← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 113

Sashe 29

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai yayi wadda ta bayyana haƙoransa dukka a waje, dariyar da sautinta yay min mugun daɗi, ya daɗa rungume ni yana cewa,"Sai ki ce masa me idan kika je?".

"Na ce mijina da ka aika a jirgi can wani waje na zo ka bani abina mu tafi, don na fiku buƙatarsa".

Na faɗi hakan ina murmushi ina kai hannu na taɓa sumar kansa, fuskansa ya shiga gogawa da nawa muka yi shiru ni da shi sai fitar numfashinmu kawai da kake ji. Da wani kasalalliyan muryasa yake ce min,"Myyy wannan Ƙamshin na ki, ko naje na faɗawa Maa a fasa taron mu wuce kawai? Ni ba zan iya ƙara jiran lokaci ba".

Lumsassun idanuna na buɗe ina kallonsa, sai dai ni kaina a yanda na ke jina jikinsa ko maganan ba zan iya ba, ni fa gaba ɗaya a yacca na ke jin soyayyarsa da feelings ɗinsa tamkar ban taɓa sanin komai ba a game da soyayya da aure. shi yay ƙarfin halin da ya raba jikinmu yana sauka akan gadon yace,"Myy ba zan yarda ki ƙara kwana ba, zan faɗa musu yau zamu wuce kin ji".

Knooding kaina kawai na masa, ya fita yana faman shafa kansa, na bi bayansa da ido har lokacin ina jin rungumar da yay min wadda naji kamar muna manne ne still.
Babu jimawa sai ga shi ya dawo da tray na abinci, ya zauna yana cewa da ni na sakko, na dube shi na ce,"Wai kai Salim baka jin nauyin mutanen da ke kallonka ne?".

Shiru yay min sai da ya gama zuba faten doya kana ya dube ni yace,"Kina cin Teba?". GyaÉ—a masa kai na yi nace,"Jiya da aka kawo ya bani sha'awa".
"Oya to sakko".

Na zamo akan gadon yace alalle sai dai na zauna saman cinyarsa, naƙi babu yanda bai da ni ba, yace ya ɗaga min ƙafa ne kawai saboda ba gidanmu ba ne, ina masa dariya na kai hannu zan fara ci ya riƙe hannun nawa, da kansa ya ke bani na tambaye shi miyan menene yace min sunanta Ogbono soup, yana sonta sosai na dage na iya zan mallake shi da ita.
Sai da ya tabbatar na ƙoshi kafin ya bar ɗakin har yana zolayana,"Da ga cin teba sau ɗaya har kin zama ƙatuwa".

Na ce masa ko dai daga ci har gari ya tsotse ni. Yay dariya yana ƙwafa wadda na san ma'arta.
Karfe biyu wata budurwa ta shigo ɗakin sa'ilin muna magana da Safiyya, wadda ke ta bani tips na kula da miji, tana ce min ko da naji ana matan ƙabila na ƙwace miji ba da asiri ba ne ba kuma makirci ba ne, kawai tsantsan iya kula da buƙatunsa ne da iya tattalinsa su mayar da shi kamar jariri, babu batun kuma an girma an aje ƴaƴa shikenan batun soyayya ya tashi, riƙe abinsu suke da ladabi da biyayya jin kai duk a aje a gefe ayi ta gurzar lamura, har tana faɗin banda dai aure rubutaccen al'amari ne da ita dai bata ga me zai sa Salim ya ƙara aure ba, domin Kudrat kat ce wajen sanin zamantakewar aure, naji haushin maganar ma Safiyya har zuciyata na ɗarsa min ko kishi take taya Kudrat ɗin, to nima dai za su ga salon nawa mallakar mijin ne babu boka babu Malam.

Budurwan da ta shigo tace Maa ta turota ta shirya amarya, lokacin bamu jima da gama cin wani abincin ba, duk da cikina a cike yake da wanda Salim ya bani, to saboda kar Hajjo ta tsare ni da tambayan inda na ci na ƙoshi dole haka nasa hannu, ni kam har na gaji da ganin abinci ma.
Duk wanda muka zo tare sai da aka basa kayan shigan partyn ya saka, ni kuwa ban san ta yanda zan faɗa muku haɗuwar da nayi cikin shigar da aka min ba, Safiyya ta ƙwala wani ihu tana tafi da tsalle tana cewa,"Ke kam ai zam igbo ɗin, wallah wanda bai san ki ba zai rantse ba bahaushiya ba ce". shigan blue akan min ni kai na da na kalla madubi sai da naji na burge kaina, ku kuwa dama sai dai na barku da haskowa idanunku kawai.

Lokacin da aka fito da ni Mommi ta riƙe ni ta tsayar da ni gefen Salim, wanda kaɗan ya rage ban sume ba saboda yacca ya tafi da ni a kyan da yay cikin shigarsu. Ga wata sanda ta ƙarfe ta ya riƙe, kai ba ka ce sojana ba, fuskarsa sai annuri take fiddawa. Ranƙwafo kansa yay saitin kunne na yana cewa,"Baby kyan da kika yi kaman a sace a gudu, to Allah ya so ma ni zan ɗauke kayata ba kuma me hana ni, nan gani nan bari ɗumamen maya".

Na waro ido ina ce masa,"Har da su karin magana ka iya, lallai ne Onochie".

Ƙuguna ya matsa yana murmushi. Tab lallai arziƙi na inda yake, haka talauci ma na can inda ake kukan babu, ashe duk girman compaound ɗin nan akwai inda ya fishi, ta can ciki wani wawakeken fili ne anan suke shagulan bikinsu babu ruwansu da kama event center, an ƙawata wajen ka rantse wani mashahurin event center ɗin aka kama, plate na abinci ne kawai ke haske maka ido da drinks. ni dai kaina na ƙasa amma ba ƙarya kowa a wurin abun kyau da burgewa ne, Musamma yaransa da aka yi musu shiga iri ɗaya suna zaune a gabanmu kan kujeran da muka zauna, suma kamar ni hannayensu duk da ƙananan mafitai me gashi.

Hoto kawai ake ta É—asa mana, sai naji ina ma acan gida ne nayi hoto da mahaifiyata da Æ´an uwana, ba shakka Yaya Imam ma zai kyau cikin irin shigar nan, sai dai na san ko me za'a masa ba zai saka murjani a wuya ba. Taro yay taro, duk ba wasu mutane ne da aka yi gayya ba iya Family ne kawai, Safiyya ce ta gabatar da ni ta faÉ—i tarihina tun daga haihuwa har kan matakin aikina, Kudrat ma ta zo masha Allah wallahi da na ganta sai da na raina kaina, ashe kyan da na gani jikin Æ´aÆ´anta da wanda ake faÉ—a min ba komai ba ne.

Nayi ta mamakin me ya kai salim ƙara aure shi kuwa yana da wanga zuƙeƙiyar mata. Babu ruwanta sakaraftunta kawai takeyi cikin farin ciki kamar ba wadda miji kewa kishiya ba, ni da ka aka kawo ma na fita kishin miji, har da su zuwa tayi mana liƙi, haka ta zo tana ta yaƙe min haƙora hoto kuwa mun yi da ita yafi a ƙirga, tun ban sakin jikina da fuska da ita sai da na rissina, kowa na ta rawa ni dai na kasa saboda kunya, Salim kuwa ya zage yana ta abarsa shi da ƴaƴansa da matarsa, Kudrat ɗin ce ma ta kamo hannuna ta shigo da ni tsakiyar su tana rawar tana aikin watsa mana kuɗi dukkan mu.

Ba'a watse a wajen ba sai ƙarfe bakwai Granny ya aiko a kashe kiɗa aje ayi ibada, sai lokacin naga Salim ya murmusa, don tunda ya gama rawarsa yaci magani sai zungurana yake wai ana ta ɓata lokaci salon aja masa ƙin tafiya da ni yau, ni dai dariya kawai nake ƙasa ƙasa, kunya na ke ji na biye masa yanda idon kowa ke a kanmu.
Fakar ido yay ya fige ni muka shige wani ɓangare, yace min da na koma ciki kawai in cire wannan kayan hayaniyar na shiryo na fito, nace masa ni kam ban iya rashin kunya ba, sai ya matse bakina na samu dai na zilla masa ganin abinda yake ƙoƙarin aikatawa.

Ai kuwa ana can ana nemana duk sai naji kunya, ina jin wata mata ina ga inlaw ce a gidan tana faÉ—in a bawa Onochie matarsa su wuce yau, Kudrat ma ta hango ni ta taho da hanzarinta tana ce min a yau fa zamu tafi gaskiya ba za'a kuma barinta kwana a gida ita É—aya ba tunda dai mijina ba barinta kwana anan zai yi ba.

Nace da ita,"Tafiya da wannan daren?".
Ranta fess tace,"Mene dare? Shi bai faÉ—a miki babu nisa ba, 2hours ne fa kawai zuwan".

A hankali na ce mata,"Da dai mu bari sai goben ma tafi da safe".
Hannuna kawai ta kama muka yi ciki sai É—akin Maa. Ita ta kira shi a waya tana faÉ—a masa wai ya shigo ya shirya ni mu tafi, ni duk sai ta bani mamaki sosai, kamar ba kishiya aka mata ba, to ko ba auren soyayya suka yi ba ne? Ko kuwa dai dama matan arewa ne kawai ma su kishi?. shi kuwa sai ce mata yayi to idan ni ban son tafiyan ta kwaso masa yaransa su tafi yana jiransu a waje idan ya so gobe ni na kai musu kaina.

Yanda yay maganar sai da nayi dariya don a fusace yayi ta. Can ɗakin da muka sauka na koma, Umman su Safiyya ita ta shirya ni, tayi min shigarmu ta hausawa kamar dai jiya swizz less ne na saka blue sai faran lafaya, haƙƙun nayi kyau ko a faɗa ko kar a faɗa, duk wanda yace ban ba to ɗan hassadata ne. Yo idan ka ganni ma ina zaka taɓa cewa Sa'ida ta taɓa aure? Ina zaka taɓa cewa ba tsaleliyar budurwa ba ce a gabanka? Rantsuwa kuwa idan za'a kwana ana maka da labarin irin rayuwar da nayi a baya ba zaka taɓa yarda ba, to ina ma wani alama da zai nuna na fuskanci ƙabulace me raɗaɗi a rayuwata, canjin rayuwar fa ba ƙaramin canji na samu ba sai dai godiya ga me sama kawai, shiyasa aka ce haƙuri ba yawa, me haƙuri ba ya tawaya, haka kuma me haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa, ga matakin nasarar da haƙurin ya kawo ni nan.
Chapter 29 · 0% Book details