Sashe 57
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza kai nayi ina faɗin,"Allah ya kyauta, ita Umma ana girma rayuwa na tafiya amma tana abu kaman yarinya ƙarama, wa ya san ranar rabuwar da babu dawowa, ni kam ban jin daɗin halin nan nata".
Ashe Abbaa yana jiyo mu sai ga shi ya fito daga ɗaki yana cewa,"Kin ga rabu da ita kar ki je, idan Babanki ya dawo taci albarkacinsa. Shiga ɗakin Kakan ku ga shi can naji yana ƙwala kiran ki".
Allah sarki Kaka, ai kuwa da hanzarina nayi ɗakinsa, ina shiga na same shi kishingiɗe yana firfita, ya ƙara tsufa bawan Allah, na isa gabansa kaina rissine a ƙasa muka gaisa, ashe bama ya gani sosai yanzu dama tun ina can ake ta ce min yana fama da jinya, to da yake dai cuta ba mutuwa ba ce. Na ɗan jima a wurinsa kafin na fito na koma ɗakin Abbaa, na same shi zaune shi da Ummani, an baje min kulolin abinci Ummani na cewa,"Da duk yanda aka yi a ƙoshe kike ko, na ga ba ki halin sabonki ba na ki diro gida ki ce akwai abinci".
Gajeriyar dariya nayi ina cewa,"Kinga ai mun ci abinci a jirgi shiyasa, don ma dai na ce ba zan ci da yawa ba kar na cika cikina".
Ummani tace,"Ohh banda Allah waye zai maka, wai yau ƴar mu ce ta hau jirgi ta keta hazo, to ubangiji yanda ya kira ki tafiya ƙasar turai karatu ya kira mu zuwa ƙasa me tsarki mu ziyar ɗakinsa mu ziyar ci ƙabarin masoyi fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW".
Dukkan mu muka yi salati ga manzon tsira, na zauna ina cewa,"In sha Allahu Ummani indai saudiya ne mun kusa muje, Allah ya bani arziƙin da zan kai ku, amma tabbas a jikina ina jin lokacin ya kusa".
Ita da Abbaa suka haÉ—a baki wajen furta,"Ilahi ajib".
Sannan muka shiga gaisawa da su, zuciyata sai motsawa take da so da ƙaunar mahaifana gami da tausayin su da jin ƙan su, rayuwa kenan duk sun ƙara girma musamman ma Abbaa kansa duk furfura ta fara yawa, da ka gansa dai ka san shekaru sun ja masa. Ummani tace,"Ai ni dawowarki ta min hajji da umara, ga shi nan tun shekara jiya Abbanki ya siyo ganda saboda ke".
Tuni yawuna ya tsinke na matsa wajen kwanukan ina cewa,"Allah sarki Abbaana na gode Allah ya ƙara lafiya da wadata, fatan dai ba'a kwashe an rabar min ba".
Ummani na girgiza kai tace,"Au wahalar dafuwar ma da nayi ban miki gwaninta ba kenan, to bara na ɗauka na ƙarasa rabarwar".
Murmushi nayi da cewa,"Yi haƙuri Ummanin mu". Tuni na tasa kwano a gabana na fara kaiwa baka don ganda na ɗaya daga cikin naman da na ke so a rayuwata, ko da sallah ni ban fiya ma cin nama ba kamar yanda na ke cin ganda".
Da yake ba wani yawa ne da ita ba dama dai ya siyota ne saboda ni É—in, don haka tuni na ga bayanta Ummani har na tsokanata da kura kura. Bayan na gama ci ne nake cewa,"Wai yaushe su Maman Yasmin suka yi tafiyar?".
Ummani tace,"Kwana uku da rasuwar kenan, shima Yashaik É—in ai sai É—azu da rana ya tafi da yace zai jira dawowarki".
Nace,"Allah jiƙan rai, naji mutuwar iya kuwa".
"Da safe sai ki kirata ki mata gaisuwa, kin san ita ta yayeta".
Abbaa yace to naje nayi salloli na kafin yaje masallaci shima ya dawo, na fito sai yanzu na ke ƙarewa gidan namu kallo da yake sun kawo nepa yanzu yanzu, sai naga gidan yay min faɗi kamar ba shi ba, an dai yi masa kwaskwarima ba kamar yanda na tafi na barsa ba, duk jikin bango da ya farfashe anyi siminti, sai irin fasassun tiles ɗin nan iri ɗaya da aka lailaye tsarkar gidan da shi, yay kyau sosai wallahi, gyara yana da kyau a ƙalla ko baka sabunta ba yafi ka bar waje a lalace.
Na idar da Alwala na ke cewa da Ummani wacca ke daga cikin É—aki,"Ummani wa ya saka tiles É—in nan?".
Tace,"Al'amin ne wallahi, sun yi aikin gini a wani gida sai me gidan yace ma'aikatan su ɗauka su raba, shi ne bayan sun rarraba shi kuma ya ƙara siya, har fa ɗakina da na ki, ɗakin Abban ku ne kawai ba'a saka ba, yayi kyau ko?".
"Kyau sosai ma Ummani, sai ya ƙara haska gidan".
"To yi dai sallar tukunna kya gyaran da aka yi, É—akinki kamar ba shi ba".
Tsalle na É—anyi ina murna na ce,"A'a su Yaya Al'amin anyi abin kai iyee, har da É—akina".
Ɗakin nawa kuwa yay kyau, an yi shafe irin dai ragowa yay aka ɗan gogga, dama tun asalinsa ba fenti siminti ne shima kuma ba ko'ina ba, hatta rufin ɗakin ma an mayar da silin wajen da suka ciccire in ana ruwa ya dinƙa zuba.
Allah sarki uwata ta gyara min shi gwanin sha'awa sai ƙamshin turaren wuta yake yi, ƴar yaloluwar katifata ma ta lailaye min ita da wani tsohon bedsheet ɗinta, bani da filo amma har da filo ba zai wuce ko nata ko na Abbaa ta ɗauko min ba.
Allah dai ya bani ikon kyautatawa musu, ya kuma basu tsawon rai da lafiyar da zasu ci moriyata.
Bayan na idar da sallah ina ƙarasa karanta suratul yasin da iza waƙa da basu wuce ni duk dare, Ummani ta leƙo tana ce min. "Kinga da na zuba miki ruwan zafi kiyi wanka, ko ba sai kin yi ba?".
Na kai ƙarshen suratul yasin ina cewa,"Zan yi Ummani, jikina duk gajiya".
"To sai ki hanzarta kar ya huce, garwashin ya ƙare kuma bamu da wani gawayin a ajiye, gas kuwa yay tsada idan kin ganmu da shi albashi aka yiwa Yashaik".
Na shafa adu'a na miƙe ina lalubo zani na ɗaura, ita kuma sannan ta shigo tana gyara min net ɗin da aka kafa a jikin taga saboda sauro.
"Wallahi Ummani gyaran nan da aka yi yayi kyau, kinga anyi dabara sauro ya rage shigowa".
"Al'amin yay dabarar, ba kiga har bakin ƙofar ya haɗa da net ba a jikin labulen, Abbanki yanzu sai yay kwanciyarsa ma babu net ba maganin sauro".
"An huta ai da cacar siyan maganin sauro kuwa, Su Yaya Al'amin an yi abin arziƙi".
Ta É—an yi dariya da cewa,"Ke da shi idan ya shigo ya jiki, kyama yi masa Allah sanya alkhairi anje an tambayo masa aure".
Na waro ido waje ina faɗin,"Da gaske Ummani! Tab wace wannan kuwa ta ɗaukarwa kanta halin nurƙufanci". Na ƙyalƙyale da dariya ina sake faɗin,"Tab Yaya Al'amin ni wallahi ban tsammaci ma yana kule kulen ƴan mata ba, dama shiru shirun nan ki kalle su kawai, aina ya samo matar Ummani?".
"Kin ma santa ai, ina gidan Alhaji Saleh nan baya wajen gidan me markaÉ—e, to jikin gidan akwai gidan farare da ake cewa ana siyar da kunu da awara da safe".
Nace,"Eh eh na gane gidan, da suna markaÉ—e ko?".
"Ƙwarai nan kuwa, to ɓangaren da suke yin gurasa za kiji ana wajen Baaba tabawa, ai yarinyar jikarta ce ruƙonta take yi".
Bakina buÉ—e nace,"Ko dai wata za kiga tana biyowa Sajida tafiya islamiya, doguwa fara me É—an jiki haka, naji kamar ma buzuwa suke ce mata".
"Ai kuwa dai ita ce, su Abbanki har wani daji acan ƙarshen katsina suka je bincike".
Ina kaÉ—a kai na ce,"Abbaa kenan, hakan ai yana da kyau gudun samun matsala".
Muna haka Yaya Al'amin ya leƙo ɗakin, guntuwar dariya saman fuskata na ce,"Su Yaya ashe an girma an kusa aure".
Murmushi yay yana kawo min hannu yace,"Ki kiyaye ni, ke ai na ke jira ma ki zo ki kwance jaka ki fiddo min lefena dan nauyin akan ki yake yarinya".
"Yaya baka da damuwa kai dai kayi adu'a Allah yasa na samu aiki, in dai aiki ya samu Yaya to lefe sai na maka akwatu biyu da izinin Allah, ai kafi ƙarfin haka ma a wurina, ko me nayi muku ban faɗi ba wallahi. Ga gyara nan ma kayi mana gida yay kyau mun zama ƴan gayu".
Yace,"Kin ga ma gado da kwabarta nace a kaiwa Yahuza kafinta ya siya na cika ayi mata sababbi taƙi yarda".
Ummani tayi karaf tace,"Kaga ni fa ka ƙyale ni da wani zancen sauya gado da kwaba, ka adana kuɗin akwai lokacin amfanin su, haka kawai na tsufa sai kace wata yarinya ace za'a sauyan kayan ɗaki".
Na fita a ɗakin ina cewa,"Ƙyaleta Yaya Al'amin ka yiwa Abbaa gudunmawa idan ya tashi ƙaro aure, ai dama naji ƙishin ƙishin ɗin sun daidaita da Rabi dillaliya".
Karaf naji saukar murfi akaina. Ina dariya sosai na shige banÉ—aki da gudu, bayan na fito a wanka na shirya tukunna na isa É—akin Abbaa, ina shiga yace naje mu gaisa da Baba Sabi'u da Baba Tijjani duk sun dawo.
Sai bayan na dawo daga wurin su ne na ci abinci na ƙoshi sannan kuma aka shiga hira, ina ta basu labarin can ƙasar da yanda akayi gwagwarmayar karatu. Sosai iyayen nawa suka ji daɗin yanda ban wani wahala ko na fuskanci ƙalubale mara daɗi ba, dama ƙalubalen dai farko farko ne da ban wani ƙware da iya turanci ba to sai nayi ta jin wahalar yin magana da mutane musamman Malamai, har dai kuma a hankali da Allah ya haɗa jinina da wata Joy Johnsun take cewa haka zan ke ta gwada ko da za'a min dariya, nobody is perfect duk wanda ba yaren uwarsa ba ne to koya yay, da hakan kuma sai ga shi ko a award ɗin speech na ƴan nigeria da aka bayar ina ɗaya daga cikin mutum biyar da aka bawa kyauta, ni ce ta uku sai wani mas'ud da tare muke karatu da shi aka basa na ɗaya.