← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 113

Sashe 6

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To a rayuwar gidan aurenmu babu abin da zance da ubangiji sai godiya gare shi da ya mallaka min Yaya Nazifi matsayin mijina, domin kuwa nayi dacen samun miji na gari da ya san darajar mace, wata iriyar rayuwa muke shimfiɗawa me cike da zallar soyayya da ba zamu taɓa mancewa da ita ba a tarihin rayuwarmu, Yanda Yaya yake ji da ni tamkar zai haɗiye ni da soyayyarsa, zazzafar ƙauna yake nuna min ta kowanne ɓangare, bai taɓa bari na koka ba, motsi kaɗan ya tambaye ni me nake so, me zai yi min, duk wani abu da ya san ina so sai yay ƙoƙarin samar min shi, haka idan ya fita ya tashi dawowa da ɗan namansa ko kifi ko kayan marmari, a gida ma mu girki me kyau da rai da lafiya ko gidan wasu masu kuɗin sai haka, haka idan ya fita aiki shine baro shago da rana ya zo ya duba ni sannan ya koma, kullum faɗamin yake son da yake min baida adadi, domin samun macen aure ta gari irina da wuyar samu, don haka yay min alƙawarin mutuwa ce kawai zata rabamu, kuma yay min alƙwarin zai inganta rayuwata da dukkan ƙarfinsa da ikonsa.

Ta ɓangaren ƴan uwansa ma haka, nuna min so suke tamkar zasu haɗiye ni, komai suka samo a rakito akawo min, abinci wannan sai naga damar girkawa don da wuri ake gama abinci acan a kawo min, kuma da yake bamu da nisa sosai kusan kullum ina gidan don Iyam bata da wani batu a bakinta sai na Sa'idata, Nazifi turo Sa'ida ta zauna kusa da ni idan ka dawo daga aiki sai ka zo ku tafi tare. Irin ƙaunar da sirikata ke nuna min sai nake jin kamar mahaifiyata, komai Iyam taci sai ta bani, duk wani sirri ko shawara ko damuwarta ni ɗin nan dai nice, sai ta faɗa min ma abin da ya shafeta bata faɗawa ɗanta ba, har shima yake tsokana da cewa gaskiya zai yi ƙarata wurin alƙali na ƙwace masa mahaifiya.

To haka ma babbar Yayarsu Yaya Maijidda, matar nan yanda ta ɗauke ni ko yanda ta ɗauki Nazifi da suke ciki ɗaya albarka, itama komai matar ƙaninta Ƙarami, har facalolina suka fara jin haushin hakan, bini bini ta kira waya ta tambaya ya muke, ban da wata matsala ko, kuma Ƙarami ba ya min komai ko? Idan yana min wani abu kar na ɓoye na kira na faɗa mata. To ni kuwa ƙarar me zan kai mata akan mijin da ya tattara dukkan soyayyarsa da ƙaunarsa, kulawarsa da hidimtarwasa ya ɗora akaina? Ai ni babu abin da zance da Nazifi a rayuwa.

Kamar yanda Abbaa ya faɗa min shekara guda da aurena ya canja min kayan ɗaki sababbi masu kyau, kuma ba'a kwashe tsofaffin ba yace duk na haɗa, nayi murna sosai da farin ciki tare da adu'a wa mahaifina. Dama ɗakuna biyu ne don haka sai na mayar da tsofaffin ƙaramin ɗakin, da yake kujera ɗaya ce dama duk sai ya ɗauke ɗakin bai cunkushe ba, wancan ɗakin kuma da yafi girma can na bar sababbin kujeruna har uku na bar shi a matsayin ɗakin Hubbi, don har labulaye Abbaa ya canja min, dama waɗancan wasu ajiyayyu ne na Ummani da bata saka su aka fito min da su.

Jarabawar waec da neco ɗinmu ta fito a lokacin kuma sai ban ci ba duk biyun, a waec bani da english da biology, neco kuma bani da english da maths, haka na sha kukana Abbaa yay ta lallashina yace in bari idan za'a kuma yin wata sai na ƙara zanawa, to ita kuma lokacin da ya zo sai ya zamana babu kuɗi har aka rufe biya, amma haka Abbaa yay ta ban haƙuri da cewa in jira lokaci Yashaik yace masa ana zana wata da ake biyan kuɗi masu yawa a ci, to idan za'a yi indai da kuɗi zai biya min na kwantar da hankalina.

Cikin shekaru biyu da aurenmu al'amura suka fara taɓarɓarewa Hubbi, rana ɗaya megidansa yace ya saida shagonsa, ya sallami su Hubbi da dubu tamanin tamanin yana basu haƙuri. Wannan rasa shago da Hubbi yay shine mafarin ƙalubalen da muka fara fuskanta, kuɗin sallamar da aka ba shi da su ya samu ya buɗe tireda a ƙofar gida yake siyar da provision.

Sauran kuɗin da yay saura kuma ya siyo kayan abinci na ɗan lokaci ya ajiye, sai ƴar dubu huɗu da ya bani yace na ɓoye ko da wata buƙatar ta ujila zata ta so. To yau da gobe kayan abinci duk suka ƙare, tireda kuma sai dai ace an gode Allah domin tuni itama kayan ciki suka ƙare kuma ya rasa ta ina kuɗi suka tafi, abun dai ba'a cewa komai lokaci guda komai ya tsaya masa cak.

Kullum zai fita amma haka zai je ya dawo babu wani ƙwarin jiki, ya buga duk ta inda zai buga ya rasa wata sana'a da zai kama, sai dai ya fita haka yaje wajen su Yayan Shago inda suke leburanci ya zauna wajensu ya ɗan taya su wani abun, su kuma a kuɗin sallamar da ake basu a ciki suke sammasa, to ɗan kuɗin ba wani me yawa ba ne idan yazo da su basa kaiwa ko'ina, iyaka abin da za'aci na lokaci ɗaya ne kawai ake samu, to don ma Allah yasa babu yara da damuwar da zamu shiga sai tafi haka.

Rayuwa taci gaba da tafiya har aka zo gaɓar da kullum sai dai ya fita haka ya dawo babu komai, ɗan na garin kwakin ma da ake siyowa aci yanzu ba ya samuwa, ƙanzon da muka shanya duk ya ƙare, muka koma sai dai wata rana muci watarana kuma haka zamu yini mu kwana da yunwa, ruwa kawai muke sha. Wannan hali da muka shiga na tsananin babu ita tasa na koma yin waya gida ina yin dabara na ce ni abincin gida nake so ci idan anyi a aiko min da shi, har aka fara zargin ko ciki ne da ni, to fa da wannan ne ma muke samu muci rana da dare, dama na safe ba'a batunsa, wataran kuma idan na tashi sai in je can gidansu na yini to acan zanci na rana idan dare yay kuma a zubo mana mu taho da shi, kuma duk wannan hali da muke ciki babu wanda ya sani domin kuwa muna da wadatar zuciyar da babu wanda zai ganmu ko ya zo gidan ya gane halin da muke ciki, fes fes zaka ganmu cikin annuri da walwala, gidanmu ɗasɗas babu wani alamar tsanani.

To abu fa yaci tura babu wani sauƙi sai tsanani, talauci yay mana ƙatutu, ko lalura muke sai dai mu roƙi Allah ya bamu lafiya magani kau biyar ɗin siya ma babu. Da haka dai na bawa Hubbi shawarar ko in nemi sana'a ko da aikatau ne nake yi, yace bai amince ba sam, zai ci gaba da jajircewa wajen neman abun yi.
Kullum cikin hawayen tausayin halin da muke ciki na ke, ga mijina me tsananin tawakkali wanda ko bacci cikakke baya iya yi haka yake kwana yana gayawa Allah ya kawo masa É—auki da mafita. Watarana kawai na yanke shawara ni É—aya domin ba zai yiwu muci gaba da zama a haka ba, ba tare da sanin Hubbi ba na nemo dillaliya ta siya kayan É—aya É—akina da sabuwar kujerata guda É—aya.

Hubbi ya dawo da daddare na damƙa masa naira dubu talatin a hannunsa. Ya kalle ni yana tambayar Habibity ina kika samo damin kuɗi haka sannan ne nake sanar da shi yanda aka yi. Tsabar farin ciki har da ƙwallarsa, ya rungume ni jikinsa yana saka min albarka da godiya.
A washegari kuwa yaje kasuwa ya siyo buhun garin masara da shinkafar hausa, yasa kuma aka yiwa tiredarsa Æ´an gyare gyare, ya fara aunar da garin masara da shinkafa dama babu irin masu awo a cikin layin sai anje titi, ai ko kan kace me wannan Æ´an unguwa an ganewa wajen, ni kuma cikin gida sai na ke sana'ar wanki da guga, haka zanyi wanki me uban yawa, idan dare yayi Hubbi ya tayani guga, kuma É—an abin da za'a samu bai kai ya kawo ba amma a hakan dai babu laifi, haka muka haÉ—u da taimakon juna muna rufawa kanmu asiri.

Muna cikin wannan rayuwar dai Allah ya kuma kawo mana jarabawa, shima awon da Hubbi ke yi aka zo aka sace tiredar, rana ta farko da na taɓa ganin hawayen mijina wanda yay matuƙar ɗaga hankalina ranar har ban yi bacci ba. Tun daga nan kuma Hubbi ya sare yace shi ya gaji, ta kai ta kawo idan ma ya fita da anga ya dosa waje za'a fara ƙusƙus ana maula ta kawo shi, masu shago kuwa duk sun sauya masa fuska saboda basa son ba shi bashin kayan abinci don ba'a samun damar biya da wuri. Duk ƙarfin hali irin na Hubbi haka zuciyarsa ta mutu yace kawai ubangiji yay ikonsa akanmu, har ta kai ga ya kusa yin saɓo sai da na rufe masa baki.

Tsaka da wannan tashin hankalin da muke ciki na kwashi kujeruna duka naje na siyar, kayan kicin É—ina ma haka duk na tattara masu kyan na siyar da sitturuna masu kyau, don har ga Allah na gaji da ganin mijina na zaman jugum yana hawaye, na gaji kuma da jin yana fita mutane na gulmarsa suna gudunsa.
Don haka kuɗin da na haɗa dubu arba'in da biyar na kaiwa maƙocinmu na ce don Allah ya nema mana aron adaidaita sahu ga wani abu zamu rage, a hankali kuma sai a dinƙa cikawa, amma don Allah kar ya bari mijina ya san nice na zo da zancen kawai yace shine ya taimaka masa.

Mutumin da ke yana da mutunci a washe gari kuwa sai ga shi ya kira Hubbi, suka je can wurin karɓar babur ɗin aka saka hannu da komai tare da yarjejeniyar cikin shekara guda zai gama biyan kuɗin babur ya zama na shi, ya dawo yana ta farin ciki yana shaida min yanda akai, ni dai ko kusa ban nuna masa ma ina da sa hannu a lamarin ba, haka muka kwana cikin farin ciki da adu'ar Allah sa zuwan ƙarshen komai kenan.
Chapter 6 · 0% Book details