← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 113

Sashe 2

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma yay shiru kafin ya ƙarasa maganar,"Ki yi haƙuri kin ji".

Kai na sunkuyar ƙasa, ni kam wannan kalmar ta ban haƙuri da ke fitowa daga bakinsa ko da yaushe da ace tana tsiro da tayi a jikina. Haƙurin nasa duk yana bayarwa ne saboda mahaifiyarsa, Marfu'a ta taɓa ce mana in ace Mahaifinsa ne ya buge ni da mota to SJ zai iya tayamu shigar da ƙara kotu, kuma ba zai tsaya akaina ba don ganin na sami lafiya kamar yanda ya ke a yanzu, hasalima zai ce ina ruwansa shi shan sigarin mahaifin nasa ne ya janyo masa ba wani ba, ai anyi anyi ya daina shan sigari yaƙi ji.

Muryana kamar an shaƙeni na kalle shi ina jin gabana na tsananta faɗuwa saboda kwarjininsa na ce,"Bayya ka daina ba ni haƙuri don Allah...".

Ban ƙarasa ba ya ɗaga min hannu alamar in dakata, sai kuma ya ce da ni,"SJ not Bayya". Bayan ya huta da wannan ɗan guntun furucin ya ƙara cewa,"Su ƙannena ke kuma wata ce daban, just call me with me my name Sadeeq or SJ".

Kai na gyaɗa a hankali don tuni na fahimci bai son wancan sunan kam yafi so a kirasa da SJ ko Sadeeq, ƙannensa ma da suke faɗin Bayya ba so yake ba, shi a kirasa da zallar sunansa kawai, su kuma ƙannensa na ganin idan suka kira sunansa gatsal tamkar aikata zunubi ne, nima kuma gaskiya a irin yanda na taso da tarbiyar gidanmu ba zan iya faɗar sunansa ba domin ya girme min nesa ba kusa ba.

"Ƙafan na ki yana takuwa sosai yanzu?".

Ina É—aga kai na ce,"Ehhh, ta daina ciwon".

Ya gyaɗa kansa sau biyu, bai kuma ƙara cewa da ni komai ba ya mayar da ƙafafunsa cikin motar ya rufe ƙofar, ni dai ina tsaye kawai kamar me neman gafara duk a tsorace na ke ina jin jikina na kyarma, sai satar kallonsa na ke ina jin wani abu na motsawa a tare da ni.

Ji nayi suna magana da Na-Madam cikin yarensu wanda ban san me suka ce ba, sai kuma naji Na-Madam ya ce da ni.

"Idan kin shiga ki ce da Maamee su fito mu tafi".

"To".

Na amsa a hankali ina barin wajen da sauri. Yanda na shiga gidan kamar wadda taga wani mugun abun, na faɗa ɗakina ina haki tare da dafe ƙirjina da ke ta bugawa. Sai da na natsu kana na fito na shiga ɗakin Ummani, daga gefe na tsuguna na sanarwa da su Maamee saƙon su SJ na cewar su fito.

Ni dai tun daga wannan ranar wani sabon Al'amari ya sauka akaina, gaba ɗaya na rasa me ke damuna mene kuma dalili, domin kuwa tunanin SJ ya samu muhalli a cikin raina, komai na ke yi duk abun da na ke yi da tunanin SJ, haka idona a kowanne bugawar sakan da minti sai na tsinci haskawar hoton surarsa, bini bini kunnena ya jiye min sautin muryarsa, gaba ɗaya sai na rasa gane kan dalilin hakan, abu ɗaya kawai da na sani tunda na taso nayi hankali ban taɓa jin wani abu irin haka ba, kuma ban taɓa jin namiji ya burge ni ba har ina son wani abu nasa sai akan SJ.

Yawaitar faɗuwar gaban da na ke a duk lokacin da na ayyana kamar bayyanarsa a inda na ke sai na fara ramewa, ramar har tayi min yawa saboda rashin sake ganinsa da banyi ba tun wancan zuwan da suka yi gidanmu, sai wata rana ne ma Ummani ke ce min taje gidan zuwa yi musu godiyar ƙara turo kuɗin magunguna da suka yi da aiken da akayowa Abbaa na kayan abinci. Ranar ji nayi tamkar na fashe da kuka domin ko babu komai da taje da ni zanga SJ mutumin da na rasa dalilin tsaya min a rai da yay. Ban taɓa sanarwa da kowa halin da na ke ciki ba hatta Safiyya da ta gallazeni da tambaya ganin duk na sauya.

Bayan wucewar kwanaki masu tsayi ina daɗa girma da wayo da hankali na farga da cewar na kamu da son SJ, so kuwa me tsanani tun da har yana wahalar da ni duk da ƙarancin shekaruna, du da cewa so ba shekaru ba ne, don in ace a ƙauye muke tuni an min aure ba kuma zan kawo ya wannan shekarun ba ma ban fara tsayawa da saurayi ba, sa'annina kowacce da yaronta.
Kuma tun daga lokacin da na fahimci na kamu matuƙa da soyayyar SJ na yiwa kaina faɗa akan dole na yakice tunaninsa da sonsa a raina domin SJ ba tsarana ba ne ba ajin aurena ba ne, shi mai kyau ne, mai ilimi, mai kuɗi, mai ji da kansa, ɗan manyan mutane, to ina gamin haɗi tsakanina da shi daddawa a kunu? Shi kam ai sai manyan mata da suka amsa sunansu, masu ilimi ƴaƴan masu kuɗi ba irina ƴar Malam Salman me teburi a kasuwar rimi ba, wadda bata da komai ɗin da namiji kamar SJ me aji zai gani yace yana so, sai dai tabbas da ace zan samu wata dama da zan isar da saƙon zuciyata ga SJ lallai da nayi hakan, to amma ban san hakan me zai iya haifarwa a gare ni ba, ba na son wulaƙanci haka ba na son abin da zai haifar da matsala tsakanina da iyayena, amma tabbas ina son SJ kuma zan so rayuwar aure da shi.

Ganin fa ni kaɗai na ke kiɗa da rawata akan soyayya, tuni na miƙe da adu'a, na duƙufa akai babu dare babu rana akan Allah ya cire min son SJ ya kuma ƙara nisanta tsakanina da shi ta yanda ba zan gansa ba balle ya zame min famin ciwo, sai na fara samun salama domin kuwa babu abin da yafi ƙarfin adu'a, a hankali a hankali yawan tunaninsa da jin motsawarsa a zuciyata duk ya tafi sai jefi jefi, nayi hamdala na gode Allah don hakan ba ƙaramin alkhairi ba ne a gare ni na sani, tunda ba taɓa samun SJ zan yi ba, ba zai taɓa zuwa yace yana sona balle har ya furta zai aure ni.

Tambayar ma da na kewa kaina har kullum garin ma ya akai na kamu da sonsa? Shi son dama haka ya ke babu shawara babu neman izini?
Sau tari na kan yi murmushi takaicina idan na tuna kwanciyata a asibiti, wato lokacin a haukar tunanin da nake yi irin rawar jikin bani kulawa da tsananin nuna damuwa gami da tausayi akaina da SJ yay sai na tsammaci ko sona yake yi, tun ma da naga yanda ƴan gidansu kowa ke haba haba da ni kamar wata shaƙiƙiyarsu ba tsintuwar hatsarin titi ba, ashe duk ina cin alfarmar mahaifiyarsa ne da kuma kyan zuciyarsa ta masu imani, ba yanda na ɗauka na soyayya hakan yake a ɓangarensa da ɓangaren ƴan uwansa ba, hasalima yana da matar da zai aura wacca ba'a ƙasar nan take ba, naji hakan ne a bakin Ummani, wadda itama na san hira ce tayi hira tsakaninta da Maamee har ta san hakan, ranar kuma na ga rashin hankalina don kwana nayi ina kuka, har ina ayyana ina ma ace SJ ya fasa auren kowacce mace ya dawo gare ni, sai dai babu yanda zan yi haƙura da shi ya zama dole, silar ciwo ya haɗamu da su kuma samun waraka ya rabamu da su, don tun da na gama wartsakewa likita ya tabbatar musu da bani da wata matsala ta ko'ina muka bar jin ɗuriyarsu haka suma suka daina jin tamu ɗuriyar. Sai ma in wataran ana zaune ne haka Abbaa ya tuna su ana faɗin kirkinsu.
____________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR02FT5*

*Advert!*
_Ina masu son koyan kalolin abincin ƙasashen waje? Kamar irin su mandi rice, Chinese rice, chicken biryani, Afghani rice, eggs rice, chicken kabab, chicken biryani da sauran abincin labarawa da indiyawa masu daɗi da kwantar da hankali tun daga jin ƙamshin su. akwai kalolin salad irin su patoosh salad, normal salad, macaroni salad da sauran su. Baku da labarin Leemars_mandi zatayi class don ta taimakawa mata ta koya musu kalolin abincin ƙasashen waje wanda mu bamu san da su ba...?. Ta ƙware indai a wannan b'angaren ne shiyasa ake mata take da "Home of delicious and Arabian foods." ni na shaida Leemars_mandi ta ƙware a wajan sarrafa d'anye ya koma dafaffe. Ka da ku sake ayi babu ku class d'in zai zo muku nan bada jimawa ba akan naira 7k kacal, akwai ragi mai auki ga wad'anda suka fara biyan kud'in su. Domin neman ƙarin bayani nemeta akan wannan number 09030398006, ko DM a Instagram @Leemars_mandi._
__________________________________
A gefe guda kuwa Allah ya haɗa jinina da Nazifi Bala Mai Kalwa, nagartar Yaya Nazifi ita ta sanya muka yi shaƙuwa ta ban mamaki, ya zama tamkar ɗan gidanmu, kuma yanda ake zumunci da gidanmu da gidansu in ba sani kayi ba zaka ce ko dama can ƴan uwan juna ne mu. Kowa nawa ya san shi, ba shi da shamaki da ko'ina a cikin gidanmu, abota me ƙarfi ta ƙullu tsakaninsa da Yayyuna, ƙwarai shi kam mutum ne me shiga rai saboda kyawun halinsa da ɗabi'unsa ga uwa uba kuma addini, yayi haddar ƙur'ani har sau uku banda manyan littafan addini da ya haddace, duk wani mutum na ƙwarai zai so ace yay mu'amala da Yaya Nazifi, kai ba ma shi kaɗai ba zuri'ar Malam Bala Mai Kalwa kaf babu na yarwa, ko kwatance ake a unguwarsu na matasa na gari za'a sako sunan Yaya Nazifi a farko haka za'a sako maka sunayen samarin gidan Malam Bala Mai Kalwa.
Chapter 2 · 0% Book details