← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 113

Sashe 112

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuma a ranar da takewa Iyam wannan hargowan lokacin ya fito daga ɗaki da niyyan cin mutuncin Marawiyyan kawai sai ya tadda ta tunkuɗa Iyam baya ta zame akan wannan ruwan karkashin, shikenan daga ƙwaluwar da tayi a ƙasa kuma sai ciwo, ba magana ba motsi. Akai neman kuɗin maganin aka rasa a sa'ilin har sai da ya tuna da alkhairin Sa'ida gare shi, sanda suna tare da ta ɗauka kuɗin makarantarta ta siyar da kayan ɗaki ta ba da kuɗin maganin Iyam har aka mata aiki, haka da sanda yaje asibiti aka ce masa yanzu ta tafi ga kuma kuɗin da ta bayar, ranar yay kuka iya kuka, yayi nadama da danasanin wulaƙanta Sa'ida da yayi a rayuwarsa, ya kuma ji takaici da baƙin cikin sauya kyakykyawan halinsa da yay, ga shi Allah ya nuna masa ƙarshensa, ya tozartata ya mata cin kashi ita da ƴan uwansa akan rashin haihuwa ga ta can cikin gata ita da yaranta.

Idanuwansa suka rufe yana jin zuciyarsa na masa ciwo, sai yay murmushi yau ga shi ɗanta ya ramawa uwarsa abinda yay mata, sai ya kai hannu ya shafo wurin da ball ɗin ta ƙwalu, daga jin zafin ball ɗin ma ka san me shegen tsada ce. Ya buɗe idanu a hankali yana kai dubansa gare su, ganin yanzu saɓanin na ɗazu, yanzu tana tare ne da mijinta wanda ya fito daga cikin arniyar mota, tana karanta masa ƙiriniyar da Ayman yayi har tana yi masa nuni da inda Nazifin yake tsaye.

_"Nazifi Allah kar ya ƙara nuna min kai a rayuwata, Allah kar yasa na ƙara tozali da fuskarka har na koma gare shi, macuci azzalumi"_

Kalaman nata na wancan lokacin suka haska masa cikin kai, a ƙasan ransa yace haƙiƙa Allah ya amsa miki adu'anki, ga ki ga ni, har kina iya nuna ni daga nesa amma idanuwanki ba su samu damar ganina ba. Hawaye suka daɗa sakko masa masu zafi, a hankali ya duƙe a ƙasa zai kwandon gyaran. Ɗagowan da zai yi kuma Salim ya ƙaraso wajensa, ganinsa ɗin sai da gabansa yay mugun duka, har yana saurin ja da baya.
Salim É—in na dubansa da murmushi yace,"Ba wani abu ba ne".

Nazifi ya haÉ—iye yawun wahala, jiki na rawa ya ce,"To ai ranka ya daÉ—e ganinku ne akwai furgici, Allah yasa lafiyar". Ya faÉ—a da tsammanin ko Sa'idar ce ta faÉ—a masa abubuwan da yay mata ya zo ya kama shi.

"Ranka ya daÉ—e ni dai wallahi ba mai laifi ba ne".

Yay maganar cikin rawar murya da ruÉ—ewar ciki. Still da murmushi fuskan Salim ya ce,"Ni ne Mahaifin wannan yaron, Mahaifiyarsa na faÉ—a min rashin jin da yay ne".

Da saurin murya da na jiki Nazifi kamar zai duƙa masa yake cewa,"Laa ai babu komai, yaro ma shi da yake wasa, ball ɗin kuma ai kayana ta buga ba ni ba, batun haƙuri ma ka bari kawai ranka ya daɗe, don Allah a bari ba sai an bayar ba".

Foridat ta ƙaraso wajen tana cewa,"Paapa Mommy tace ga takalmin Ajmal a gyara masa, zai shiga mota ya gurɗe ƙasan ya ɗago kaɗan".

Da Salim na shirin ya ce a ƙyale kawai a siya masa wani tunda store za su shiga, sai kawai ya bari Nazifin ya gyara ɗin shima ya samu wani abun, tunda ba lallai yay ciniki ba fitowarsa.
Shi kuwa Nazifi mamaki ne ya kama shi jin suna yare, ƙarya yake yace bai ji burgewan su ba musamman ma Sa'idan da Ƴaƴanta, yanda ta buga shigan alfarma ga haƙoran makkanta sai ƙyalli suke daga nesa.

Hannu na rawa ya jawo kwandon kayan gyaran ya karɓi takalmin hannun Forida ya shiga gyara, ya gama Salim yay yay da shi ya karɓi kuɗin gyaran yace a'a su barshi, takurawan da Salim yay masa dole tasa shi miƙa hannu biyu ya karɓa.
Ya shiga zura hannu cikin aljihun koÉ—aÉ—É—un kayansa lalubo canji.

"Ranka ya daÉ—e bari na É—an samo canji a can, da yake ba a samu an yi cinki ba ne tun fitowan nawa".

Ya faɗa sai faman buɗa haƙwara yake duk a ruɗe, ya bi ya dabarbarce, Salim da fara'ar nan tasa ya ce,"No barsa kawai ka riƙe gaba ɗaya, idan na koma da shi ma Madam faɗa zata yi ban barwa mabuƙaci kamarka ba, Allah ya bada sa'a".

Dubu ɗaya ce sabuwa fil, amma haka Nazifi ya zube ƙasa yana ta jera godiya. "Na gode, Na gode ranka ya daɗe, Allah ya raya iyali, Allah ya ƙara matsayi da ɗaukaka, Allah ya jiɓanci al'amura".

Salim yaja yaransa suka tafi, ya so da cash a jikinsa da yawa ya ɗan yi masa ihsani don ba ƙaramin basa tausayi yayi ba, abin a taimaka masa ne tabbas, sai dai bari su fito daga siyayya sai ya cire kuɗi a ciki ya basa, tunda yaga kamar nan ɗin ne wajen zaman sana'ar tasa, duk da masu sana'an gyaran takalman ba su fiya zama wuri ɗaya ba sun fi bin hanya suna kaca cau kaca cau.
Nazifi na kallon Sa'ida daga nesa gwanin ban sha'awa ita da iyalinta, Sa'idansa ta zama matar manya, ji yay kamar ya bisu, kamar ya isa gabanta ya duƙa ya ƙara neman gafararta, yana kallo suka shiga cikin Sahad Store ɗin, fuskarta da ta mijinta cikin nishaɗi da farin ciki, ga wani bayyananiyar soyayyar junansu da ka kalle su.

Jiki a matuƙar mace ya juya ya shiga ta wani ɗan loko, bai yi tafiya me nisa ba ya isa wani gajiyayyan gida, ƙofar langa langar gidan duk a farfashe ta lanƙwashe. Iman da Ƙanwarta Mubina na can ƙofar wani gida suna wasan ƴanta, suka kwaso a guje ganinsa ya dawo don ya hana su yawo, su kuma rashin jin daɗin zaman gidan ke sawa su fice. To matar gidan jarababba ce, ta daka ta kuma daka, su yi kukan ta kima musu uban aiki, abinci sai taga damar ba su ma, tayi ta musu gorin ai uban na ku me gyaran takalma da kwasan kwata bai kawo ya aje ba, don haka ba zan ba ku ba, sai in su ci sa'a ne wataran ta ke ɗan tausaya musu ta ba su.

Duk sun yi furkai furkai da su, da ganinsu ma ka san ba su yi wanka ba, riga daban É—an kwali daban, rashin uwa ma dai gaban Æ´aÆ´anta babu daÉ—i.
A tsakar gida suka sameshi ya zauna bakin rijiya ya zabga tagumi, suka shigo a tsorace kar ya dake su ko faÉ—a. Iman me wayon ita ta lura da kaman kuka mahaifin na su yake.

Ta ƙarasa da sauri ta zauna kusa da shi tana faɗin,"Baba sannu da zuwa".
Kallon su kawai ya tsaya yi, tausayinsu ya kama shi. Iman É—in ta zare masa hannun da yay tagumin tana cewa,"Baba ka daina tagumi, kuma naga kaman hawaye ka ke yi, Baba wani abu ne ya faru?".

Numfashi ya sauke, cikin dabara ya goge hawayensa don ka kaÉ—an ba ya so yaransa ke ganin cikin irin yanayin nan. "Ina ku ka je?".
Tayi ƙasa da kanta a hankali tace da shi,"Baba muna ƙofar gidan Malam Musa muna wasa".

Murza fuskarsa yay. "To kun samu abinci kun ci?".

Suka girgiza kansu a tare alaman a'a. Ƙwalla ta daɗa cika idonsa yana zura hannu cikin aljihunsa ya zaro dubu ɗayan da Salim ya ba shi. Ya bawa Iman ɗin yana cewa,"Ku je kantin Gambo ku siyo taliya ƴar hausa ta ɗari uku, sai manja na ɗari, sai ki haɗa abinda za ku daka yaji".

"Tom Baba". Suka faɗa suna miƙewa cike da murna, sai dai suka je soro Mubina ta dawo tana cewa,"Baba na siyo biskit don Allah?".

Kai ya É—aga mata,"Ehh ki siyo idan akwai canji".

Cikin wani irin yanayi da shi kaɗai ya san a halin da zuciyarsa take ya goge hawayensa. Idanunsa hoton iyalin Sa'ida kawai ke haska masa, yaranta tsab tsab da su cikin shiga ta alfarma, yara kamar larabawa kaji ina ma naka ne ko ka sace ka gudu. amma ga nasa yaran kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin jaka. Ba su daɗe ma da dawowa hannunsa ba don ba su cika shekara ba, Zahra'u ta kawo masa su zata yi aure, tun rabuwar da suka yi bata ƙara aure ba sai yanzu, to mijin da ta aura yace ba zai riƙe ƴaƴan da ba nasa ba, ta dage ta tafi da su gidan Kishiya ta sakota gaba da sharri da makirci, a dole ta tattaro yaran ta kawo masa abinsa, ga su nan cikin rashin galihu makaranta ma ya kasa saka su.

Marawiyya ta fito daga ɗaki, ganinsa ta wurga masa wani matsiyacin kallo tana jan tsaki tare da ɗaukan buta ta shige banɗaki. Haka suke zaune da shi sam bata ganinsa da daraja, ina ma yake da gashi idon da zai samu arziƙin gaisuwa daga wurinta. Dama ita taji ta gani tace da shi su rufawa juna asiri, tunda shima bai haihuwa ita kuma taƙi auruwa sai gantalin zawarci take, ba namijin da ke iya zama da ita, shi kuma saboda yaransa ma ya yarda saboda ya samu me riƙe masa su, to ashe ma gwara bai auren ba ya zauna ya riƙe yaransa a gidan su.
Chapter 112 · 0% Book details