← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 113

Sashe 32

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ɗazu wani ya tashi ya buƙaci shigowar Insifecta Usman. Shima bayan ya zo Barr ta kalle shi ta ce,"Insifecta lokacin da kuka isa gidan Alhaji Nazifi Mai Kalwa, wanne makami ku ka samu da Sa'ida tayi amfani da shi ta hanyar kashe ƴar kishiyarta?".

"Babu".
"Kace Babu? Kenan da me ta kasheta?".

Numfashi ya sauke yace,"To a iyaka duk binciken da muka yi gaskiya babu wani shaida da ke nuni da cewa kashe yarinyar aka yi, don ko hoton sawun hannaye duk mun ɗauka na inda ita Sa'ida ta tattaɓa, kuma binciken likitoci ma babu rahoton nuna cewa kashe yarinyar aka yi".

"Ok kenan har likita ma yay nasa bincike akan rasuwar?".
"Ehh ƙwarai kuwa, likitoci har uku ma".
"Da kyau, kun zo da rahoton?".
"Ehh mun zo da shi".
"Ko zaka iya bamu?".

File ɗin da ke hannunsa ya bata, ta karɓa tana faɗin,"Na gode, kana iya komawa". Daga haka ta miƙa file ɗin wurin Alƙali.

Alƙali yay rubuce rubucesa, sannan Barr Zaliha ta ce da shi,"Idan mai shari'a ya bani dama ina so na gayyato likitan da ya duba yarinyar domin yayi mana bayani yadda zamu fahimta".

Alƙali ya sake yin rubutu yace,"An ba ki dama".

Aka nemi ganin likita ya ƙaraso ya tsaya, ta ƙarasa kusa da shi tace,"Dr ko zaka iya faɗa mana sunan ka?".

"Sunana Dr Bashir Adam ƙwararre a fannin likitan ƙananun yara."

Ta jijjiga kai tace,"Me ya kawo ka zaman wannan kotun?".

"Domin bayar da rahoto akan binciken lafiyar wacce ta rasu".

"Wa ya buƙaci da kayi binciken?".
"Insifecta Usman".

"To ko zaka iya mana bayanin rahoton rasuwar Salma Nazifi Mai Kalwa wato Noor, jaririya me kimanin kwana talatin da Æ´an kai, wacce ka tabbatar da hukumar Æ´an sanda sun baka damar yin bincike akanta?".

"Ehh zan iya domin da kaina na dubata lokacin da Insifecta Usman ya buƙaci na tabbatar musu da ta rasu ko tana raye".

Barr tace,"A yayin da kake dubata akwai shatin shaƙa ko guba a jininta wanda zai tabbatar mana da kasheta akayi?".

Likita ya girgiza kai yace,"Babu ko ɗaya a ciki, domin kuwa ta silar ciwo ta rasu ba silar guba ko shaƙa ba".

Barr Zaliha tace,"Ciwo dai?".
"Ƙwarai ciwo".
"To wanne irin ciwo kenan, ko zaka iya yi mana bayaninsa da kuma adadin kwanakin da ya É—auka a jikinta".

"Jaundice shi ne ciwon da ke tare da yarinyar, wanda kuma ya kai kimanin kwana talatin da biyar a jikinta, shaidar cewa da shi aka haifeta, kuma symptom ɗinsa a bayyana yake ba'a ɓoye ba, za'a samu fatar jariri tayi yelo da idanuwansa, yelo sosai, to shi wannan ciwo dama idan ya zama chronic har yay yawa ya hau ka shi ne yake leading to death, so yawanci iyaye idan suka haifi yaro a haka tunaninsu ba ya basu ga cewar ya kamata suga likita, sai su tafi akan an haifi yaro da rana ko shawara, in da kuma sai su tsaya a iya maganin gida, wasu iyayenma suna ganin hakan amma sai suyi ignoring su zuba ido har azo a rasa jariri".

Barr tace,"Wato Dr idan na fahimceka wannan ciwon da kayi mana bayani shi ne silar barinta duniya ba dalilin hannu ko wani abu da aka bata ba?".

Ya jijjiga kai cikin tabbatarwa yace,"Ƙwarai da gaske shi ne silar rasuwarta, bayan shi gaskiya babu wani abu".

Tayi murmushi tace,"Na gode likita, zaka iya komawa ka zauna".

Ya juya ya koma itama kuma ta kalli alƙali tace,"Ya mai shari'a ina so ayi duba ga bayanan Likita da bayanai akan ciwon da ya kashe yarinyar a tabbatarwa da jama'a Sa'ida ba ita ta kashe yarinyar ba, Allah ya nuna a bayanta zata rasu ne amma bawai dan ta kashe ta ba. Haka ma idan aka ƙara duba bayanan mahaifiyar yarinya, Da wannan na ke so kotu tayi watsi da wannan ƙara domin babu komai a cikinta sai zallar ƙazafi da son cutar da Sa'ida, sannan ina nemawa Sa'ida hakkinta akan sharrin da akayi mata. Na gode".
Ta faÉ—a tana komawa ta zauna.

Alƙali yayi rubutu kafin yace,"Shin lauyan da yake ƙara ko yana da abin fad'a?".

Barr Mu'azzam ya tashi yace,"Babu ya mai shari'a".

Mai shari'a yayi rubutu na wani lokaci, kotun tayi shiru ana jiran hukunci kafin ya ɗago yace,"Duba da rashin hujja gamsashshiya da ba'a samu daga ɓangaren masu ƙara ba, da kuma bayanai da hukumar ƴan sanda ta bayar, da rahoton likita da ya bayar zai tabbatar mana da abin da ake zargin Sa'ida da shi bata aikata ba".

Ya sake yin shiru yana rubutu kafin ya sake cewa,"Wannan Kotu mai adalci ta wanke Sa'ida Salman Madobi daga zarginta da ake yi akan laifin kisa, bata da hannu kuma bata aikata ba, duk wasu bayanai da hujjoji sun tabbatar da hakan. Sannan kotu zata ci tarar Zahra'u Abdullahi da Nazifi Bala Mai Kalwa akan ɓatawa wadda suke ƙara lokaci, da wahalarwa, da kuma ɓata mata suna da tayi, ta ɓatawa shari'a lokaci, bisa hakan kotu taci tararsu naira miliyan ɗaya da rabi. Sannan Kotu na gargaɗin Nazifi Bala Mai Kalwa da Zahra'u Abdullahi akan ko dan gaba yana da kyau su san gaban alƙali ba wajan wasan yara bane, su samu hujja mai ƙarfi kafin su shigar da ƙara in ba haka ba nan gaba kotu zata hukunta su".

Da haka alƙali ya buga teburi ko ya tashi da faɗin koootuuu.
Ahalina da dukkan magoya bayana muryoyinsu da ke fitar da kalmar Alhamdulillah ita ta karaɗe cikin kotun gaba ɗaya. Ta ɓangarena kuwa zan iya cewa babu wani abu da naji a tattare da ni na farin ciki ko na murna, haka babu akasinsa domin kuwa cikin kwanakin nan da nayi a cel jina na ke tamkar wadda babu zuciya a ƙirjinta.

Safiyya ta zo da saurinta ta rungume ni tana kukan farin ciki, Ummani ma haka, ina kallon yanda mahaifina ke share ƙwalla wadda na san bata komai ba ce illa tsananin farin ciki da murna. Yaya Imam da Yashaik na can gefe suna tattaunawa da wani insifecta.
A wannan lokacin ƙyam na ke a tsaye, ƙwayar idona ta gama wurgawa kan kowa da komai, kafin a hankali ta shiga haska min hoton fuskar Nazifi.

Na sani babu kalma mafi ɗaci da ciwo gami da firgici a rayuwar kowacce ɗiya mace irin kalmar ZAWARCI, to amma a yau nafi buƙata da kwaɗaituwar nayi zaman Zawarci fiye da zaman gidan miji. a yau na tsani kalmar miji, bana son auren, na kuma sha alwashin ni da aure har mutuwa, tabbas a yau ba sai gobe ko jibi ba sai in Nazifi ba ya raye amma sai ya sake ni, sai ya sakeni ko ta wanne hali.
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR16FT5*
Farantin hannuna ya suɓuce ya sauka akan tiles ya bada sautin rikitacciyar ƙara, ƙarar da taja jaririyar da ke kwance razana ta farka daga baccin da take, nan kuwa ta tsanyara uban kuka wanda lokaci ɗaya gidan ya ɗauka da sautin kukanta, kan kace me wannan uwarta ta sakko daga sama, ta bangaje ni daga ƙofar ɗakin Iyam ta faɗa ciki tana ɗora hannu aka da faɗin ta shiga uku.

"Ni Jummai me ya faru da yarinyar nan take tsala uban kuka haka?".

Cikin kuka tana dudduba jikin yarinyar take cewa,"ban san me tayi mata ba Iyam, shikenan ta ƙara kashe min yarinya, na rantse da Allah a wannan karan ba zan yarda ba".

Ai kan ƙiftawar ido sai tsintar Iyam nayi a gabana, tasa hannu ta ɗauke fuskata da mari tana zazzaga ruwan bala'i.
"Wanne irin rashin imani ne danƙare a zuciyarki?, Mayya ɗiyar mayu kin dawo ki kashe kowa kenan, ke ninfa ko da haihuwa kika yi ba ƙaunarki zan yi ba, kuma ko rubuce yake sai na saka Shalele ya rabu da take".

Kamar kar in tanka sai kuma na sauƙaƙa zuciyata, ko ba komai bayani na da daɗi duk da ba amfani zai yi ba, kuma ni rigima da tashin hankali ne ban so, Idona akan uwar da ƴarta na ce,"wallahi tallahi Iyam babu abin da na mata, kawai fa na ajiye miki abinciki ne na zo fita tsautsayi farantin ya suɓuce a hannuna, to ƙarar ita ta firgitata".

Rufe bakina ba wuya Iyam ta ɗau waya ta kira uban yarinyar, da kwakwazo take faɗa masa ai na zo na ƙarasa kashe masa yarinya yay gaggawar zuwa wannan karan kotun ƙoli ce zata raba mu. gabana ya faɗi jin ƙaryayyakin da take gilla masa, ga jaririyar kamar haɗin baki sai ƙara tsanyara kuka take yi kace ɗaukarta nayi na buga da ƙasa, ba'a ɗebi wasu mintuna masu yawa ba sai ga shi ya dawo, lokacin ina tsaye a parlo na kasa zama saboda fargabar abin da zai faru.

Ganinsa a furgice ba ƙaramin razana ni yay ba, kallona ya tsaya yi a fusace sai ga Uwar ta sakko tana jijjiga ƴar itama sai kuka take yi, ya tafi da sauri ya karɓi yarinyar yana duddubata, ita kuma uwar faɗa masa take yi wai asibiti zata kaita saboda kunnenta ya toshe, kuma bata san me aka tusa mata a baki ba dai maƙogoronta ya cushe ko nono ta kasa sha.

Ni dai tsabagen mamakin sharrin daskarewa nayi a tsaye, to wai uban me ma ya dawo da ni gidan?, aikuwa ban yi aune ba naji saukar duka a jikina ta ko'ina, Nazifi ne ya shiga ɗaki ya zaro belt ya ke dukana kamar an aiko shi, garin in ƙwaci kaina in guje masa goshina ya bugu ajikin ƙarfen matakalar bene, tsananin azaba yasa na kurma uban ihu ina kiran sunan Allah. jini ya fara malala, ya koma saka ƙafa yana tattakeni yana faɗin sai ya kashe ni akan lahanta masa yarinya da nayi. ba Nazifi ya ƙyaleni ba sai da ya haɗa min jini da majina, fuskata duk ta kumbura idona ɗaya har bana ganin komai da shi.
Chapter 32 · 0% Book details