Sashe 100
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗi hakan yana manna min kiss a saman gashina, cikin soyayyarsa da yaƙinin samun kwanciyar hankali da dawwamemen farin ciki na kewaye shi da hannayena ina rugume shi na ce,"Ina sonka Mahbub".
Da wani sauri ya ɗago fuskana. "Mahbub?". Na jijjiga kai,"Beloved". Sai ya ƙara rungume ni yana faɗin,"Thank you for the name".
Muna haka ya duba wayansa. "Kinga kiran Kudrat har four times, Allah yasa lafiya". ya faÉ—a yana kiran wayar kafin ya tashi tsaye ya saka doguwar riga ya fita bayan yace min yana dawowa yanzu.
Fitarsa duk sai naji babu daɗi, zuciyata na harbawa, daga daren jiya zuwa safiyar yau adadin harbawan da zuciyata tayi yafi ƙarfin adadi, na ƙara nutsewa cikin kogon sonsa da kishinsa.
Na bi ƙofa da kallo idona na ƙara haska min yanda ya fita da hanzarinsa saboda kiran Kudrat ɗin, duk yanda na so na danne na kawar amma na kasa, nan take naji raina ya ɓaci, gudun faɗawa cikin wani yanayi nayi saurin sakkowa akan gadon ina ambaton sunan Allah a cikin raina, wadrobe ɗinsa na buɗe na ɗakko jallabiyarsa na saka, sannan na shiga gyaran gadon, ban bar ɗakin ba sai da na gyara ko'ina tass, na je ɗakina na ɗakko turaren wuta na zo na saka, ai fa turaren Ummin Sauma ba na banza ba nan da nan ƙamshi ya gauraye gidan.
Bayan na kammala na koma ɓangarena, na shiga wanka haka ina wankan ina aikin ƙunci, turarukan wankan da nayi amfani da su kuwa idan ka shigo ɗakin zaka tsammacin kamfanin turare ka shiga. Ina zuge closet na yi katari da an gyara min ita, kayana an jera su jere me kyau, abayas ɗin duka a hanger suke, ansa wadrob balls sai ƙamshi cikinta yake. Amma ya aka yi haka? Naga ai sai da ya rufe ɗakin da key tukunna muka fita jiya da daddare, ko kuma da ina bacci aka zo aka karɓa, na san gyaran ba zai wuce na su Maman Khairi ba, murmushi nayi ina gode musu da ƙoƙarinsu, ɓangaren da aka jera atamfofi na kai hannu na ɗakko wata super me kyan gaske, ɗinkin riga da skirt ne simple ba me hayaniya ba, dama gani da hips masha Allah, na yi simple make up ena nayi kyau abun burgewa wanda na san dole mijina zai yaba.
Bakin gado na zauna tare da ɗakko wayata kafin na fita naje na gaida su Gwaggo, ina dubawa kuwa sai ga misscalls ɗin Safiyya har uku, Allah sarki ƙawar amana tuni fushin da na ke da ita akan kwana wurin kishiyata yabi iska, na bi bayan kiran tana ɗagawa kuwa da karaɗinta tace,"Su Beb an dirji soyayya wato sai ma yanzu naki garin ya waye, to ya amarcin da brother nah? I hope komai dai normal na san harka da sojojin nan ba wasa ba".
Samun kaina na yi da jan tsaki nace,"Daman abinda kika kira ki tambaya kenan gulmamma?".
Sai tayi shewa da faɗin,"Ahh lallai ne matar soja, kin sha madarar daɗi kin ƙoshi, bakinki a buɗe kike min tsaki ko".
"Nayi É—in".
Sai ta sassauta murya da cewa,"Na ji ki a fusace, lafiya dai?". Amon muryarta ya fito da kulawa.
Na rumtse ido sosai ina cewa,"Mayi magana idan kin shigo". Na faÉ—a ina yanke kiran".
Abbana na kira, mun jima muna magana da shi a wayar, yana gida yana faɗa min bai ma fita kasuwa ba saboda ana masa gyaran sabon teburin da ya siya, muka yi waya da Ummani ma har da Kaka, duk sunata tambayana ya baƙon waje, albarkar nan tasu da nasiharsu ta kullum ba su fasa sa min ita ba, Jin muryar iyayena sai naji komai da ke zuciyata na rashin daɗi yabi iskar ɗakin ya tafi.
Mun gama waya da Yashaik a lokacin Salim ya shigo, yana aikin bina da kallo kamar sabon gani a idonsa, nima kuma kaina na san dole ya kalle ni saboda kyan da nayi.
Hannaye harɗe a ƙirji yake ce min,"Yaushe muka yi da ke ki taho nan?".
Nayi masa wani irin kallo me tafiyar da imanin masoya nace,"Naga ka É—an jima ne, ni kuma ina so nayi wanka naje mu gaisa da su Hajjo".
Ƙarasowa yay ya zauna kusa da ni yana kama hannayena yace,"To na wa wankan kuma fa? Ni ban iya wanka da kaina ba, ga shi kinyi kwalliyan da ba zan so ya ɓaci ba".
Sai ya marairaice min kaman yaro,"Shiyasa da kin ɗan yi haƙuri kin jirani na zo mun yi tare, ba ki san wankan miji da mata tare na ƙara danƙon soyayya ba, ko tsoro kike kar nayi maimaici?".
Murmushi nayi ina jan hancinsa da cewa,"Kai bakinka ko, yanzu to ai sai ka tashi muje na taimaka maka ɗin, amma saɓi ɗaya zan maka ka ƙarasa sauran da kanka".
Sai da ya ɗan matsa cikina kafin yace,"Ahaf ki yi min saɓi ɗaya saboda kina gudun kar labari yasha banban kenan, dama kema na san ai ba ki ƙoshi da ni ba".
Ƙaramin filo ɗin kusa da ni na ɗauka na ƙwala masa, sai ya miƙe yana dariya da cewa,"Tunda kin min wayo ba za ki min wankan ba yanzu bari naje na shirya, idan ban wanku ba ke ce kika ja kar ki zo shimfiɗa kina min ƙorafi. Sai kije wurin su Hajjo ɗin nima naje mun gaisa da su, kafin nan na gama sai muyi break fast ko ma nace lunch tun da dai har azahar ya kusa".
Na miƙe ina cewa,"Break fast ɗin ƴan boko ba, ka muje na maka wanka to ko da na ɓaci sai na sauya, kwalliyan ai dama na ka ne, kuma ka gani har ka yaba, so sai a ƙara yin wani ai ba za'a gajiya ba wajen yin abinda zai burgeka".
Janyo ni yay jikinsa yana shafa gefen fuskana, sai faman yabon kyan da nayi yake yi, a hankali hannayensa na shafa marata zuwa cikina yace.
"Soon wannan shafaffen wajen zai É—auki ajiya insha Allahu".
Maganar ta taɓa zuciyata, na ɗago ido na kalle shi da zummar yin magana, kamar yasan me nake shirin faɗa yayi saurin haɗe bakinmu waje guda, sai da yay me isarsa kana ya rabu da ni yana cewa,"Just sai Allahumma amin".
A sanyaye na ce,"To Allahumma amin".
"Awwa ko ke fa Myy, adu'a na sauya ƙaddara so muyi adu'a kawai Allah ya bamu me albarka".
"Ko ban samu daga gare ni ba ma su Isioma sun ishe ni". Na faɗi hakan ina tunawa da baya, yanda duk sona da yaran Nazifi haka mahaifiyarsu tayi min katanga da su a ƙarshe har aka min ƙazafin kisa.
Haɓarsa bisa kafaɗana yace,"My muna da buƙatar ƙarin yara, Baby ina son yara, so na ke ku cika min gidan nan da ƴaƴa inta kallon ku ina jin daɗi".
Kunnena ya É—an ciza tare da raÉ—a min magana, wai zan basa na rana yaji an fara tsikarinsa, sanyayyan murmushi nayi me faÉ—i wanda muka yi a tare da shi.
Sai ce yay,"Na shiga na samu kuna magana da Safiyya a waya, saboda asaran kati irin na ku kuna cikin gida É—aya, ko da yake na san gulmana aka yi".
Na waro ido waje ina cewa,"Gulmanka kuwa?".
"Ehh mana in ba haka ba Me kika ce mata to? Nasan dai ba za ki iya faɗa mata kin wahalar mata da ɗan uwa a daren jiya ba, sai dai zan so ki sanar mata ɗan uwanta ya rasa hankalinsa ta dalilin wannan halittar me kyawun sura, har yana tantamar akan da gaske ne kuwa matarsa ta taɓa wani auren a baya ba rufe shi kawai aka yi ba, Ki ce mata gaskiya ina da ja akan hakan, don ni hanyar da na shiga ba a taɓa taɓata ba".
Murmushi nayi kawai ina sunkuyar da kaina, ina jin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ni, ni kaina a jiya nayi matuƙar mamaki, ko da yake ba ƙaramin gyara su Maman Yasmin suka min ba, ni kaina na rikice balle shi.
Tare muka fita da shi a É—akin, sai da na je na haÉ—a masa ruwan wanka da turarukan wankan da nayi amfani da su, na so nayi masa wankan sai dai yace no na bari nayi masa na anjima yanzu na je wajen su Hajjo kar na barsu da tunanin lafiya, su tsammaci ko yay musu kaca kaca da Æ´arsu ne.
Ina dariya na fito a toilet É—in na É—akko masa kayan sawa na ajiye masa, kana na fito na wuce wajen su Umman Batula, ina zuwa kuwa na faÉ—a jikin su Maman Yasmin cike da kunya har ina kasa É—ago ido na kalle su.
Hajjo tace,"Allah ya dawwamar da ke a wannan farin cikin da na ke gani a fuskarki".
Dukka aka amsa da amin. Wai sai naji suna min batun ai yanzu za su wuce, Abbaa ya kira É—azu yana ta faÉ—a ba ko kunya sun zo sun yi zamansu a gidan siriki.
Na ce,"Kwana biyun kawai? Ni fa nayi zaton ko sai zuwa jibi ma za su ku tafi".
Maman Yasmin tace,"To ni har zagina ma sai da yay, yace bai ga amfanin ace sai mun kwana a gidanki b, mene ma na zuwan to tunda mun bada amanar taki ai sai mu kamo hanya, gidan na ki ma zo daga baya".
"Kayiii Abbaa to shi da sai na zo gidana babu wani nawa, kenan ma ni na kawo kaina".
Mama A'i tace,"Ai kin dai san halin Babanki, shi da ya so ma ku taho da mijin kawai ba sai an miki rakiya ba".
"To kuma da gaske yau É—in za ku tafi?".
"Ƙwarai ma kuwa, ai yanda kika ganmu nan ke kawai muke jira dama muyi sallama, shima kansa Salim ɗin da ya zo yana ta mamaki yace ba zamu ƙara kwana ba, muka ce aa bar muku gida zamu yi ba a yi iyayen kawai ba".