← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 113

Sashe 31

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ko aikawa zan yi a taso Yashaik?".
"A'a don Allah mu bar yaran nan su huta haka nan, tun da ni zanje ai ba sai kin damu ba. Kuma dama sun ce yau É—in zasu bayar da ita in sha Allahu".

"To ubangiji Allah yasa, Allah ya amince saboda sirrin la'ila ha'illallahu. ga shi nan ma na saka mata sauran awarar jiya da bamu ci ba naji bata yi yami ba. Don Allah kasa taci abincin kaga tana da ulcer".

"In sha Allahu. Bari na wuce".
"Tom aje lafiya a dawo lafiya, amma idan anyi cinikin lemo zaka ganni na taho".

Kai kawai ya gyaɗa mata ya fita. Kana duban idonsa ka san ido biyu ya kwana, haka kana ganin yanayinsa kaga na me ƙarfin hali, dauriya kawai yake yi, dauriya saboda ƴarsa da iyalansa. Haka yake tafiya da ƙyar, bai jima a bakin titi ba ya samu me napep ɗin da ya ɗauke shi da taimako har ƙofar na'isa a naira ɗari.

Zone 1 shine headquater ɗin dama da case ɗin yake, ko da yaje dakatar da shi aka yi daga waje aka ce ya jira zuwa ƙarfe goma, babu irin roƙon da bai yi musu ba akan su taimaka ko abinci ne su barsa ya bata amma suka ƙi sai karɓa suka yi, sai bayan ya shafe awa guda har da rabi sannan ɗan sandan da ya shiga kai mata abincin ya dawo yana faɗa masa ai ya manta ma anje da ita asibiti babu lafiya tun daren jiya.

Ai jin wannan furuci Abbaa ya nemi yanke jiki ya faɗi, su kuma ƴan sandan babu tausayi bare imani don haka babu wanda yabi ta kansa, da taimakon ubangiji ya samu kansa, tunaninsa ɗaya me ya sami Sa'ida kuma wanne hali take ciki? duk yanda ya so su faɗa masa asibitin da aka kaita suka ƙi, har sai sha biyu na rana lokacin AIG ya shigo, sannan ne insifecta Usman wato Yayan Zahra'u ya kira shi ofishinsa.

Lokacin su Ummani da Yayyun Sa'ida kaf sun zo har da Kaka, sai da aka jira zuwan su Nazifi sannan Insifecta yake shaida musu da cewa an tura case ɗin na su gaba zuwa Fagge Shari'a Court, kuma zasu fara zama a sati na gaba in Allah ya kaimu, saboda haka sai su nemi lauyan da zai tsaya musu. Nazifi yace babu matsala suna da lauya a hannu, su Abbaa dai basu iya cewa komai ba illa ma dukkaninsu tunanin ta in da zasu fara nema lauyan da kuɗaɗen da za'a fitar suke, ga babban tashin hankalinsu an ce basu da damar ganin Sa'ida, Ummani tun tana kuka da hawaye har ma ya daina zuba sai dai ka jita tana fizgar numfashi, Abbaa ma duk ƙarfin halinsa da dauriyarsa sai da ya karaya, Ƴaƴansu ne kawai masu ƙarfin gwiwa da suke tausar su.

Malam mahaifin Nazifi zai yi maganar cewa ko za'a iya basu lauyan da zai tsayawa Sa'idan, zuwan Safiyya ya katse maganar tasa wadda ta zo ita da Antynta da kuma lauya, wacca ta gabatar da kanta wa Insifecta. Ta kuma karɓi bayanai da date ɗin fara zama, daga nan ta buƙaci a kaita wurin Sa'ida nan aka shaida mata cewa tana asibiti, haka aka haɗata da ɗan sanda wanda suka tafi da shi can asibitin.

*23-Nove-2023, Fagge Shari'a Court, Muhammad Murtala Way, 10:30am.*

Kotun bata cika sosai ba iya ƴan uwa ne na jiki wanda suka san da case ɗin sai baƙin fuska ƙalilan wanda sha'awar sauraron shari'a ya saka suka zauna.
Bayan shigowar Alƙali rajistara ya tashi tsaye yace,"A yau juma'a sha bakwai ga watan nuwanban shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, wanda yayi daidai da uku ga watan jumada auwal shekara ta dubu ɗaya da ɗari huɗu da arba'in da biyar A.H. zamu saurari ƙarar Zahra'u Abdullahi wacce take ƙarar kishiyarta akan kashe mata yarinyarta da tayi har lahira".
Ya faɗa yana tattara file ɗin ya miƙawa Alƙali ya karɓa yana dubawa.

Shiru kotun tayi na wani lokaci kafin Alƙali ya kalle su yace,"In lauyoyi masu kariya suna kusa su gabatar da kansu."

Wani dogon namiji baƙi mara tsaho sosai ya miƙe ya ce,"Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Mu'azzam Ibrahim ni ne Lauyan mai ƙara". Ya faɗa yana zama.

Wata Mace doguwa mara jiki ta miƙe itama tace,"Sunana Barr Zaliha Muhammad, ni ce lauyan wacce ake ƙara".
Ta faɗa tana zama itama. Alƙali ya fara rubutu a kan file na wani lokaci kafin ya ɗago yana kallon su.

"Lauyan wanda yake ƙara ko yana da abin faɗa?".
Alƙali ya faɗa yana kallon su.

Miƙewa yayi yace,"Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai alfarma da ta bani dama domin yiwa wacce ake zargi tambayoyi".

"Kotu ta baka dama".
"Na gode ya Mai Shari'a".
Ya faɗa yana fitowa ya ƙarasa inda Sa'ida take tsaye yana kallonta.

"Malama Sa'ida ko za ki iya yiwa kotu bayanin yarinyar da aka rasa wacece a wajan ki?".

Sa'ida ta haɗiye yawu ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce,"Ƴar mijina ce".
Ya kalleta da kyau ya ce,"Ƴar kishiyarki ce kenan ko?".

Sa'ida ta É—aga kai alamun eh. ya girgiza kai ya ce,"Ke ina naki Æ´aÆ´an?".

Tambayar tashi ta motsa zuciyata, na É—ago ido ina kallonsa kafin na ce,"Bani da su".
Ya girgiza kai sannan yace,"Kenan dan ba ki da su shiyasa kika kashe Æ´ar kishiyar ki?".

Da mugun faɗuwar gaba na sake kallonsa jin yana neman ƙara ɗaure ni.
"Ina da ja Ya mai girma mai shari'a!"
Barr Zulaiha ta faɗa tana miƙewa tace,"Bai kamata lauyan mai ƙara ya fara yiwa wacce ake zargi tambaya akan abin da ya shafi rayuwar ta ba. Rashin yara abu ne da ya shafi rayuwarta bai shafi case ɗin da muke magana a nan ba".

Mai shari'a yace,"Barr Mu'azzam a kiyaye".
Yace,"Na gode ya mai shari'a".

Ya kalle ni yaci gaba da cewa,"Ƴar mijinki ƴarki ce Malama Sa'ida amma meyasa kika kashe ta?".
Na kalle shi nace,"Wallahi bani na kashe ta ba".
"To waye kasheta?".

Na share hawayen idanuna na ce,"Kawai ta rasu ne amma bani na kashe ta ba".
"Me ye silar rasuwar tata shi za ki faÉ—a".

A hankali nace,"ban sani ba nima".
Ya sake kallona yace,"Kenan da gaske ne ke kika kashe ta?".

"Wai sau nawa zan maimaita ban kashe ta ba?".
"Ki daina É—aga mana murya".
"To ya ku ke so nayi, iyaka gaskiyata na ke ta faɗa muku amma kun ƙi yarda".
Na faÉ—a ina jin tamkar zan shiÉ—e.

Barr Mu'azzam ya kalli mai shari'a yace,"Ya mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai adalci da tayi duba akan bayanan Sa'ida sannan tayi duba akan itace ƙarshen ɗaukar yarinyar da ta mutu, yarinyar da lokacin tana hannun mahaifiyarta lafiya lau take, amma da Sa'ida ta ɗauketa sai ta mutu alhalin bata ɗaukar yaran, To babu wuta me ya kawo hayaƙi? Saboda haka Ya mai girma mai shari'a ina so a duba halayen mata akan kishi, tabbas Sa'ida zata iya kashe yarinyar kishiyarta ko don ganin cewa ita bata da su. Don haka na ke roƙon kotu ta hukunta Sa'ida akan laifin kisan da ta aikata kamar yanda mahaifin yarinyar da mahaifiyarta ke roƙon a ƙwatar musu hakkinsu. Na gode ya mai shari'a".
Ya faÉ—a yana dawowa ya zauna.

"Ko lauyan wacce ake ƙara tana da abin faɗa?". Cewar Alƙali.

Ta miƙe tsaye tace,"Ina da shi ya mai shari'a. Ina roƙon wannan kotu da ta bani dama na kira Zahra'u Abdullahi mahaifiyar ita yarintar da aka rasa".

Wani a cikin kotun ya miƙe yace,"Malama Zahra'u Abdullahi in kina kusa ki fito".

Tasowa tayi with confidence. Barr Zaliha ta matso kusa da ita tace,"Malama Zahra'u ya ƙarin haƙuri?".

"Haƙuri da godiya, Na gode".

Barr ta numfasa sannan tace,"Malama Zahra'u ko za ki faÉ—a mana hujjarki da zata tabbatar mana da Sa'ida ce ta kashe miki yarinya?".

Ta gyara tsayuwarta tana kallona, wanda ƙwayar idanuwanta ke nuna tsantsar tsanata a ciki tace,"Saboda itace ƙarshen ɗaukarta kuma goye a bayanta ta rasu".

Barr ta girgiza kai tana murmushi tace,"Wannan ita ce kawai hujjar ki?".

Ta ɗaga kai bayan ɗauke idonta akaina tace,"Zata iya kasheta saboda tana baƙin ciki ita bata haihu ba, shiyasa da ta goyata tayi mata wani abun har ta mutu".

"Kafin wannan lokacin Sa'ida ta taɓa yunƙurin kashe yarinyar?".
Ta girgiza kai tace,"Bata taɓa ba".

Barr ta jijjiga kai,"Ok amma ta taɓa ƙoƙarin shaƙeta ko bata wani abun da zai iya zama silar barinta duniya?".
"A'a bata taɓa ba".
"Kenan akwai kyawun alaƙa ta nuna kulawarta akan yarinyar kafin ta rasu?".

Wannan tambayar da Barr tayi mata sai na saddaƙar, domin dai na san daga ita har Nazifi da Iyam babu wanda zai amsa wannan tambayar da gaskiya. Sai dai kuma mamaki ya kamani da amsar da ta bayar wanda na ke da tabbacin ubangiji ne ya matsi bakinta ta faɗi hakan.

"Ehh to gaskiya tana son yaran, farkon haihuwarsu tana nuna kulawarta akan su, hasalima ni na shiga tsakani na nuna mata bana so tana raɓar min yara, na hanata ɗaukarsu kwatakwata, to da yake tana da sanyin hali da haƙuri sai kawai ta janye jikinta da su saboda a zauna lafiya".

Barr tayi murmushi tace,"To amma kuma duk wannan kyakykyawar shaidar da ta samu daga bakinki me yasa kuke zargin ita ta kashe miki Æ´a?".

Ta kalli Barr tace,"Saboa itace ƙarshen ɗaukarta, kuma a bayanta ta mutu".

"A bayanta ta mutu? Kenan kin ganta da idon ki lokacin da ta kasheta?".
Ta girgiza kai alamun a'a. Barr tace,"Magana za kiyi".

Ta ce,"Ban ganta ba". Ta faÉ—i hakan jiki a sanyaye.

Barr ta juya ta kalli Alƙali tace,"Ya Mai girma mai shari'a ina so ayi duba a bayanan mai ƙara, ayi Nazari za'a tabbatar da babu hujjar da zata gamsar da kotu cewa Sa'ida ita ta kashe yarinyar, ko don duba da yadda ita uwar yarinyar ta faɗa na cewa Sa'ida mutuniyar kirki ce. Idan mai shari'a ya bani dama zan gabatar da insifecta Usman Abdullahi wanda shine ɗan sandan da ya isa da gaggawa gidan a lokacin da abun ya faru".

"Kotu ta ba ki dama".
Chapter 31 · 0% Book details