Sashe 101
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai duk sai naji babu daɗi da zancen tafiyar tasu, jikina yay sanyi, Maman Khairi na tsokanata wai ni da naje na ƙule ma na barsu, idan suka ƙara kwana ai abinda yafi haka za su fara gani.
Maman Khairi ke ce min,"Ai da safen na fito da ke ƙarfe shida fa Abbaa ya doka mana kira Allah yaso wayar Maman Yasmin ce". Ta faɗa tana dariya. "Da Safiyya ai naci karo a falon, dama ina cewa zamu je ɗakin naki a shirya miki sauran abubuwa sai tace ai ta gyara miki komai".
Sai naji raina yay min babu daÉ—i, na san fa tabbas Safiyya zata iya gyara min É—akina amma saboda banzan kishi ban wani kawota cikin raina ba.
Mama A'i na ta faɗa min kirkin Kudrat, suka ce ita ta zo ta tada su da asuba, da kanta ta shiga toilet ta saita musu ruwan zafi suka yi alwala da shi, kuma kafin bakwai ta kawo musu abin kari tana ta ce musu idan da akwai wani abu da suke buƙata suyi mata magana, sai faɗar kirkinta suke yi, Gwaggo na cewa ance dai baka saurin shaidar mutum amma ita wallahi har zuciyarta taji Kudrat ta kwanta mata, haka kuma ta shaidata shaidar da tana da tabbacin ba za su ji labari mara daɗi ba.
Nan suka sakani gaba suna ta min faÉ—a da nasiha gami da shawarwari, sai ma da Hajjo tasa aka kira Kudrat suka haÉ—e mu gaba É—ayanmu, hannuna cikin nata haka Mama A'i tasa muka yi musabaha tana cewa adu'anta da dukkan fatanta yasa hannayenmu ba zasu rabe ba. Kudrat É—in har da hawayenta tana ce musu suyi tayi mana adu'a don Allah kar a samu shaiÉ—anin da zai raba kawunanmu.
Ina zaune nan wajensu anata hira, Umman Batula tace ba don aure me kai mutum inda bai tsammani ba ita ina ta taɓa tunanin zata zo wannan garin me uban nisa, sai ga shi ta kawo ƴa har ta kwana ma.
Ana ta shaftan hira ni dai duk a ƙage na ke na tashi na tafi wurin mijina, hankalina na kansa ban son barinsa ahi kaɗai. Can sai ga Kudrat ta dawo da ƙaton tray na abinci ta aje, suka shiga yi mata sannu da aiki da ɗawainiya da su.
Hajjo na cewa,"Ya kamata ki huta haka tun safe kike kai komo da mu, kinga mu abincin safe da muka ci har yanzu a ƙoshe muke wallahi, ya kamata ki huta haka kuma, an gode Allah ya shi albarka, munji daɗin yanda kika karrama mu wallahi kin mana kamar na ki".
Tana murmushi tace,"To ai dukka É—aya ne Mama, ku É—in nawa ne nima ku É—auke ni taku tunda har zama ya haÉ—ani da Æ´arku".
Dariya ta suɓuce min saboda hausartata, ban da ɗazu da aka haɗamu ana mana nasihar nan ni ban taɓa jin tayi hausa ba, to ɗazun don ina cikin zafin kishi ne shiyasa ban ji gwarancin da kyau ba, ashe haka ta iya kwaɓa hausa, kuma ba wai kwaɓar ba ne, hausar akwaita a bakinta yanayin fitar maganar ne abin dariya.
Ita ta dube ni tace,"Me kina wa dariya?".
Ta faɗa da turanci sai na ce,"Ai da hausa za ki faɗa Madam". Ta kawo min duka tana cewa,"Ƴar wulaƙanci, zan zo in fiki iya hausan ne ai".
Gwaggo tace,"Rabu da wannan ƙanwar taki, mu dai don Allah ki huta haka kin ji ƴata, hidiman yay yawa".
Tace,"Mama waye zai gajiya da yiwa manyansa hidima, idan kana son ganin daidai ai sai ka kyautatawa iyaye, na ɗauke ku iyayena ina kwaɗayin adu'anku da albarkanku, ba zan gajiya da biya muku buƙatunku ba har ku tafi, ko wannan yarinyar ba zan bari ta ƙwacen lada na one second ba, komai ni zan ke yi muku".
Naji daÉ—i sosai da yanda ta mutunta min Æ´an uwa. Sai da zata fita ne take ce min,"Sisi na haÉ—e mana namu gaba É—aya a dining ko É—aki za ki tafi muku da shi?".
Na ce,"ki yi mana yanda kika ga ya dace".
"Ah ah ni dai ki faÉ—a don Allah".
A hankali cikin wani yanayi nace,"To ki haÉ—a mana, gani nan fitowa".
Tana fita baki ya É—auka da nayi dacen kishiya. Na so naci abincin a wurinsu sai ga Foridat ta shigo tace,"Momi Maama tace ki fito mu ci abinci".
Na tashi muka fita tare da ita ina riƙe da hannunta, ina tambayanta ba su je school ba tace min ai suna holiday.
Dukkanmu kuwa muka zauna a dining har da Safiyya da yaran, Kudrat na mitan ni da Salim sai mun haÉ—a har na safe da bamu ci ba, ba zamu bar mata abinci ba, ita tayi girki ba Kuku ba, idan ba haka ba kuwa É—umamensa zata mana da daddare.
Ina dariya na ce,"Ni dai miƙo min plate ɗina, ke dai tunda kin dafa Allah yay miki albarka".
A wanda ta zuba min Safiyya ta jaye gabanta, sai wani ta zubo ta miƙo min, haka muka ci abincinmu cikin raha, muna ta hirarrakinmu shi yana faman danna wayarsa, Kudrat na tsokanar Safiyya akan ta zauna mana sai wani lokaci ta tafi Safiyya ta hau bala'in mun rainata, saboda mun mayar da ita bata da miji shine amu mata wannan zancen, haka tayi ta bambami ni da Kudrat dai na ta mata dariya. Na ke cewa Kudrat,"Kema ashe wannan ƴar bata barki ba". Tace,"Idan Sofiyya na masifa to ina yi mata shiru ne, idan ta ise ni sai in kunna wayana in ware kiɗa n abarta da halinta".
Cikin nishaɗin da kowannemu yake Sofiyya tace da Salim,"Brother ni ba zan ƙara yini a gidanka ba ka sallameni kafin matanka su saka min ciwon kai".
Yana murmushi ya tashi ya barmu anan. Komawata É—aki ne yake faÉ—a min su Umman Batula a jirgi za su tafi, na ce masa kuÉ—i ai zai yi yawa, sai yace Sir ne yace ba zai yiwu su zo a mota su koma a mota ba, zaman motar babu daÉ—i, tunda akwai hali zasu tafi a jirgin kawai, nayi ta masa godiya kuwa da nuna masa jin daÉ—ina.
Gabanin la'asar muka raka su airpot suka tafi, kamar kar a rabu ni dai har da ƙwallata, Safiyya nata min tsiyarta, shi ɗin ma bata barshi ba sai da ya ranƙwasheta a ka, haƙiƙa nayi kewan su tun ba'ai nisa ba, Gwaggo ce take haihuwa me rana yau ga shi silar arziƙin ƴa za su hau jirgi.
Bayan mun dawo daga rakiyar tasu ne a mota yake min zancen dinner É—in da abokan aikinsa suka shirya mana, yace anan cikin barrack É—in namu za'ai ba a wani waje da nisa ba. Ko da muka koma gidan aje ni yay yace zai je wani waje.
Ni da Kudrat muka zauna ita tayi ta min hira tun ban saki jiki ba har na ware, yaran na gefenmu suna na su wasan, da kanta ta kira min Mamanta ta haɗamu a wayan muka gaisa, itama Mamanta mace me halin mutunci, tana ta ce min daughter ne, muka sa wayan a handsfree ita kuwa dai faɗa ta dinƙa mana har da cewanta idan bamu haɗe kanmu ba sai ta zo har gida tayi mana duka, cikinmu duk babu wanda yafi ƙarfin duka a wurinta.
Sai bayan isha'i ne Salim ya kira Kudrat, yake ce mata mu shirya da ya zo tafiya zamu yi can wajen dinner ɗin, shirinsa ba mai wuya ba ne. Kudrat ce tayi min kwalliya ashe makeup artist ce, nayi shigan white material na gown, nayi kyau sosai a ciki, su kansu yaran cewa suke Momi kin yi kyau. Ita kuwa haka ta dage tana tayi min hoto a iphone15 ɗinta. Sai da muka gama shirinmu muna ta zaman jiransa a falo tukunna ya dawo, ba ƙaramin daɗi yaji ba da yanda ya same mu, don sai da ya kasa ɓoye farin cikinsa, har da ce mana,"Yawwa kunga yanda na sameku ɗin nan tare kuna hira kuna dariya, haka na ke so na sameku ko da yaushe har sanda zan daina numfashi a doron ƙasa".
Ni ce me saurin cewa,"Please ka bar mana zancen mutuwa". Ya murmusa kunci yace,"Mutuwa dole ne". Kudrat tace,"Mun sani ai, yanzu dai jeka shirya".
Shima shigar white suite yayi yay kyau sosai, sai dai muna zuwa can wajen taron suka sa shi sai dai ya cire ya saka uniform ɗin su. Ni dai ƴar kallo na zama a wajen don duk wadanda suka zo mana murna magana suke da yare. Ba wani taron mutane aka yi ba na azo aji a gani, iya ƴan barrack ɗin ne suma kuma manyan cikinsu duk da iyalinsu, ai kuwa naga yanda ake shan barasa kamar lemu haka aka dinga fasa kwalabenta. Na kasa daurewa sai da na taɓo Kudrat na yi mata gulman. tana dariya sosai tace ai kusan duk cikin barrack ɗin mu ne kawai Allah ya zaɓa da gidan wani soja Moses nan ne kawai ba'a shan barasa. Amma ko gidan mutum kaje aka tashi kawo ma ruwa sai an haɗo maka da ita.
Kiɗin da aka saki shi yaja mana lokaci, ban san Salim haka yake ba ai, ya shiga sai rawa suke tiƙa ba ya ko jin kunyar yaransa. bamu baro wajen dinner ɗin ba sai after eleven, kyautukan da suka ba ni har da na kuɗi, har da ƙaton frame da aka mana na hoton mu gaba ɗayan family ɗin, nawa ne aka yi merging akai nasu kuma already dama akwai shi, lokacin Rofi'at na jaririya.
Kafin mu ƙaraso gida yaran duk sun yi bacci a mota, Foridat ce kawai idonta biyu itama don suna buga ludo game ne da Kudrat, Allah sarki babu ruwanta tana kujeran baya ina gaba, ko irin nunawan nan fa sam, dalilin hakan har sai da na tuna ranar da zamu fita da Zahra'u nayi ƙorafin ta shiga gaba Nazifi ya nemi yaci mutuncina, gaskiya samun irin mata kamar Kudrat a wannan zamanin sai an tona.