Sashe 28
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayi murmushi kaina a ƙasa, tace min akwai towel a toilet ɗin sabo ta ajiye min, dama da ƙaton hijabi a jikina haka na shiga da shi sai a banɗakin ma na cire kayana. Har na fito still tana zaune bakin gado inda na barta, tayi min nuni da dressing mirror tace ga stool nan na zauna na gyara jikina, ga turaruka nan duakkansu na fesa. Ina shafa man ina ji suna waya da Kudrat tana ce mata tom sai ta ƙaraso.
Ban san me yasa na ke jin zuciyata kamar bata son Kudrat ba, ko duk cikin kishi ne, ko ambatar sunanta aka yi sai naji zuciyata tayi bala'in motsawa da haushi, har mamakin kaina na ke yi, adu'ana É—aya kar wannan kishin yay min illa.
Na shirya cikin kayan da Maa ta bani nayi kyau sosai, lokacin ne take ce min,"Kun samu magana da Onochie?".
Kamar ta san Alla allan da nake kenan tayi maganarsa, na rasa wa zan tambaya shi to, ai kuwa ban san lokacin da na amsa da sauri ba nace"A'a ina ta kiran wayarsa ba ya tafiya tun jiya". Na faÉ—i hakan da muryan damuwa.
Sai bayan nayi maganar ne kuma kunya ta lulluɓe ni, itama murmushi tayi da sautinsa ya fito sosai tace,"Yana lafiya kwantar da hankalin ki, za ki saba ne a hankali". To ni kowa sai yace min in kwantar da hankalina, ta ya kenan alhalin su kansu ba su ji daga gare shi ba.
Muna zaune tana É—an jana da hira wanda duk tambayoyi ne take min game da rayuwana, har tana tambayana mun dai gama magana da Salim akan asibitin da zai nema min ko na ce mata ehh, tace sai ranar da zan je ganin gida zamu tafi har da ita su gaisa da iyayena.
Wani dogon saurayi me kama da ita ya shigo É—akin, ba zai wuce 20years ba. Da fara'arsa muka gaisa suna kama da Maa É—in sai dai shima ingarman jikin Sir yayi, over over ya miÆ™a mata yace Brother ne yake magana yace a bawa matarsa. Idona akan abar ina mamaki wai ta nan ake magana mutum kuma yaji, abar da nake gani a film sai gata gaban idona har zan taÉ“a kuma zan yi magana da wanda na sani ta ciki, ina wannan tunani kuwa na jiyo muryansa na faÉ—in,"Nná»á»(Hello)".
Ita kuma tace masa,"Ibolachi(Good morning)".
Dama iya abinda na sani kenan a yaren shima kwanaki ne da muna chart da shi ya É—an koya min, yo wa ya san ma ko zan iya ni da na zo rayuwar dindin a cikinsu, yaren da na ke jinsa da wahala.
Sai da suka gama magana da Maa kafin ta miƙo min, na karɓa kaina a ƙasa, fita tayi sai naji daɗin hakan ko don na samu sakewar magana da shi.
Na riƙe a bar a hannuna ina zuba mata ido, a baki zan sa ko kuwa a kunne? Don lokacin da Maa ke maganar da shi ban lura da yanda tayi ba, muryansa nan da ke kashe min jiki naji yace,"Ola’m (My Diamond)".
Wani yanayin daɗi naji ya ratsa ilahirin ɓargona, idanuwana a lumshe ina sauke ajiyan zuciya, wallahi na azabtu da rashin jinsa Allah ma ya sani, ashe haka na ke mugun sonsa ban sani ba.
"Myyy are you there?". Kawai sai naji na fashe masa da kukan gaske, kuka har ina jan numfashi. Hankalinsa ya tashi ya shiga jero min tambayan mene? Me ya faru?, cikin shagwaɓan da ban taɓa sanin na iyata ba a duniyana na ce,"Tun jiya ban ji muryanka ba, ina ta kira bana samu, ban san wanne hali kake ciki ba, zuciyana nata min zafi, hankalina duk ya tashi".
With low voice da ke fita da amon damuwa da tsantsan kulawa yace,"Am so sorry Ola’m, banda yanda zan yi ne, duk abinda na ke hankalina na kanki, kowa sai da ya gane bana cikin natsuwata, har kwaɓa nayi a confrence meeting, ni kaina zuciyana bai samu salama ba sai yanzun da naji muryanki, amma kuma hankalina ya fi da tashi dalilin jin kukanki, kiyi haƙuri kin ji ina nan lafiya, ki daina kukan please bana son zubar hawayenki masu tsada, kukan yana taɓa min zuciya kar kisa ta samu matsala".
Na É—an ja numfashi nace,"To yaushe za ka dawo?".
A hankali yace da ni,"Muna Abuja right now amma na gama shiryawa tahowa kawai zan yi, ba zan iya ƙara yini ba tare da na jini tare da ke ba. Kin yi breakfast?".
Kaman ina gabansa na girgiza kai da cewan,"Na kasa cin komai tun jiya, kai kawai na ke son gani".
Ya furzar da iska wanda na tabbata sai da ya shafi goshi kamin yace,"Ki yi haƙuri kin ji, zan iso gareki nan ba da jimawa ba, amma ki daure ki ci abincin ko kaɗan ne idan na zo sai na ƙara ba ki".
Na ƙara shagwaɓe masa da faɗin,"Ni ba zan iya cin komai ba sai na ganka, baki duk babu ɗanɗano kuma kasan kai ne ɗanɗanon bakin nawa".
Haka yay ta lallashina da soyayyarsa, na amsa masa da to zan ci abincin amma ba da yawa ba. Ya tambaye ni ya naji yanayin nan É—in, banda wata matsala ko? Sun min tarba me kyau? Ya makwancina? Na takura? Garin da daÉ—i?".
A hankali na ce masa,"Naji daɗi sosai da yanda aka karɓe mu hannu bibbiyu, abinci har sai da muka bar shi, wurin kwana kuwa ai ƴan gida muka zama ba baƙi ba, garin kuma akwai daɗi duk da babu inda na fita".
Duk na ba shi labarin abun da ya wakana daga jiya zuwa yau, sai naji yayi farin ciki musamman da na ce masa family ɗinka suna da kirki kuma naji daɗin kasancewana cikinku, su Maman Khairi ma kowa yaji daɗi yanda ba su nuna mu ɗin ba nasu ba ne suka rungume mu da soyayya, Ina basa labarin irin adu'an da Sir ya dinƙa min sai naji kaman na tsoma shi cikin kogon nishaɗi.
"Myy dama na fada miki ai, Family na ba za su nuna miki banbanci ba, kowa zai so ki, nima suna sona sosai kuma suna son duk abinda na zo musu da shi, wani gatan ma tukunna dai, wataran Maa sai ta kusa goya ki saboda soyayya, za ki ga gata iya gata a wajen family na, an kai ki wurin Granny?".
Na ce masa,"Ehh mun je, Mommi ma duk ta raka ni na gaida su Uncles".
"Ohh wan nan tsohuwa sai da ta ja min ke yawo kenan ta wahalar min da ƙafan mata, ita bata zama da anyi baƙo ta dinƙi kaisa wuri tana aikin masa bayanin mutane, kema haka ta miki ko?".
Ina ƴar ƙaramar dariya na ce masa,"Ehh amma tana da shiga rai babu ruwanta".
Kaman ina gabansa na ji sanda ya ke jijjiga kai da cewan,"Uhmm da kike ganinta masifaffa ce, ke ma É—okin ganinki ne na sabunta, ita ko wasan jika da Kaka bata yi, kowa a gidan shakkarta yake, amma idan kika iya zama da ita bata da damuwa sam, ta dungure miki kai?".
Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata da ce masa a'a. Mun jima muna magana da shi kaman ba zamu rabu ba, haka kamar ma ba zuwa zai yi ya É—auki kayarsa ba. Wallahi sai naji ma ashe idan ina tare da shi nafi missing É—insa, kaman na bisa ta cikin abar haka na ji, haka na É—auka waya na masa text me daÉ—in gaske, kai wani hanin ga Allah ma dai baiwa ne.
Ina zaune ina ta juya over over ɗin a hannuna Maa ta dawo, tace to naje can wurin ƴan uwan nawa nan da ƙarfe biyu dai za'a fara taro. Nace mata to na tashi na fita tana ta cewa na yi kyau sosai a shigan kayan.
Da ƙarfe sha biyu ina kwance ni ɗaya a ɗakin da aka sauke mu, wayata ce a hannuna ina ta kallon hotunan ɗaurin auren da Yashaik ya saka a status, bana kallon kowa da kyau sai mijina, nayi nisa cikin kallon wani hotonsa naji an faɗo kaina, na razana zan kurma ihu sai aka toshe min baki, ido warwaje na ke kallonsa, yaushe ya shigo ban ji motsi ba? Mutsu mustu na shiga yi zan ture shi ina tsoron kar wani ya shigo ya ganmu, sai naji yace,"Nasa key a ƙofan fa".
Mirgina ni yay na zamana a samansa, yay min peck a goshi kafin ya shiga bawa fuskartawa kiss ta ko'ina, ina ta kakkaucewa ina ce masa ya bari wani zai iya shigowa ni ya ƙyale ni bana so.
Sai kawai yay min wata runguma da har sai da ƙashin bayana ya amsa. "Myyy kin san yanda na ƙagu na mallake ki kuwa? Halalina ce fa ke yanzu ko waye ma ya shigo ya ganmu a haka babu abin da zai ce, wuri ma za'a bamu kuma mutum shi zai ji kunya".
Sai ya kulle ido yana cika bakinsa da iska ya hure min a fuska, na lumshe ido shi kuma ya buÉ—e nasa yana ta kallona kaman zai cinye ni.
"I missed you so much matar Soja, kaman zan mutu fa haka naji".
Ina haɗiye yawu da ƙyar na ce,"Plss ka daina zancen mutuwa, yaushe ku ka dawo?".
"Yanzun muka shigo, wurinki na yo direct, kowa sai kallona yake don na tambayi ina amaryana suka ga na taho kai tsaye, laifi nayi hakan?".
"Ko wurin Maa baka je ba?".
Yay wani killer smile ya ce,"Na leƙa ɗakinta naga ba ki nan, na san kuma ta ganni don naji sautin fitar murmushinta".
Ɗan marin wasa nayi masa ina kwantar da kaina a ƙirjinsa na ce,"Salim ka ba ni kunya".
Yana nutsa yatsunsa cikin gashina yace,"Har an É—aura aure ma ba ki daina faÉ—in sunana ba gatsal ko, oookkk na ma gane so kike sai anyi abin kana ki sama min suna".
Ni dai da ace da hausa yake magana sai na fi jin kunya, fuskata na ɓoye a ƙirjinsa. "Ka san yanda ka tashi hankalina kuwa? Da sai dai ai kaji labari a media ana wata matar soja taje neman mijinta fadar shugaban ƙasa, don shi zan je na tsare da tuhumar ina ya kai min abin ƙaunata".