← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 113

Sashe 38

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan abun ba su kaɗai ba hatta Iyam bata ragwantawa ba, yanda ba zata bawa yaran abinci ba haka itama ba zata bata ba sai na daren dai, kira idan Iyam zata yi mata sau dubu miliyan ta amsa mata guda ɗaya tayi mutunci, kuma Iyam bata isa ta sakata aiki ba, kai tsaye zata faɗa mata ɗanki na ke aure ba ke ba, idan ma har ta samu arziƙin ta tanka mata kenan, don tafi gane ma taja mata tsaki ta wuce ta barta.

Yanayin yanda ta ke takunta ba ƙaramin shakkarta suke ba, ita kanta Iyam tsoron Zahra'u take ji ba kaɗan ba kamar wadda ta asirce, gidan kuwa tsakani da Allahnta ya isheta ta gaji da zaman gidan Nazifi, don ko kaɗan Zahra'u bata mutuntata bata ganinta da daraja, magana ma idan zata yi mamta murya a sama kamar da sa'arta take, ga babu damar komawa gida don tun ranar da aka yi sakin Sa'ida Malam ya kira ya faɗa mata cewar kar ta sake ta ƙara ko da zuwar masa gida ne, tunanin dawowar shi kuwa ma kar ta soma a lokacin da sha'awar hakan ya taso mata, sai san da yaga dama yace ta dawo tukunna.

Duk lamarin da ke faruwa babu masaniyar Nazifi tun da ba zaman gidan yake ba, duk da dai ya lura da canjin wasu abubuwan amma sai ya ɗauke ido bai maida hankali akai, hakan ma kuma saboda kar yay magana ne Zahra'u tayi fushi don ko kusa ba ya son yin abin da zai ɓata mata rai a cewarsa ita Uwar Ƴaƴansa ce, ba ta cancanci ɓacin rai a wurinsa ba tunda ta basa abin da ya shekara da shekaru bai samu ba.

Tana kan gado kwance tana bawa Iman nono, gefe ɗaya kuma waya ce a hannunta take dannawa, tayi ƙiba ta ƙara fresh, kaɗan kaɗan take murmushi. aka turo ƙofan ɗakin aka shigo, kasancewar tayi nisa akan danna wayar sai sam bata ji alamun shigowa ba.

Atika ta maƙale daga bakin ƙofa tsoro duk ya cikata, shayin yin magana take yi don ko magana ce suka yi zama tashin hankali ne, tace suna cika mata kunne idan ba Kakarsu ko uban ruƙon su zasu wa magana ba to ita su daina mata magana suna saka mata ciwon kai. Shiyasa ko da yaushe idan suka zo wurinta sai su raɓe a bakin ƙofa tana musu kallo ɗaya za su fice da sauri kafin ta sakko ta faffale yarinya da mari.

"Anty".
Ta kuma kiran sunan a karo na uku tun shigowarta. tana shirin juyawa ta fita sai taga Zahra'un ta miƙe zaune tana gyarawa Iman kwanciyarta. Aje wayarta tayi a gefenta sannan ta ɗaga kai ta kalli Atika tace,"Zo nan".

Yarinyar ta tafi a hankali cikin sanyin jiki gami da bala'in tsoro, tana zuwa Zahra'u ta cafkota tare da É—auke fuskarta da mari, cikin wata gigitacciyar tsawa da ta amsakuwa a É—akin tace,"Don ubanki ban hana ki shigo min É—aki ba, ban ce kome ne ba ku jira ni na fito, uban me zan miki da kika zo kina damuna da kira?".

Cikin rawar jiki Atika da tuni hawaye suka wanke mata fuska saboda zafin mari tace,"Anty kiyi haƙuri don Allah".

Zahra'u ta kama kunnenta ta murɗe sosai har sai da yarinyar ta fashe da kuka. "Durƙusa ƙasa da ubanki, na kira ki kin zo kin min tsaye saboda ba ki da ɗa'a".

"Don Allah kiyi haƙuri ba zan ƙara ba".
"Idan kika kuma shigo min É—aki me zan miki?".
"Ki yi min duka".
"Ba duka zan miki ba kakkarya ki zan yi, me ya kawo ki yanzu?".
"Dama yunwa muke ji, cikina ciwo yake yi".

Ai tana rufe baki ta fara jin saukar duka a jikinta. "Shegiya munafuka masu kashe aure, wato so kike ya dawo yace bana baku abinci ko, ina guntuwan taliyan daren jiya da na baku, ko Kakar taku cinyewa tayi bata rage muku ba?".

Maganar take tana tsutsula mata wayar caja. "Ba magana na ke miki ba, na ba ku abinci ko ban ba ku ba?".

"Kin bamu Anty, mun ci mun ƙoshi kiyi haƙuri don Allah ba zan kuma zuwa na ce miki ina jin yunwa ba, don Allah kiyi haƙuri wayyo Allah na, Anty na daina dama Iyam ce tace na zo na roƙe ki".

"Kina ban haƙuri kina min kuka, to idan kinga na bar dukanki kin rufe min baki, kuma kije kice mata ba zan bayar da abincin ba idan so take ku ci ta fito ta dafa muku, zaman ɗanta na ke yi ba zamanta ba, kin ji me na faɗa miki ko kuwa?".

Ai kuwa babu shiri Atika tasa hannu ta toshe bakinta tana faman susar jiki, da ike da É—an haskenta jijiyar goshinta ta fito tayi raÉ—au, idonta yay jawur duk ga shatin wayar nan ya fito a jikinta.
"Sai na ce ki tashi ki fita sannan za ki tashi, in ci gaba da dukan na ki kenan, shegiya makira me kama da ƴaƴan aljanu, wai yunwa ku ke ji, don uwarki da ta kasa riƙe ki sauran taliyar da na ba ku da safe ubanki ne ya cinye, to wallahi ko za ku mutu cikin gidan nan ba ku isa nayi girki akanku ba sai dan son raina, shima kuma sai naga dama zan ba ku...kin fice min ko sai na tashi na take ki dangin tsiya da jaraba".

Da sauri kuwa ta miƙe har tana kifawa ta ƙwala goshi akan gadon ta fice da gudu. Sai da ta fita ta buɗe baki ta saki kukanta, tana zuwa ɗakin Iyam ta faɗi a ƙasa tana burgima. Yaya wacce ta zo babu jimawa ta miƙe da sauri tana cewa,"Ke lafiyar ki?".

Yarinyar cikin kuka mai ban tausayi take cewa,"Anty ce ta zane ni".

"Duka? Me kika yi mata tayi miki wannan mugun dukan haka? Ji fa yacca fatarki ta farfashe, kutumar bala'i anya Zahra'u ta taki hanyar zama lafiya da mu kuwa".

Yaya ta faÉ—a tana waigawa ta kalli Iyam wadda tayi shiru cikin damuwar abun, tace da ita. "Iyam kin ga fa yacca Zahra'u ta daki yarinyar nan".

Iyam tace,"Uhmm ai ki bari kawai, Zahra'u ta zama abin da ta zama, yanzu bata da kirki sam, gaba É—aya ta sauya daga Zahra'un da kika sani a baya, ni kaina ban isa ba yanda kika san ba uwar mijinta ba, ranar nan ma kusan kawo min hannu tayi saboda na É—aga mata murya na ce ta gyara ko nasa É—ana ya koya mata hankali".

Nan ta kwashe komai take faɗawa Yayan, wacce ɓacin rai yasata cewa,"Ba ta ba ku abinci? Shi kuma Nazifin yana ina?".

Iyam ta haɗa hannaye alamun bata sani ba kafin tace,"To ina na ke ganinsa ma balle na masa bayani, yanzu fa idan ya shigo ya gaida ni da safe shikenan sai wata safiyar, dawowarsa ma bana sani don ba ya shigowa yace min ya dawo, idan na aika yara su kira shi sai dai yay ta cewa gashi nan ga shi, ita kuma.ta ƙware a makirci duk wannan iya shegen da take yi a gabansa bata yi mana, ke idan ya wuni a gidan ma sai tayi tamkar zata cinye ni".

Yaya ta waiga ta kalli ƴarta Rumana da ke kwance kan gadon Iyam ta dafe ciki, idonta a rumtse tana cije fuska. miƙewa tayi ta fita a ɗakin Iyam na ta kiranta akan ta dawo ta dawo, bene ta nufa sai ga Zahra'u na sakkowa.

"Ke ashe ba ki da mutunci, ba ƴar arziƙi ba ce, saboda ba ki darajarta uwarki shine za ki dinga wulaƙanta tamu uwar, kuma tsabar ba ki da imani har kike bar mana uwa da yara da yunwa, so kike ciwon yunwa ya kama su, ko ke kika kawo abincin da har kike da ikon hana su, banza mara mutunci".
Tayi maganar cikin faÉ—a sosai.

Zahra'u tayi mata duba na rashin mutunci tace,"Kin san wani abu? Na ɗaga miki ƙafa iyaka yau amma ko don gaba ki kiyaye ɗaga min murya ko kuma ki kwantata lamari da mahaifiyata, sannan kar ki ƙara zagina ni ba banza ba ce, idan kika yi kuskuren hakan za ki gane banbancin aya da tsakuwa. Sannan da kike maganar na wulaƙanta muku uwa ta dai wulaƙanta kanta, ban da wulaƙanta kai da aurenki da gidanki, mijinki da ransa da lafiyarsa ki kwaso ƙafafu ki taho ki tare a gidan ɗa...abinci kuma ba su suka aje ni ba, don haka girki zan yi shi me kawai na bawa wanda ya aje ni a gidan, idan sun ga basu iyawa su tattara su koma gidan ubansu tunda su ba shegu ba ne, idan kuma shegu ku ka haifa sai naji bayani don haka kawai ba za ku ɗebi ƴaƴa ku lalaƙa masa ba, ke koma shegun ne a yau ki tattara garanku ki wuce da su domin ban shirya ruƙon ɗan kowa ba, aikin wofi kawai ba ki da aiki ke kenan kina kan hanyar gidan ƙani sai jace wata tsohuwar bazawara".

Hannu Yaya ta kawo zata mareta aikuwa Zahra'u tayi saurin riƙeta tana yin wurgi da hannun nata, ta ɗaga yatsa tana nunata da cewa. "Ko wannan tsohuwar ta gefenki bata isa ta ɗaga hannu ta mareni ba bare ke karan kaɗa miya Yayar miji".
__________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar

[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR20FT5*
Nazifi na isowa gida ya tarar da Yaran Yaya har su shida, Maza huÉ—u mata biyu wai sun zo ramawa uwarsu dukan da aka mata. A falo ya tarar da su sun kafa sun tsare a bakin matakalar bene, Maimu da Zuwaira sai danna uwar ashariya suke me muni suna faÉ—in idan Zahra'u ta cika Æ´ar tasha ta sakko taga idan basu nakastata ba yau. Yau sai sun ga wanda ya tsaya mata ba kaki ba ko ubanta ne shugaban sojojin Najeriya sai sun mata lahani kuma sun zauna lafiya.
Chapter 38 · 0% Book details