← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 113

Sashe 9

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na shiga gida na sanar da Ummani, tace to nayi sauri kar Abbaa ya dawo ya tarar da ni naja mata faɗa. Batun da Hamisu ya zo min da shi yay matuƙar girgiza ni har na kasa tantance ma wanne irin abu naji a tare da ni, wai faɗa min yake Yaya Nazifi yana sona kuma har jinya yay akaina, ya rasa ta yanda zai faɗa min ne tuntuni har wani yayi masa shigar sauri. Har dalilin janyewar da yay min duk sai da ya faɗa min wai saboda kar ya zama ya haddasa fitina don ya lura akansa zan iya cewa na haƙura da auren wancan iyayena kuma ba za su ji daɗi ba, shima kuma ba zai juri ganina da wani ba, amma tabbas yana tsananin sona kuma da gaske aurena zai yi duk da bai san ya zan karɓi maganar ba, amma idan na amincewa soyayyarsa yana roƙon da na basa damar gabatar da soyayyarsa kafin wani ya ƙara riga shi.

Lokacin da Hamisu ya gama isar min da duk saƙon Nazifi ban iya cewa da shi komai ba na koma gida. Har raina ban ji daɗin batun da ya zo min da shi ba, ban kuma taɓa tsammanin wannan maganar daga bakin Nazifi ba, hasali ni ban taɓa hasaso shi matsayin wanda zamu yi soyayya ba balle aure.
Kawai sai naji ina jin haushinsa sosai, amma wataƙila yana so ya yanke alaƙarmu ne kwatakwata shiyasa ya ɓullo da maganar soyayya tsakaninmu, ni soyayyar Yaya da Ƙanwa na ke masa kuma ita zan ci gaba da masa, ba irin wadda yake nema a yanzu ba soyayyar saurayi da budurwa.

Sai dai me duk yanda na so na ƙyamaci wannan batun da Yaya Nazifi ya zo min da shi abun sai ya faskara, Saboda yanda Yaya Nazifi ya nace ya dage wajen cusa min soyayyarsa, ya koma kusanta kansa da ni fiye da baya, shine rakani makaranta da ɗauko ni, kullum yana ƙofar gidanmu, a da idan ina farin ciki da ganinsa a gidanmu yanzu duk ba na yi, ina ta kaucewa faɗawa tarkon soyayyarsa amma sai da ya san yacca yay ram da ni a tarkon soyayyarsa domin yau da gobe tafi gaban wasa.
Ba zan ce ba, kuma ban san taya ba, lokaci ɗaya, rana ɗaya cikin lokaci ba mai tsayi ba na aminta da soyayyarsa, Soyayya me ƙarfin gaske ta ƙullu tsakaninmu, Wani irin soyayya yake muna min tsaftatattciya, Kulawarsa, ɗawainiyarsa da gudunmawarsa akaina suka ƙara ninkuwa, ya maida ni ƴar gata a cikin ƴan mata, soyayya mukewa juna me tsanani da har muke ganin ba zamu iya rayuwa ba tare da juna ba.

Kuma ba tare da ɓata lokaci ba iyaye suka shiga maganarmu don Yaya kasa haƙuri yay yace gwara yay magana a sabon matsayinsa kafin wani ya ƙara zuwa da neman aurena, don yana tsoron sharrin samarin da ke ta kawo min hari.
Ranar da ƙyar na iya sanarwa da Umman su Hindatu ta faɗawa Ummani Yaya Nazifi na so ya turo iyayensa ayi maganar aurenmu. Ranar kuwa ji nayi tamkar na buɗe ƙasa na shige ciki saboda yanda suka hau tsokanata, wai dama can ai sun san soyayya muke yi muke ta ƙaryata kanmu, Ummani ma tayi ta min tsiya kunya duk ta kamani na kulle kaina a ɗaki.

Ranar Asabar Malam wato mahaifin Yaya Nazifi da Æ´an uwansa suka zo suka nema masa aurena. Kamar yanda Abbaa yaywa magaban Salim bayani haka suma yay musu bayani kan cewar karatu shine burinsu akaina a yanzu, don haka ba zasu ce ba zasu bawa Nazifi Æ´arsu ba amma sai dai ba yanzu za su aurar da ni ba, idan zai iya jiran lokaci to, da yake da Yaya Nazifin aka zo ya amsa da cewar ya amince shima dama ba maganar aure yake yanzu ba tunda akwai tsare tsaren abubuwa da yake yi, sai dai yana so Abbaa yay masa alfarma ya bada kuÉ—in aure yanzu saboda wasu Æ´an dalilai. Lamari na babbar magana su Abbaa suka fahimci nufinsa suma suka ga dacewar bayar da kuÉ—in auren, don haka cikin sati guda kuwa Yaya Nazifi ya kawo kuÉ—in aure naira dubu ashirin.

Tsakanin Ummani da Abbaa ban san wanda yafi wani farin ciki da batun auren ba, domin na faÉ—a muku babu wasu iyaye da za su kasa yiwa Æ´arsu kwaÉ—ayin Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin mijin aure ba, haka babu wata budurwa da ba zata so ta mallake shi ba in har ba burin auren me kuÉ—i ne kawai a ranta ba.
Tafiya tayi tafiya soyayyarmu na ƙara ƙarfi, ina jin duk duniya babu wanda zai iya min irin wannan soyayyar tasa, haka ina ganin na gama dacewa da samun mijin aure. muna gabanin fara zana jarabawar neco sai Yaya ya fara matsamin lamba akan zancen shi gaskiya muyi aure, shi kawai zai fi samun kwanciyar hankali da natsuwa idan ina gidansa, shi yana buƙatar aure yanzu kam nan ba da daɗewa ba, karatu ne dai yay min alƙawarin ba zai tauyeni ba zai barni har in ga ƙarshen biro da takarda.

Raina ya ɓaci da wannan maganar tasa, domin ba haka suka yi da iyayena ba, an faɗa masa an jadda masa sai na kusa kammala karatun jami'a a ƙalla nan da shekara biyar masu zuwa, ya kuma ce ya amince shima yafi so sai ya mallaki wurin zama, amma shine yanzu ko shekara ba'a gama rufawa da magana ba zai fara wannan zancen saboda yaga da kuɗin aurensa akaina.
Dalilin hakan ya janyo saɓani mai girma tsakaninmu, muka dinƙa rigima da shi rigimar da bamu taɓa yi ba, na nuna masa fushina da bai taɓa sanina da shi ba tsawon tarayyarmu, haka shima naga fushinsa da ban taɓa ganinsa da shi ba a sanin da na masa.

Ni dai na tsaya masa akan bakana na cewan ba zan taɓa iya tunkarar iyayena da maganar aure yanzu ba, nima ina so in faranta musu in saka musu da irin ɗawainiyar da suka yi da ni a rayuwa, kuma karatun da zan yi na likita ba ƙaramin karatu ba ne don haka damata yanzu ce, yanzu ne na ke da damar natsuwa in mayar da hankali da ban da ɗawainiyar kowa akaina, don haka yay haƙuri kawai zuwa lokacin da aka ɗiba, yama rufe maganar aure ba yanzu ba kam, shekara biyar ne kamar yanzu zai ga lokacin ya zo, kafin nan in sha Allahu ya mallaki gidan kansa ma.

Amma yanzu idan yace aure ƙarshen shekara ina zai kai batun neman gidan zama da haɗa lefe da sauran hidindimu, ɗawainiyar gida bayan aure da tunanin kuɗin gidan haya da ta yara. Duk yanda na so in fahimtar da shi sam yaƙi fahimtata, yaƙi jin shawarar da na ke ta ba shi akan ko da fili ne ya fara mallaka tukunna, amma ina sai yay min mummunar fahimta ma, yake ganin kamar na daina sonsa ne, har yake cewa Safiyya ce take neman hure min kunne saboda ɗan uwanta me kuɗi yana sona, shi kuma bai da kuɗi kuma shi ɗan talakawa ne, ya kama maganganun ashe na raina nemansa, duk irin jajircewar da yake akan sana'arsa shine na ke ganin ba zai iya riƙe ni ba, shi ariziƙi ai na Allah ne, kuma shi dama fatansa Allah ya rufa masa asiri yafi ƙarfin ci da sha, kuma idan har akan ina ganin ba zai iya riƙe ni ba ne to naci amanar soyayyarmu.

Haka muka ta fafatawa da shi tsawon lokaci, kullum cikin rigima muke da shi akan fa sai an saka rana ƙarshen shekara. da yaga na cije na kafe sai ya koma sauke murya yana lallashina, ya dinƙa roƙona yana min daɗin baki, ƙarshe kuma sai ya fara faɗa min shi yana da matsala ne, yana gudun kar ya faɗa wani halin, kaza da kaza dai, da wannan ya shawo kaina har na yarda na amince don nima a gaskiya ina jin idan ba shi ba ba zan iya rayuwar aure da wani ba.

Ranar da najewa Ummani da maganar Yaya Nazifi yace yana so a saka rana nan da ƙarshen shekara, kasa cewa da ni komai tayi sai da Abbaa ya dawo ta faɗa masa, ai kuwa raina yay mugun ɓaci, na sha kuka iya kuka saboda irin faɗan da Abbaa ya dinƙa min, yana cewa wato soyayya har tayi tasirin da zata sa karon farko in fara tirjiya da maganarsu, to idan yaga dama sai ya mayar musu da kuɗin na su auren Nazifin ma ba zan ba.
Sosai Abbaa ya ɗauki fushi da ni kamar yanda ya ɗauki mugun zafi da maganar. hankalina ya tashi, shi kuma Yaya Nazifi idan naje masa da batun halin da ake ciki shima sai ya ƙara dagula min lissafi, na rasa ina zan saka raina, haka har sai da yasa na tada hankali a gida akan ni dai nan da ƙarshen shekara na ke so ai aurena, har ma na kai ƙarar Abbaa wurin Baba Tijjani lokacin kuwa ba ya gari.

Da wannan Abbaa ya fusata kuma don ya ƙure Yaya Nazifi sai ya ce shi kuma ya tsayar da auren nan da wata guda, idan har ya wuce haka to ba zai kaffara ba ya fasa bawa Nazifi ƴarsa, don haka nan da sati biyu ciff ya kawo kayan lefe. Wannan hukuncin na Abbaa duk ya ɗaga hankalinmu, musamman ma daga ni domin na san shikenan na rasa Yaya Nazifi, don kuwa a halin da ake ciki yanzu Yaya Nazifi bai da wasu kuɗi da ya aje da zai iya haɗa lefe balle akai ga tanadin wurin zama duk cikin wata guda.
Chapter 9 · 0% Book details