← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 113

Sashe 88

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nace,"To Maijidda me ma zai kawo ki gidanmu kuma".
Tayi murmushi me ciwo da kuma jin amsawar sunan da na kirata da shi kai tsaye, tace,"To ai Sa'ida ya zama dole a zo gareki, to yanayin yanda rayuwar ke ta ƙwallo da mu ne kowa babu sukuni, wallahi muna cikin tsaka me wuya sai dai adu'a kawai, Ni dai Sa'ida ba sai nayi dogon jawabi ba ina me bada haƙuri akan abubuwan da suka faru a baya tare da neman yafiyarki, ni da mahaifiyata da ma dukka ƴan uwana".

Nayi murmushin da ni ɗaya na san ma'anarsa nace,"Ah haba ni ai babu komai, yanzu ma banda Allah ya ƙadarta haɗuwarmu ai tuni na mance da ku balle batun mun taɓa rayuwa tare har wasu abubuwa marasa daɗi sun faru, ki manta kawai Allah ya kawo sauƙi cikin lamuran na ku, ni yanzu ai sai godiyar lillahi bana cikin wata matsala da damuwa".

A sanyaye tace,"Haka ne wallahi duk wanda ya ganki zai shaida, banda nayi miki farin sani ma ai ba zan saurin shaidaki ba, wallahi kin ƙara kyau kamar sake halittarki aka yi".

"Uhum". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen, ta dakatar da ni da faɗin,"To Sa'ida ni ina nema mana yafiya, haƙiƙa mun zalunce ki a rayuwa".
Na ce,"Na yafe Allah ya yafe mu gaba É—aya".

Sai naga taji daɗi sosai. Nan take bani labarin yanzu ma ta dawo ne daga police station Fati ce suka samu matsala da kishiyarta abin dai babu daɗi tana can tsare wurin ƴan sanda, to kuma ma tana kan hanya aka kirata Barira ƴarta auren ya mutu, Uwar mijin ta sakota gaba akan rashin haihuwa to yanzu can zata tafi taje ta taho da ita wai duk sun watso mata kayanta waje, bayan cin mutuncinta da zarafinta da suke yi ko da yaushe yanzu har suna cewa ma za su yi ƙararta saboda ƴar ƙanin mijinta da aka bata ruƙo ta ƙala mata sharri.

Nace,"Allah sarki".
A kunyace ta sake cewa,"Don Allah Sa'ida kifa yi haƙuri ko yawun bakinmu zai ƙare wajen baki haƙuri bamu yi komai ba".

"Hmmm ni fa Maijidda kin ganni a rayuwar nan tawa da na ke cikin jin daÉ—i da walwala na mance da ku da abinda ku ka min, yanzu ma ban da kun shaida ni zancen gaskiya daga ke har yaranki babu wanda na gane".

Sai ta shiga roƙona akan in daure in ƙarasa na duba Iyam, na ce mata ai bani ɗaya ba ce tare da mijina na ke, furucin da yasata zabura amma haka ta dake ta shiga taya ni murna har da cewa amma har nayi aure ba su da labari, a raina nace uhmm ana nan dai har yanzu da ƙarancin tunani, taron girma ai mutanen arziƙi ake gayyata ba na tsiya ba.
Tare da ita muka je wurin Salim, yana daga cikin motar ya buɗe ya zuro ƙafa ɗaya waje yana ce min,"Baby yanzu na ke shirin biyo ki ai, kin barni ni ɗaya babu daɗi?".

Na ce,"Sorry Sojana, ga wasu bayin Allah ku gaisa".

Yayan ta duƙa ita da yaran su ka gaida shi, yanda take faman gaisuwar ka rantse irin almajiran nan masu baran kan hanya. Ina ta kallonta ni dai a raina sai mamaki na ke yi, mace ƴar gayu da ƙwalisa amma kalleta fuskar hijabi ma a karkace, na kasa yiwa Salim bayanin wacece, ban san me zai iya faruwa ba idan nayi hakan don har ga Allah yana nuna min tsananin kishinsa akan tsohon mijina, sai Allah yasa ma bai tsaya tambayana ba ya zaro kuɗi masu yawa wanda a ƙalla na san zasu wuce dubu goma yace na basu.

Ai kuwa kamar anyi mata bushara da aljanna sai gata ta koma ƙasa ta duƙe a gabanmu tana zuba godiya da adu'a, to ina ruwan zuciyan da bata da tsatsan komai a cikinta, sai duk naji mugun tausayinta ya kama ni, idona ya cika da ruwan ƙwalla ganin tana hawaye, kana dai ganinta ka san ba'a jin daɗin rayuwar ana tsaka me wuya.
Sai da ta tafi ina kame kame nace da shi zan je na duba Mamarta ce aka kwantar, yace muje tare sai naji Æ´aÆ´an cikina sun kaÉ—a, ina tunanin abin ce masa aka kira shi a waya yace daga wurin aiki ne naje kawai amma kar na jima, ya koma cikin motar ni kuma na kama hannun Rumana muka wuce.

Muna tafe tana bani labarin makarantar islamiyarsu, littafan da ake musu bata jin wuyarsu ta riƙe karatun da nayi mata, jarabawarta ma duk ta biyu take zuwa, ni dai jinta kawai nake yi, dukkan tunanina ya tafi akan ina Nazifi da ya bar Iyam take kwance a asibitin Murtala bai kai ta babban asibiti na kuɗi ba, shi kuwa yana me?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, da naga yanda Iyam ta koma wallahi sai da na nemi ƙarfen gado na dafe har na zube ma ban sani ba. Jikina ya kama rawa tsoron duniya ya shige ni, Lubabatu ta taso da sauri ta riƙo ni, abinka da me ruwan ido tuni hawaye suka wanke min fuska, murya na rawa nace,"Lubabatu me yake damun Iyam?".

Sai itama hawaye suka sakko mata tace,"Wallahi ciwon kansa ne na hanta, kinga duk yanda ta ƙare ko".

Na rufe ido ina girgiza kai, sosai ta bani tausayi, ko gane wanda yake kanta ba tayi, lamarin ya matuƙar taɓa ni Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya.
Kusan mintina goma wajensu kafin nayi musu sallama, ban taho ba sai da na kira Sister Khadija ta haɗa ni da Yayarta da ke aiki anan asibitin, nace mata don Allah ga wa'annan bayin Allah'n take taimaka musu, Lubabatun taji daɗi sosai har ta kira Malam ta shaida masa, yay ta mini godiya yana cewa ya so ace yana nan ya ganni yaji daɗi, na karɓi account number ɗin Lubabtu na tura mata 20k na ce don Allah ta bawa Malam 10k, sauran kuma sayi wani butaƙan da shi, godiya ta dinƙa min kaman yawun bakinta zai ƙare.

Ta rakoni a hanya take faɗa min ibtila'in da Nazifi ya gamu da shi, wai Zahra'u ta yashe shi ta gudu ta barsa, ƴaƴansa biyu dukka ta hana shi, yanzu ma dai yana nan shima bai da cikakken lafiya, jininsa ne yay mugun hawa, hannunsa guda ya samu matsala dalilin faɗuwan da sanda aka ce ƙaramar ƴarsa ta ƙone, ana dai ta so ayi masa hoto a gano me ya samu wajen to ba'ayi ba har yanzu saboda matsalar rashin kuɗi, dama ga banki na binsa maƙudan kuɗaɗe, ga shi shagon da yake gadi an haura anyi sata an ce da sa hannunsa lamarin dai babban lamari ne, yanzu haka anata cuku cukun gano gaskiya saboda sun ce ba zasu yarda ba sai ya biya su duk ɓarnar da aka yi, take cewa wallahi ta tabbata har da hakkina, tana ta roƙona akan na yafe musu, na ce,"ai ni Lubabatu ba ki min komai ba wallahi, zaman da muka yi ba zan taɓa manta alkhairinki gare ni ba". Tace,"To don Allah na yafewa Iyam da Yaya Ƙarami".nayi murmushi me ciwo da takaici na ce,"Iyam ma ai na yafe mata". Tace,"To Yaya Ƙarami fa? Wallahi Sa'ida ba kiga ba duk yana cikin damuwa, ko ranar nan ina jinsa yana faɗin yayi nadamar abubuwan da ya aikata miki". Wani murmushin kawai nayi nace,"uhumm".

Har bakin mota ta rakoni, suka gaisa da Salim itama sai da ya bata kuÉ—i, haka tayi ta masa godiya itama cikin jin daÉ—i tana gaya min haÉ—uwarmu tayi musu rana saboda yanzu haka tun shekaranjiya ake neman kuÉ—in da za'a siya alluran Iyam da scanning É—in da za'a mata, bayan nan tana faÉ—in ta taya ni murna sosai da ci gaban da na samu.
Ni dai tunda na shiga mota hawaye na ke ta yi, matuƙa na tausayawa Iyam, haka na tausaya musu dukkansu, Nazifi ne kawai banji komai ba a kansa. Salim kuwa na ta complain akan da ya san da haka bama zamu je asibitin ba, ban iya masa magana ba har muka ƙaraso gida, yay lallashin duniyar nan amma ina ni dai na rasa ta yanda zan dakatar da hawayena zuba, haka ya haƙura muka yi sallama zuƙatanmu duk babu daɗi ni da shi.

Ko da na shiga gida ma duk sai suka yo kaina da tambayar me ya faru, na dai ce musu rasuwa aka yi a asibitinmu na shige ɗaki kawai na rufo ƙofa. Wayata na ɗauka na kira Lubabatun don sai da muka yi exchanging number wanda Malam ne yace ta karɓa masa lambata, tana ɗagawa nace ta lissafa min kuɗin bill ɗin na su sai ta tura min account number, haka na tura mata dubu asharin a madadin dubu arba'in da ake nema, to nima babu kuɗin ne da dukka zan tura mata. Ba jimawa sai ga kiran Yayan Shago wanda yake ta min godiya, shima yana bani haƙurin abubuwan da suka faru, ya haɗa ni da Malam wanda yace yana matuƙar godiya da abun arziƙin da na yi musu haka yay ta shi min albarka, yace ai a kasuwarsu ma an faɗa masa Abbaa yaje nemansa bai nan amma yaga ya bar masa invitation, nan yay ta min adu'a tare da fatan alkhairi, nayi godiya kafin nan muka yi sallama.

Da magriba na fito zan yi alwala, sanyin magriba duk yasa an shishshige ɗaki, na aje buta zan tsuguna sai ga yaro ya shigo, yace wai an aiko shi wurin Sa'ida, na ce masa menene ya miƙo min baƙar leda an nannaɗeta kamar laya yace wani ne a waje yace a bani.
Karɓa kawai nayi, wa zai min aike idan ba Salim ba, ni kuma a yanayin da na ke ciki ban jin zan iya fita na sameshi.

Na idar da alwalar na shiga ɗakin Ummani na sauya kayan jikina, take nuna min buhun kayan miyan da ƴan ƙauye suka ƙara kawowa, nace an gode, bata lura da yanayina ba nayi saurin fita gudun kar ta tsare ni da tambaya.
Sai da na idar da sallah tukunna na kunce ledar, takarda ce a ciki ƙarama, na warwareta ina duban gajeran rubutun da ke jikinta.
Chapter 88 · 0% Book details