Sashe 11
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motsin shigowa naji na É—ago na waiga kaina ina kallon in da Zahra'u ke tsaye, har zan É—auke kai sai kuma naga tana lalube, ban san me take nema ba, ban ma san me ya shigo da ita kitchen É—in nawa ba, tunda tuni aka raba mana kitchen tun sanda ta nuna bata so mu haÉ—a girki, wai ita ba girkin kowa take ci ba, kuma in aka ce za'a haÉ—a girki ita zata takura da yawa. Sai ya zauna ya sauya tsari yace kowacce ta dinga girkinta amma nauyin ciyar da duk wanda yake zaune a gidan da duk wani É—an uwansa da zai zo ya rataya a wuyana ne.
Ba tashin hankali na ke nema ba kuma ba abu ne da zan soma shi sabo ba na amince ba tare da nuna masa ko rashin jin daÉ—in hakan ba, lokaci ne dai yana nan tafe da zai gane gaskiya kuma Allah ya saka min.
"kina neman wani abu ne?".
Na tambayeta a mutunce, shiru tayi ta ci gaba da binciken durowa, na bita da kallon mamaki ina ajiye kofin hannuna da na É—aga zan sha lemo. Kaf dai kitchen É—in idan ba shi ya faÉ—a mata cewa duk kayan ciki nasa ba ne to banga wani abu da yake mallakinta a ciki ba da har ta zo nemansa tana min bincike haka.
Na buɗe baki na ƙara cewa da ita,"Ina magana kin yi banza da ni. Ko kin mance ba ki da hurumi da nan ɗin?".
"Ba sai kin tuna min ba ai na sani, Idan ban da mallaki anan ɗin ai ba zaki ganni a ciki ba, ko kin manta kafin sama min nawa da yafi wannan girma da ƙawatuwa kayan kitchen ɗina sun haɗu da naki, so ina son bincikar abin da aka iya ɓoyewa ne".
Juyawa nayi ban saurareta ba don na fahimci neman tashin hankali take da ni, ni kuma bata isa ba tayi kaɗan, ko kusa ba zan taɓa sauraron rigimarta ba.
Da farko ta nuna kamar zamu zauna lafiya da ita, tun da har hira muke zama muyi a falo, ayi wasa da dariya cikin mutunci da girmama juna, har ma a lokacin take cewa taga ina fama da halin Fati saboda haka zata gyara mana zamanta don ita gaskiya bata da haƙuri da shiru irina, ni a lokacin murmushi kawai nayi ban ce mata komai ba. Idan gari ya waye taji shiru ban fito ba da kanta take leƙowa ɗakina mu gaisa, to amma lokaci ɗaya sai naga ta fara sauyawa, muna ƴar hy hy da ita kafin kuma ta sauya gaba ɗaya wanda magana ma idan nayi mata bata ɗaga kai ta kalle ni, bar ta dai da min kallon wulaƙanci.
Na kammala duk abin da zan yi na fita na barta a kitchen ɗin. Bayan na idar da sallar magriba ina biyawa Rumana karatu sai naji an murɗa ƙofa, da tsananin mamaki na ke kallon Nazifi da ke shigowa, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai akansa, rabonsa da sanyo ƙafa cikin ɗakina har na mance wallahi. Rumana ta yi masa sannu da zuwa tare da gaida shi, nima kuma yaci darajar yarinyar na buɗi baki nace masa.
"An dawo lafiya?".
Bai amsa min ba sai ce yay da Rumana,"Je ki É—akin ku zan yi magana da Antynki".
Kallona ta tsaya yi don yarinyar tuni ta fara tausayina a gidan, gyaɗa mata kai nayi kana ta miƙe ta fita tana ta waigena, da alama dai tana ji a jikinta ba mutunci ya kawo uban ruƙon nata ba.
Tsaye yay min aka hannaye zube cikin aljihu, jirana yake na masa magana oho dai, ni ko na ci gaba da abin da na ke nayi kamar ma ban san yana cikin É—akin ba, sai can ya nemi wuri ya zauna yana kiran sunana.
ÆŠago ido kawai nayi na dube shi ban amsa ba, ya numfasa kana yace,"Wai ke me yake damun ki ne?".
"Me ko yake damuna, lafiyata ƙalau ni kam. Yanzu dai me ke tafe da kai?".
Kallon mamaki yay min kafin ya ce,"Tambayata kike hakan?". Sai kuma ya kama ɗaga murya yana faɗin,"Sa'ida so kike sai na fito na miki bayanin irin wulaƙancin da kike min ne? Ina matsayin mijinki wanda aljannarki ke tafin ƙafarsa amma ba ki ganina da daraja balle ki mutunta ni, sai in wuce ki wuce ba zaki buɗi baki kiyi min magana ba, yaushe rabonki da zuwa ɗakina? Yaushe rabonki da shiga ki gyara min makwanci? Yaushe rabon da ki dafa abinci ki ba ni? Yaushe rabonki da bani hakkina? Yaushe rabonki da gaishe da ni? Yaushe rabon da na fita na dawo kiyi min sannu da zuwa? Kina abu kamar wadda ke zaman kanta a cikin gidan, ko kina so ki faɗa min ke kika auro ni?".
Ya kai aya ya kalle ni muka haɗa ido, muryarsa ta ƙara fitowa da ɓacin rai wajen cewa,"Ina magana kin kafe ni da ido, to na gaji da wannan halin rashin mutuncin da kika tsira, idan kuma hakan kika zaɓarwa kan ki ni ban da matsala ban da damuwa tunda ba ke kaɗai na ke aure ba, a yanzu ina da wadda ta fiki komai, wacca tayi miki tseren da ba za ki taɓa iya taddota ba, Zahra'u ta fiki wayewa, ta fika iya kwalliya, ta fiki sanin yanda zata tarairayi miji da ba shi kulawa, ta fiki iya soyayya, ta fiki iya gado haka kuma ta fiki ɗanɗano, saboda haka Sa'ida kar kiyi tunanin wannan girman kan da kika ɗorawa kan ki zai dame ni domin da ke da babu ɗaya a wurina".
Rasa abin ce masa nayi, kallonsa na ke babu ko ƙifce, haka kawai sai na fashe da kukan da na jima ban yi ba, kuka na ke sosai kafin na fara ce masa.
"Nazifi ni kake faÉ—awa waÉ—annan maganganun?".
Na miƙe jikina na karkarwa na ke cewa,"Ban san me na maka ba ka tsane ni? Amma kuskurena ne da na rusa farin cikin iyayena na zaɓeka, ban da haka da baka aje ni cikin gidanka kana gana mun azaba ba, da baka kalle ni kana gaggaya min magana irin haka ba, haba! me na maka a rayuwar nan Nazifi? Me nayi maka da na ke fuskantar tozarci irin haka daga gare ka?...Kuma ma idan har da gaske ni da babu ɗaya ne a wurinka menene na zuwa kayi ƙorafi akan hanyar da na zaɓa wadda na ke jin sanyi cikin raina, Mene damuwarka da rashin kulaka da na ke yi ɗin ehh Nazifi? Mene damuwarka na ce?...".
Ni gaba ɗaya ma sai na rasa me zan ci gaba da cewa, nema na ke kawai na rikice, banɗaki na nufa zan shige ciki domin Allah ya gani bana son ganinsa a gabana, ruƙo hannuna yayi ya janyo ni na dawo gabansa yana zuba idanunsa akan fuskata, ƙasa da murya yace,"Kin san me ya kawo ni wajen ki?".
Hawaye ne kawai na ke ban iya ce masa komai ba, sai ya ƙara cewa,"Idan kina tunanin na zo karɓar wata tsiya daga jikinki ne to kinyi kuskure. So idan kin gama kukan Zahra'u na so taci awara da kunu".
Ban san lokacin da nayi masa wani kallo na baka da hankali ba kafin na ce,"Me ya shafe ni da abun da zata ci to?".
Kai tsaye ya maimaita min,"Kunu da Awarar da kika dafa za ki zo ki zubawa Zahra'u tana son ci".
Na ƙwace hannuna daga ruƙon da yay min, ina goge hawaye na ce,"Saboda ita ta dafa? Ko kuma saboda kai me karɓa mata ɗin ina tsoronka?".
Buɗar bakinsa zai magana aka turo ƙofar ɗakin, muka waiga a tare, Iyam ce ta shigo da kwano tana ce min. "Ke ƴar nan ina kunu da awara da kika dafa? Zubo maza anan Amarya zata ci".
Wani murmushi nayi a ƙasan raina, duk ɗin su na gane inda suka dosa, suna so su faɗa min cewar sun samu ƙaruwa ne wanda na fahimci hakan tuntuni. Zazzafan hawaye ya ƙara sakko min nasa hannu ina gogewa, ta dube ni tana min kallon sama da ƙasa ta ƙara cewa,"Ki bar zagina cikin ranki ki bani abun da na ke tambayarki".
Na ce,"Ai ba da ita na dafa ba Iyam, azumi nayi na dafa iyaka cikina kuma na cinye".
"Iyeee lallai Sa'ida, Dama har za ki dafa abinci a gidan nan ni ba ki bani ba?".
Na saki baki ina kallonta ganin zata min sharri gaban É—anta na ce,"Akwai wata rana da na hanaki abinci ne Iyam? Wannan awara da kunu ne nayi na shan ruwa kuma azumin nan ni kaÉ—ai nayi".
"Ohh ni ban yi ba kenan ban isa ki dafa komai da É—ana ya siyo ya ajiye ki iya zubawa ki bani ba, da kyau. To yanzu dai ko me za kiyi ki zubo akaiwa Amarya don babu in da za'a je samun na siyarwa yanzu, idan kuma kin cinye É—in ki fito yanzu kije ki dafa mata wani".
Nayi murmushi na ce,"Kiyi haƙuri Iyam, amma ko akwai wallahi ba zan bayar ba, haka ko da babu wallahi ba zan dafa saboda ita ba. Jikin aiki na fita? Ko kuma iya dafawar ne bata yi ba da ita ba zata girkawa kanta ba? Ita har mene ma na sha'awar abun hannun kishiya da zata taro jama'a su zo su ƙwatar mata? To kunu da awara ne nayi nawa ne babu kuma wanda zan bawa a cikin gidan nan wallahi...".
Maganata ta katse ganin Nazifi ya ɗaga hannu zai sauke min mari, Iyam tayi saurin dakatar da shi da cewa,"A'a ƙyaleta Shalele, ai ba komai take ba sai baƙin cikin Amarya ta samu ciki ita ta nan sai ci da kasayarwa, daga yarinya ta samu ciki kuma sai ki hau baƙin ciki da hassada".