dai ta riga ta ɗauko maka ne amma na ƙawata ne a ajiye mata zaka tafi mata da shi".
Suka shiga hirarsu shi da Ummani, nan yake shaida mata ta taya shi murna kuma ta faɗawa Abbaa wani maƙocinsu ya ɗauke shi yaron shago zai ke zama a shagon kullum tun safe har dare, babban shago ne su uku aka saka a ciki amma shine oga don mutumin ya damƙa masa ragamar komai.
Cikin nuna jin daɗi Ummani ta ce,"Amma kuwa naji daɗi Nazifi, kai masha Allah da wannan albishir a ranar juma'a babbar rana, ubangiji yasa hanyar arziƙi ce ya bada sa'a ya shige muku gaba. Wallahi na tayaka murna sosai, Allah kauda fitina da idon maƙiya".