Sashe 102
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka muka dawo a gajiye, duk kuwa gajiyan da muka yi hakan bai hana Salim ƙara ɗora min wata gajiyan ba, don haka yace shi kam bai iya missing zaƙin madaran da ya sha jiyan, hakan kuwa na biye masa muka sha bidirinmu.
To Alhamdulillahi a sati uku da nayi cikin sabuwar rayuwar auren da na samu babu abinda zan ce da mahallicina sai godiya, ko a iya haka aka barni. Haka kuma ina yiwa duk wani wanda ya fuskanci ƙalubale irin nawa fatan samun kyakykyawan farin cikin da ta fi tawa, ina ganin soyayya da kulawar da ban sami irinta a baya ba, ban wani san tarairaya daga wurin miji ba irin yanda na ke samu a yanzu, ban san tattalin mace kamar ƙwai ba a wajen namiji, na dai san bautar miji da bautar ƴan uwansa.
Kuma a rayuwan baya na san na shaƙu da Nazifi fiye da dukkan tunanin me tunani, haka na so shi wani irin so da na ke jin ba zan iya rayuwa a duniyar da babu shi a tare da ni ba, sai dai mamakin kaina na ke yi a yanzu, to shin anya son da na yiwa Nazifi so ne da ake kira asalin so muraran? Saboda ji na ke yi kamar akan Salim na fara son wani ɗa namiji, son da har na ke jijjiga idan na sami gimlawar tabbatacciyar da zata iya raba tsakaninmu, a yanda na ke ji yanzu ji na ke kamar zuciyata dama can an halicceta ne da jinin soyayyar Salim.
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR16FT5*
Tsakanina da Salim zaman rayuwa mu ke yi me cike da jin daÉ—i, tsumammiyar soyayya, kwanciyar hankali, farin ciki da fahimtar juna. shi kam irin mazan da kowacce mace ke kwaÉ—ayin samu ne, wai ance soja bai sakewa iyalinsa to shi dai ba haka yake ba, a waje yake soja amma a cikin gida abokin iyalinsa ne.
Namiji ne me kyautatawa iyalinsa, me bawa iyali lokacinsa, me wasa da dariya da su, idan har yana gida to yana cikin matansa da yaransa ayi ta raha, yay ta mana barkwancin da cikinmu sai ya ƙulle don dariya, kuma ko da yaushe cikin tambaya ya ke ba ku da wata matsala? Me kuke so? Zan yi kaza ya kamata nayi mene shawaranku akai?. Duk abinda yaci a waje kuwa in Allah ya yarda muma sai munci sai in ba a garin yake ba amma sai ya rago ya taho mana da shi, babu nuna wani banbanci tsakanin mu, nuna mana yake dukka matsayinmu guda a wajensa babu wadda tafi wata, kyauta idan zai mana iri guda haka zai siyo mana, kuma shi ba irin mazan da sai sallah sallah suke wa mace suttura ba ne, in dai yay tafiya musamman in lagos yaje to zai kwaso mana ƙanan kaya kuma haka zai kwaso su kamar kayan tagwaye kala ɗaya sak, to suna ma ya koma ce mana Hassana da Hussaina.
Ni dai yaransa kuwa ba ƙaramin daɗi naji musu ba, samun uba irinsa rahma ne wallahi, bai da kyaran yaransa ko hantaransu, ko kaji yaro yaji muryan ubansa ko gyaran murya ya natsu har yana neman maɓoya, inaa ai shi da sun ji yo shi za su falla a guje tafiya taro shi, haka zai shigo da su a ɗaɗɗafe a jikinsa. zai zauna cikinsu yay ta wasa da su, shi ne yi musu makawuya, doki, ƴar guje guje, ball a compound haka zai tayi da su a cikin gidan, idan kuma karatu ne ya kama nan ma zai zauna ya koyar da su, ga ibada ko tafiya zai yi ya dinƙa roƙonmu akan mu sa ido akan ibadarsu, yaran har sun saba ma ana kira sallah kowacce zata wuce tayi alwala hatta da Rofi'at me shekaru huɗu, in bacci kuwa za su yi wallahi kaf ɗinsu da karatun ƙur'ani a baki haka bacci zai ɗauke su, na lura kuma koyarwar hakan ba daga gare shi ba ne kawai har da mahaifiyarsu don itama ba baya ba.
Na ƙara fahimtarsa sosai, shi me son a kiyaye ka'idojinsa ne, shiyasa ko da yaushe na ke iyakar ƙoƙarina wajen yin abinda yake so, na kuma guji duk abinda na san ba ya so, kullum godiya na ke ga Allah da ya sauya min abokin rayuwa, wanda sai a tarayyata da shi ne na san haƙiƙanin jin daɗin da ake kira a zaman aure, za ki yi bautar aure zaku ma ki huta a gidanki, ba irin gidan da na baro ba da ba ki da lokacin kanki. Salim har girki yake tayamu, ko gyara kike haka zai miƙe yace me zan tayaki da shi, idan kika hanasa sai dai ki jisa a toilet yana wankewa, babu girman kai sam a al'amarinsa, wani jin kai na shi me gida ne sam sam bai da shi. Kuma bai hana mu business don yana da kuɗi ba, ko kuma saboda matsayinsa, sam ina business ɗina na kunun aya da na ke yi tun a gida, cikin barrack ɗinmu siyansa suke kamar ruwa, har wani restaurant na ke yiwa suna zuwa su karɓa, to fa duk sanda zan yi indai yana gari muna zubawa a jarka shi kuma yana saka mana murfi da inji. Itama Kudrat ɗin tana yiwa wani restaurant baked meat pie, nan ma shi ke sakawa a oven ya barmu da zuba nama da dannewa, in ya so ma kwaɓin sometyms shi yake yi, kuma sam bai san ya sawa kuɗinmu ido ba, ya san muna samu amma in har mun tambaya kai tsaye zai ɗauka ya bamu, babu zancen tuhumar ina kuɗin da kike samu ko complain ɗin kin fiya a baki a baki, yace kuɗin mu namu ne mu yiwa kanmu hidima, sai in mun yi niyyan taimaka masa ne, shiyasa ga shi nan Allah na ta ƙara buɗa masa.
Lokaci lokaci haka zai kwashemu mu tafi yawon shaƙatawa, yanda yara za su hau lilo haka muma zamu hau kai, ni dai wannan rayuwar na min daɗi, to ta ina ma zaka yi baƙin ciki balle ɓacin rai? Ina kake da lokacin tuna baya? Rayuwar gidan Salim rayuwa ce ta jin daɗi da farin ciki, abinci wataran ma ce yake mu huta da girki sai ya ɗebe mu a tafi restauran aci, idan za'a dawo ayo takeaway ɗin wanda za'a ci da daddare, haka ya ɗebemu muje shopping kowa ya jido abinda yake so, wataran ya saki kuɗi kamar bai san ciwonsu ba, wani sa'in kuma sai yace ai siyayya saffa saffa bai da kuɗi sosai, wani sa'in ma sai ana zaune sai yace da da kuɗi da anje shopping, amma tunda babu ya zamu yi sai muyi haƙuri, kuma ba wai babun ba ne, a'a kawai yana koya mana rayuwa ne ta yanda in mun samu lafiya idan babu ma lafiya, musamman ma yaransa.
Tuni na koma bakin aikina, ashe already ya sama min aikin tun kafin auren anan wani asibiti Westend Hospital, sai da na cika sati biyu ya ke cewa na shirya muje ayi min interview, asibitin babba ne kuma private, cikin sati sau huɗu kawai zan dinƙa zuwa, monday and wednesday aikin safe, sai friday and saturday aikin yamma, kuma albashina ma har yafi wancan ɗari biyu zan ke ɗauka. Ina ta zuwa wajen aikina, idan morning duty ne da ni tare muke tafiya da Kudrat da ike ita tana da mota, yace nima kafin ya siya min tawa, idan na yi evening kuma zan hau cab a tagiya, Kudrat ɗin ita zata je ta ɗakko ni babu yanda ban yi da ita ba akan ta barni na ke dawowa da kaina taƙi, Salim yace shi bai yarda ya bar matansa da driver ba, gwara ya siya miki mota ki yi ta sakarftunki, Yaran dama kuwa school bus ke kai su ya dawo da su, bokonsu me haɗe da islamiya ce tun bakwai idan suka tafi sai shida da rabi suke dawowa.
Duk ranar da na ke evening da ke ina kaiwa tara na dare, kafin nayi closing sai dai naga yara sun zo sun kewaye ni suna Mommy mun zo ɗaukan ki, asibitin har an sanmu an san yaran, da yawansu ma ce suke ni da Kudrat sisters ne, kuma a haka na barsu ba wanda na nunawa abokiyar zamana ce, to in ma na faɗa sai a iya ƙaryata ni dan ba'a san kishiya da kishiya da irin rayuwan da muke yi ba, kanmu haɗe yake, abinda mijin mu ya ɗora mu akai shine mu riƙi juna, shi ma kuma bai fifita wata cikinmu, to ta ina wata zata tsiri buga iskanci?
Ni da kishiyata zama muke na mutunta juna da girmamawa, don tuni na tsayar da hankalina waje ɗaya na kama hanyar da ta dace, ki sakawa kanki banzan kishi ne fa ki sakawa kanki damuwa da zubar da aji, gwarama idan ace kisjiyar ce bata da kirki sai kema ki nuna mata kin fita. yanda muke zaune kamar ba kishiyoyi ba, akwai baƙuwar da aka yi sai zuwanta na uku ne ma take cewa wai dama kishiyoyi ne mu, ita wallahi idan ta zo yanda take samunmu ta zaci ya da ƙanwa ne.
Kudrat macece wadda ta iya mu'amalantar wanda ke tare da ita, zama na gaskiya da amana babu munafurci ko ƙullaci, macece me sauƙin hali da bata da damuwar komai, zuciyarta a buɗe take, bata da ruƙo sam sam idan abu ya haɗaku kai tsaye zata fito ta faɗa maka ko da zaka ji haushinta, haka ko laifi ka mata wallahi a ƙarshe ita zata baka haƙuri tace maka mece rayuwar? Nawa take? Wataran duk wayan gari zamu yi babu mu? So muke muje mu gamu da Allah lafiya, to don me zamu aikata abinda ba ya so? Gaba bata da wani amfani, idan an sami saɓani a fahimci juna kawai a wuce wajen a ci gaba da rayuwa. Kuma ƙarya ne kayi rayuwa da ita ba ka ɗauki ilimi ba, ina nufin ilimin iya zaman rayuwa da koma waye, nurƙufanci, ɓacin rai, jin kai Kudrat duk bata da wannan.