Sashe 71
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar doluwa nayi saurin girgiza kai. Numfashi ya sauke ya gyara zama sosai tare da cewa,"Ki yi haƙuri da irin ƙarfin halina, haka na ke ni duk wani babban lamari nawa bayan Allah nah to manyana na ke fara sanyawa a ciki, kar ki ce na zaƙe da yawa kawai ina turo iyaye su nema min aure ba tare da na fara fuskantarki ba na nemi soyayyarki. No kawai zan fi samun ƙwarin gwiwa ne da sakewa idan ya zama na tunkare ki da amincewar iyayenki...Kwana biyu da suka wuce iyayena sun zo sun yi magana da mahaifinki...A yau kuma Abbaa ya bani damar in nemi yardar ki, amincewarki ita ce amincewarsa, ni da ke yanzu dukka ba yara ba ne balle a tsaya ɓata lokaci, musamman ma dai ni da na doshi hamsin da ƴan kai....".
Mamakin furucin ƙarshe ya doke wancan mamakin da tunani na, ban san lokacin da na waro ido waje kamar zasu faɗo ba ina kallonsa baki buɗe, a raina na maimaita hamsin fa! Ta gaske ko ta wasa?. Ashe a fili nayi furucin sai naga yay dariya yana tsefe gemunsa kamar wani saurayi ɗanye shagaf yace,"Kin ganni da jikin yara ko, shekaruna basa nunawa a jikina ne, shekarun tsufa fuskar yarinta, kuma hakan ai yafi ko?".
Ya faɗa yana ɗaga min gira dukka biyu, ni dai na san wannan mutumin na gabana bai kai hamsin ba, to me ma abin so a shekarun da yake kai kansa inda bai kai ba? Na ɗauke kai a hankali kuma naji ya ambaci sunana da harafin jaaa, ƙofofin gashin jikina suka buɗe na lanƙwashe yatsun ƙafafuna.
"Sa'idaaaa! Ina son ki, ina miki irin son da ba zan iya misaltawa ba, da ƙyar na haƙura a wancan karon, amma a wannan karon bana jin akwai wasu adadin kalmomi na ban haƙuri da zasu yi tasirin da zan iya barwa wani soyayyata, ki yarda da ni ina faɗa miki abinda ke ƙuryar zuciyata ne, na miki alƙawarin kulawa, soyayya da ƙauna a cikin gidana...please ki ɗago ki kalle ni".
Ya faɗi hakan ni kuma sai na kasa wani motsi illa ma sadda kai ƙasa da na ƙara yi, sai ya miƙo hannu zai ɗago haɓata nayi saurin janyewa ina girgiza masa kai alamun kar ya fara. Sai ya sauke hannu yana faɗin,"Sorry! But please ki sanya idanunki cikin nawa domin ki yarda da abin da na ke faɗa miki ki kuma bani amsar tambayar da zan miki".
Da ƙyar na tattaro courage na sanya ƙwayar idona cikin tasa da ta kashe min jiki a lokaci guda. Ina ƙoƙarin janyewa sai yay saurin haɗe hannaye yana faɗin,"Please". Sai na fasa, shi kuma yace,"Za ki iya auren ƙabila? Za ki iya auren me mata? Kar ki tunani ta yanda za ki fara rayuwa a cikin ƙabilar da ba taki ba, family na suna da sauƙin kai, suna da mutunci, za su karɓe ki kamar ta su, ba su da matsala kuma ina tabbatar miki da ba za ki samu wata matsala tare da su ba, babu ta wani ɓangare da za ki fuskanci ƙalubale na banbancin yare".
Ganin na bada dukka attention ɗina sai ya gyaɗa min kai da cewa,"Uhmm ki ba ni amsa, ni ba zan tilasta miki ba, amma dai zan so ki bani dama, ki bani damar da zan kafa gwamnatin soyayyata a zuciyarki, ina da ƙwarin gwiwa ta wannan fannin".
Idanuwana suka cika da ruwan hawaye sai dai ba su samu nasarar gangarowa ba, a sanyaye na ce,"Wataƙila baka san wacece a gabanka ba ne...".
"Akwai wata Sa'ida bayan ke ne a cikin gidan nan?".
Na girgiza masa kai da cewa,"Ba haka na ke nufi ba".
"To ya kike nufi?".
"Ni bazawara ce ba badurwa ba, kuma ina tunanin ka zo da zummar samun waccan Sa'idar ne ba wannan da yanzu ke a gabanka ba". Na faɗi hakan ina rumtse ido sosai tare da jin wani ciwo a ƙasan raina.
Sautin murmushinsa ya fito sannan yace,"A alqur'ani ko hadisi faɗo min inda aka haramta auren bazawara, na san kina da ilimin hakan, ni kuma in har kika kawo aya ko hadisi zan tashi na bar gabanki kuma ba zan ƙara dawowa duniyarki ba".
"Babu".
"To kuma kike ce min ke bazawara ce, mene da hakan?".
"Saboda maza basa son auren bazawara".
"Saboda bazawara bata darajar da za'a aureta kenan? Ko kuma ita abar ƙyamace da bata cancanci a sota a aureta ba? Look Sa'ida na san da cewa ke bazawara ce, kuma a haka na ke son ki kuma a haka zan aure ki kuma zan zauna da ke a hakan, ke na ke so, ke ɗin dai, hasalima idanuwan Salim basa miki kallon bazawara so kar ki ƙara furta min wannan sunan".
Sai kuma yay ƙasa da murya yana cewa,"Wallahi tallahi Sa'ida ina sonki ina ƙaunarki, ba da cuta ko yaudara ba, da gaske na ke miki aurenki zan yi don Allah ki ba ni dama".
Kawai sai na fashe da kuka sosai har ina kifa kaina a saman cinyoyina, domin kuwa kalamansa sun faman ciwon da ke zuciyata, Ta ya zan yarda da irin kalaman da Nazifi yay min? Ta ya zan kuma gasgata wani namijin har na yi kuskuren aurensa?
Sai kawai na mike ina jin wani ɗaci da ƙunci sun mamaye ni, gani na ke kamar da gangan ya zo yana min wannan maganar, kamar saboda yaci mutuncina ne, to ai ni kuma har abada na rufe babin aure.
Kukan nawa sai ya rikita shi, inda shima yay saurin miƙewa yana ruƙo gefen rigata. A rikice yake tambayata,"Me ya saka ki kuka Sa'ida? Ni na faɗa miki wani abun mara daɗi ne? Don Allah ki yi haƙuri kin ji".
Nayi ƙoƙarin fizge rigata ashe ruƙon da yay mata da kyau, don haka na ɗago cikin kukana me ban tausayi na ce,"Ka sakeni, kuma don Allah kar ka ƙara dawowa gare ni da maganar aure, tsammanina ka zo ne mu gaisa matsayinka na Yayan Safiyya, ashe na tafka babban kuskuren zama ina sauraronka".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ya ambata tamkar wanda ya haɗu da wani ibtila'in. "Ka sake ni ka matsa ka bani hanya". Na faɗa a tsawace ina sake fashewa da kuka. Salim ya shafo kansa yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas da ina da damar da zansa hannayena na tunkuɗe shi daga gabana babu abin da zai hana ni aikata hakan. Kawai sai na tsinci muryarsa a marairaice yana cewa,"Don darajan Allah kar ki min haka, ni ba zan iya yafewa kaina ba idan ya zama ni ne silar wannan hawayen na ki, idan na faɗi wata kalma ne mara daɗi a gareki ki haƙuri ki yafe min kuskure ne ban san na aikata ba".
Kai na girgiza ina cewa,"Ni baka min komai ba, kawai dai ka rabu da ni kar ka ƙara min zancen aure".
Sai kawai ya tsare ni da ido da murya me bala'in sanyi da ban tausayi yace,"To mene laifina da ba za ki so ni ki aure ni ba? Ko ina da wani aibu da ban sani ba? Idan ina da shi ki faɗa min nayi alƙawarin zan gyara, kuma ni ban tilasta miki sai kin aure ni ba idan ba ki da ra'ayina zan ƙyale ki, ba zan miki dole ba amma kar ki zubar da hawaye ta dalilina, ba zan yafewa kaina ba".
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsawa daga gabana, wayarsa da hularsa ya ɗauko ya dawo gabana yana cewa,"Ki yi haƙuri ki yafe min".
Yana faɗin hakan ya juya zai fita, na bi bayansa da kallo, ba tare da sani ba sai na tsinci kaina da cewa,"Ni kawai auren ne bana so da maganarsa, ina jin haushin duqk wata fuska da zata tunkare ni da batun aurena, na rigada na yiwa kaina alƙawarin ba zan kuma yin aure ba...".
Na faɗi hakan kuka na daɗa cin ƙarfina. Ban ankare ba naji ya kama hannuna wanda sai da naji tasirantuwar wani abu a jikina, ya jani ya zaunar da ni a bakin katifa.
Ya durƙusa gabana yana dubana da kyau sannu a hankali ya fara cewa,"Bana so naji dalilin da yasa kika ɗau alwashin hakan, bana so naji ko kaɗan, sai dai hakan da kika ƙudurta ba mafita ba ce kuma ba hanya me kyau kika zaɓarwa kan ki ba, idan kika ce ba za ki kuma aure ba means ba ki son auren kenan and kar ki manta aure sunnar ma'aiki ne me ƙarfi, shi yace kuyi aure ku hayayyafa domin nayi alfari da ku. Ki manta da abubuwan da suka faru a baya ki fuskanci gaba domin shimfiɗa sabuwar rayuwa me kyau".
Sai yay shiru bai ce komai ba. Ni kuma nace,"To lallai sai nayi aure ne zan yi farin ciki? Lallai sai nayi ne rayuwata zata inganta?".
"Kina da amsar dukka tambayoyin ki a wajenki, sai dai ba za ki iya bawa kanki amsar hakan ba har sai kin sanyaya zuciyarki kin yi watsi da ƙudurin da kika ɗauka".
Sai ya miƙa hannu ya tsiyaya kunun aya a kofi ya miƙo min. Na karɓa kawai na riƙe ba tare da na kafa baki ba. Hawaye ya silalo saman kumatuna nace,"Ko da ka aure ni ba zaka iya zama da ni ba, zaka tsane ni ne, danginka ma ba za su so ni ba, zan zama abar ƙi da hantara a cikin gidanka da danginka".
"Saboda mune azzaluman farko?".
Da sauri na girgiza masa kai,"A'a ba haka na ke nufi ba".
Naga ya haÉ—e rai yana cewa,"To me kike nufi?".
"Saboda bana haihuwa, kuma babu namijin da zai iya rayuwa da mace me irin lalurata...".
Ya katse ni,"Wacce irin lalura kenan?".
Na kalle shi,"Rashin haihuwa mana, ko kana sona yanzu daga baya zaka daina sona idan ban haifa maka yara ba, suma ƴan uwanka zan fuskanci ƙalubalen hakan daga gare su, kuma matarka ma zata dinga min gori".