← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 113

Sashe 68

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baban su Safiyya yace,"Ya sani Malam Salman, ya san komai, sannan shima ɗin ba wai saurayi ba ne da aurensa, bayan aure ma har da arziƙin yara uku...".
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR03FT5*
Abbaa yay shiru yana nazarin kalaman na su, ba zai ƙi tayinsu ba, domin shi kansa ko a wancan lokacin Salim ya kwanta masa a rai, yafi gamsuwa da shi fiye da duk waɗanda suka zo neman auren Sa'ida, shiyasa ko a lokacin ya yarda ya amince aka karɓi kuɗinsa bisa sharaɗin da ya gindaya na cewar sai ta kammala makaranta, kuma ko a sanda suka zo karɓar kuɗin su bai ji daɗi ba fiye da adadin kalmomin baki, ba wai rashin jin daɗi na sun wulaƙanta su ba kan karɓar kuɗin ba, a'a rashin jin daɗin Ƴarsa ta rasa yaron kirki, yaro me nagarta kamar Salim, yaga haƙiƙanin soyayyar ƴarsa a ƙwayar idon yaron, haka ya tsinci raunin rasata a muryarsa, kuma gamsu ɗari bisa ɗari da irin shaidun da mutane suka yi akansa, ba tare da sanin iyalinsa da kowa ba ya ɗauki ƙafa yaje har garin Anambra state domin yayi kyakykyawan bincike akan yaron da iyayensa kuma duk suka samu shaida mai kyau, dama tsoronsa ɗaya bawa ƙabila auren ɗiyarsa.

To a lokacin da ace shi irin mahaifin da ke tilastawa É—iyansa abin da yake so ne ko da basa so, to da lashakka Sa'ida bata isa ta auri wani miji bayan Salim ba, to sai dai babu yanda zai yi shi uba ne me son farin cikin Æ´aÆ´ansa kuma me son dukkan abin da suke so ko da shi ba ya so in har wannan abu bai kaucewa shari'ar musulunci ba.

A yanzu tarin tambayoyi ne a ransa to amma zai bar su bincikensa ya ba shi amsa, akwai dai damuwa da fargaba a tare da shi. Major ya katse tunaninsa cikin magana me taushi irin ta dattijon arziƙi, yace,"Malam Salman Safiyya ita ta tabbatar mana da babu maganan wani akan ƴarka, bisa wannan dalili muma muka ga ya kamata muyi gaggawan zuwa kar mu makara. Kuma ni da kaina ina baka tabbacin insha Allahu my Son zai kula da ƴarka ba zai ci mutuncinta ba, yaƙini na ke baka akan hakan saboda na san waye yarona".

Da irin waɗannan maganganun Major ya ƙarfafawa Abba gwiwa. Wanda har Abbaa ya dinga jin zuciyarsa na buɗewa da yarda gami da farinciki, sai dai ba zai zama me fatan lamarin ya kasance ba har sai yayi istikara ya kuma sa Sa'ida tayi istikara itama.

Abba yay nisa sannu a hankali ya fara magana da cewa,"Tom ni babu abin da zance sai Allah ya zaɓa mafi alkhairi wa yaran namu. Sannan kamar yanda na faɗa muku ne Ƴata ba budurwa ba ce bazawara ce, saboda haka ni ban da hurumin da zan mata zaɓi kai tsaye domin kuwa shari'a ta bata damar yiwa kanta zaɓi".

Alhaji Mukhtar ya jijjiga kai da cewan,"Wannan haka yake Malam Salman, magana ce me kyau kayi".

Abbaa ya sake cewa,"To madallah, saboda haka ku faɗa masa cewa ya zo ya fara samuna domin ina da buƙatar na gana da shi kafin na basa damar ganawa da ita ƴar tawa su sasanta kansu".

Major shi ya fara cewa,"Tom shikenan zai zo É—in in Allah ya yarda, muna godiya".

Gaba ɗayansu kuma sai suka shiga yima juna godiya kafin suyi sallama su miƙe zasu tafi, Abba ya shiga ciki ya karɓo leda wurin Ummani yazo ya kwashe kunun ayar da ruwan ya zuba musu a ciki ya raka su da shi har mota. Kamar yanda suka ji daɗi suke ta godiya da irin karramawar da Abbaa yayi musu haka shima ɗin yake ta godiya a gare su. Bayan tafiyar su ya wuce masallaci bai dawo cikin gida ba sai da yayi sallar isha'i.

Ya shigo a lokacin Ummani na daga ciki tana lazimi, yay É—akin nata ya zauna daga bakin gado, kuma zuwan nasa yasa Ummani idda lazimin nata tare da juyowa ta fuskance tana nazarin yanayin fuskarsa kafin tace,"Abbaa lafiya dai ko?".

Abbaa na duban labulen É—akin kamar me son karanta wani abu a jikinsa yace da ita,"Ehh to lafiyar zamu ce".

Furucinsa nasa yasa gabanta faÉ—uwa, ta É—aga hijabinta ta cire tana aje carbi ta tashi daga kan dardumar ta dawo kusa da shi ta zauna. "Wani abu ne ya faru? Shi Alhaji Babangidan me ya kawo shi kuma mene haÉ—insa da su mutanen?".

Ganin duk ta ruɗe Abbaa yay murmushi yana me ɗora ƙafarsa ɗaya akan gado ya fuskanceta, fuskarta ya shafo tare da cewa,"Kwantar da hankalinki matata ta kaina, Sa'adatun Salmanu ba komai ya kawo su ba face alkhairi".

Ummani ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana karayar da kai kafin tace,"Yanzu naji batu, amma da hankalina gaba É—aya a tashe yake, wallahi ka ganni tun da na zauna Allah na ke ta faÉ—awa, to ai Alhamdulillahi tunda ba wata matsala ba ce, amma me ya kawo su?".

Abbaa yace"Zuwan na su akan Sa'ida ne".

Cikin mamaki Ummani tace,"Sa'ida kuma? Na shiga duhu me ya faru da Sa'idan?".

"Kinga samu nutsuwa don Allah, zuwa suka yi da batun aurenta...".

Bai ƙarasa ba ta katse shi,"Kamar ya ban gane ba, shi Alhaji Babangidan ya zo maka da wannan zancen kuma ka tsaya sauraronsa? Ya manta mahaifin ƙawarta ne shi ko kuwa ya manta akwai aminta tsakanin matarsa da ni? To ban da ma mutuwar zuciya ina shi ina zuwa neman auren Sa'ida fisabilillahi, kuma kai bai ji kunyarka ba ma".

Tayi maganar cikin Firgicin da ya bayyana a muryarta zuwa ƙwayar idonta da ta fito waje. Wannan yanayin nata da kuma maganar da tayi sai ya bawa Abbaa dariya.
Aifa ran Ummani ɓace ta miƙe tana faɗin,"Dariya na baka kenan, to ba zai yiwu ba wallahi, yanda ya zo ya tafi ya tafi kenan babu wani aure tsakaninsa da Sa'ida, hauka ake yi?".

Abbaa yace,"To idan Allah ya ƙadarta faruwan hakan fa? Kuma ina ga ai ba haramun ba ne don ya aureta".

"Allah ma ba zai ƙadarta hakan ba ubangiji ai ya san daidai, kuma nima ai ban ce haramun ba ne sai dai ai akwai duba a lamarin, kuma ya ce ko ka faɗa masa babu wurin shigarsa?".

Abbaa na yin wata dariyar ganin duk tayi kicin kicin yace,"A'a na dai ce masa ya dawo gobe ya ganta, tunda yace yana so a ba shi dama ya shiga jerin zaurawanta ya fara kafa gwamnatinsa da wuri".

Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda na san waye mijina wallahi sai in ce mutumin nan siyeka yayi da kuɗi, yanzu tsakani da Allah sai ka bar Babangida ya auri ƴarka? Kenan kaima a wannan shekarun naka tsofe tsofe zaka iya zuwa neman auren ƙaramar yarinya ƴar cikinka ta kusan nawa? Ko da ike zamu ce ta tadda muje".

Abbaa ya buɗe ba ki da mamaki ƙarara yana dubanta yanda duk ta mayar da maganar gaske.
"Ka saki baki kana kallona, to ni dai ba dani za'ai wannan zalunci ba, yarinyata da sauran ƙuruciyarta don tana bazawara ba zai yiwu a laƙaƙa mata auren tsoho ba, daga nan har hizba wallahi, mene wani Babangida daga ya ɗan taimaka mana sai ya wani kwaso ƙafafunsa na marasa kunya yace ya zo neman auren ƴar cikinsa".

Abbaa yace,"Babangida kai tsaye ma babu Alhajin".

"Yo wanne Alhaji bayan ya zubar da girmansa, neman aurar Æ´ar cikinsa fa yake yi kuma daÉ—in abin kunyar ma aminiyar Æ´arsa".

Ganin fa ta haƙiƙance har tana ɗaukan fushi da shi sai mita take yi yace,"Kinga ke ba ki tsaya kin gama jin bayanin da zan miki ba kawai kin hau kan wata maganar, Aure fa ɗan su suka zo nemawa ba kansa ba".

Ƙyam Ummani ta tsaya ko ƙyafta ido babu. "Ɗansa?". Sai kuma ta dawo ta zauna tana cewa,"Kar dai kace min yaron nan Khalid me hankali, ka san ƴaƴansa maza biyu ɗayan kurma ɗayan kuma shi ne lafiyayye".

Abbaa yace,"To ai bama a nasa Æ´aÆ´an ba ne, É—an Yayar matarsa ne yaron nan Salim da suka nemi aurenta tun tana budurwa".

Ummani ta ware ido akansa ƙwaƙwalwarta na auna maganarsa kafin tace,"Wai kana nufin yaron da ya kawo kuɗi suka dawo suka karɓa?".

Abbaa ya jinjina kai yana Faɗin,"Ƙwarai shi fa".

"Abbaa sojan nan fa da kace min babba ne da gwamnatin tarayya yake aiki".

"Shi dai Sa'a".

Nan Abbaa ya shiga bata Labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da su Baban Safiyya, Ummani bata jira ƙarashen zancen ba ma ta rangaɗa guɗa a hankali. Ta ɗaga hannu sama tana faɗin,"Allah gatan bawansa, Allah mun gode maka, Allah maji roƙon bawa".

Bakin Abbaa buɗe yake kallonta, mamaki sosai ya kama shi, kar dai abin da ke ransa ne a nata ran itama? Kawai sai yaji tana ƙara faɗin,"Bayan wuya sai daɗi, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, Rabo daga sarkin da ba ya zalunci, bijahi rasulillahi wannan yaron alkhairin Sa'ida ne".

Abbaa yace,"To ke wai kin san yaron nan ne da kike ta farin ciki haka".

"Abbaa ya ba zan yi farin ciki ba, ɗan gidan manya mutane fa, to ni dai wallahi ba don kuɗi ko matsayi ba zaɓin Allah na ke ta nemawa yarinyar nan kuma ina da yaƙinin Salim shi ne Allah ya zaɓo mana, domin kuwa tunda ta fito zaurawa ke ta sintiri akanta ban ji ina farin ciki da zuwan wani ko naji sha'awar ta ƙara yin wani auren ba sai da wannan batu ya afku".
Tayi maganar baki dukka a buÉ—e kamar zai yage saboda murna.

"Yanzu a wacca matsaya ku ka kwana da su? Na san halinka Allah sa suma ba ce kayi su kama gabansu ba, don ni dai ban sani ba Abbaa ko kwaÉ—a Sa'ida zamu yi muci ba".

Yay murmushi yana cewa,"Ba haka ba ne Sa'a, aurenta na baya ne har yanzu abinda ya faru bai gushe min ba, shiyasa na ke ta jin tsoro ban san da wa zan kuma haÉ—ata ba".

"To ya za'ai na faÉ—a maka ba dukka aka taru aka zama É—aya ba, adu'a zamu ta mata ya bata wanda yafi wancan".
Chapter 68 · 0% Book details