Sashe 70
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
With confusion na ce,"Babu komai, kawai na dawo daga aiki ne yanzu na gaji ina so zan yi bacci".
Na faÉ—a ina sauke wayan daga kunnena na kashe bayan ya cika ni da godiya.
Daga can ɓangaren Salim ya sauke ajiyan zuciya, sai yanzu ya samu relief jin muryanta ba cikin yanayi na damuwa ba kamar yanda ya tsammata, kenan babu wata matsala saboda sosai ya damu da yanayin da yaga Abbaa a ɗazu, ya san dole zata sha faɗa kam, don faɗan da Abbaa ya dinga mata a lokacin ji yay kaman ya fito ya ba da haƙuri, shi kansa ji yay ba zai iya barinta ta tafi ita ɗaya ba a wannan daren shiyasa ya aje motarsa ya shiga napep ɗin domin ya san idan yace ta zo ya rage mata hanya ba yarda zata yi ba.
Ya sauke a jiyan zuciyayana aje wayarsa, tare da jingina kai a gadon ta gefen ƙwayar idonsa kuma yana kallon Kudrat da ke gefensa tana bacci.
******Bayan kwana biyu yau tun tashina Ummani tace da na gama komai na gyara ɗakin Al'amin akwai baƙin da za'a yi anjima. Ban tsaya tambayarta ba ni dai ina gama wanke wanke na shiga na gyara tass, na sanya turaran wuta me bala'in ƙamshi da nasa ordarsa daga meduguri. Gidan duka ya ɗauka har Ummansu Hindatu sai da ta leƙo tana faɗin kamar gidan haihuwa ko sabuwar amarya.
Ummani tace na shirya zan rakata unguwa, nayi wanka na saka rigar bubu sai ce tayi lallai sai na sauya in ɗauko abayata da na siya kwanaki mana. Na ce an gama ranki ya daɗe, haka na ɗauko na saka na zauna zaman jiranta sai ƙorafi na ke ina Ummani ki zo mu tafi kin san ba wuri ɗaya kike zuwa ba, an ta shige shige kenan yanzu za ki ga yamma tayi.
Tace kar na dameta in ban rakata Yasmin zata rakata. Ban ƙara magana ba na fito da keken ɗinkina tsakar gida na hau ɗinka kayan wasu da za'a kaiwa bauchi.
Lokacin yaro ya shigo yana cewa ana sallama da Abbaa, na tashi na leƙa ɗakin na faɗa masa, babu jimawa ya fito ya fita, can ya kuma dawowa yace da ni na ɗauko masa tabarma. Da kaina na kai soro na shimfiɗa kana na dawo ciki.
Abbaa ya leƙa daga waje, tsaye ya hangi Salim jingine da motarsa hannayensa harɗe saman ƙirji, cikin kamilalliyar shigarsa ta cofee ɗin yadi da ɗinkin irin na yare, shigarsa tayi masa bala'in kyau.
Abbaa dai murmushi ya suɓuce masa, tun asubahin yau ko kuma yace tun a lokacin da yay sujjada ga ubangiji a cikin dare yana me neman zaɓinsa akan lamarin Salim da Ƴarsa yaji fargaba ya barsa yayin da ƙwarin gwiwan aurama Salim ƴarsa ya shige shi, kuma a yanzu da idanunsa ke kan yaron sai yake jin yana samun salama a cikin ransa dangane da lamarin.
Yaywa Salim izinin shigowa, ya tako cikin tafiyarsa ta namiji me cikar zati da kamala ya shigo soron lokacin Abbaa har ya zauna akan tabarmar, ya cire takalma ya nemi waje ya zauna, zaman nasa ma har sai da Abbaa yace masa tukunna don da tsugunawa yayi cikin jin nauyin zama a inda surukinsa ke zaune.
Ya gurfanar da kansa gaban Abbaa kamar me neman gafara, da girmamawa da ladabi ya sake gaida Abbaa a karo na biyu, Abbaa ya amsa ƙwayar idonsa ƙyam akansa tun a ɗazun.
Abbaa yay nisa tare da sauke numfashi ya kira yi sunansa. "Salim ka ke ko?".
"Ehhh Abaa".
"To ya kake ya aiki?".
"Alhamdulillahi Abbaa, fatan na same ku lafiya".
"Lafiya lau, Salim ko za ki iya faÉ—a min dalilin zuwanka wurina?".
Da wani ƙwarin gwiwa da jarumta irin tasa ta sojan gaske yace,"Abbaa na zo gare ka ne da ƙoƙon baran ka bani amanar rayuwar ƴarka Sa'ida...".
Abbaa ya katse shi,"Amana dai Salim? Ka kuwa san amana?".
"Na sani Abbaa, ni musulmi ne cikakke, kuma ina da yaƙinin zan riƙe amanar shiyasa na ce aba ni ita".
"Salim amana tana da girma, wutar Allah na cin wanda bai riƙeta ba".
"Bana fatan na kasance cikin sahun maciya amana Abbaa, ka yarda da ni zan riƙe amanar da zaka bani tsakani da Allah".
Abbaa ya sake cewa,"Kai ka turo iyayenka kenan ko kuwa sun yi zuwan kan su ne?".
"A'a Abbaa ni naje musu da maganar".
"Amma me yasa baka fara zuwa da kan ka ba? Ko kuma kana ganin kawai don mahaifanka sun zo sai na ce musu na baka ƴata? Shin ka taɓa neman soyayyarta ne?".
Ya ƙara yin ƙasa da kai kafin a hankali yace,"Bamu da ƙarfin ikon da zamu zo kai tsaye mu ce zamu ne abu a bamu ta yanda muke so, na fi so ne a duk sanda wani babban lamari ya shiga gabana na fara saka manyana a ciki, musamman sha'ani me girman gaske irin wannan. Sa'ida kuma ban taɓa tunkararta ba, kawai dai na san da cewa in har iyaye suka amince min na nemi soyayyarta da sannu...".
Sai yay shiru bai iya ƙarasa faɗin abin da zai ce ba. Abbaa yace,"Da sannu me? Yi min bayani ina jinka".
Ya sarƙe yatsunsa da ƙyar ya iya cewa,"In har ta bani dama na shiga sahun manema aurenta da sannu zan koyar da ita so...". Sai kuma ya canja kalamin da cewa,"Da sannu zata aminta da ni".
Abbaa ya jinjina kai sannan yace,"To amma kai da kake da iyali mene naka na son ƙara aure Salim? Ba ku zaman lafiya ne ko kuwa dai lamarin wasu mazan na son wulaƙanta matayen su ne?".
Abbaa yay maganar wajen bugun cikin Salim ɗin. A hankali kuma cikin natsuwa Salim yace,"Babu ko ɗaya Abbaa, ina dai da sha'awan ƙara aure ne domin ko addini ya bamu damar yin hakan, idan har muna da iko kuma zamu yi adalci zamu iya ƙara aure. Sannan zaman lafiya iyaka gwargwado akwai shi tsakanina da iyalina, bani da nufin na ƙara aure don na ci mutuncin iyalina, ba zan ƙara aure don na cutar da wani ɓangaren ba, lamarin aure abinda Allah ya nufa shi ke kasancewa".
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR05FT5*
Idona da ke kallon fuskarsa sai naga kamar ya haska min da ƴar ƙaramar damuwa, na tsinkaye shi da ci gaba da faɗin.
"Kina son sanin tarihina tun daga tushe?". Bai damu da jiran na amsa mishi ba ya ɗora da faɗin,"Mahaifina haifaffen garin Anambra state ne ɗan ƙabilar Igbo, Asalin sunansa na yare Kaodinakachi, sunan mahaifinsa Chibuzo Ibrahim Ude, sunan matarsa Isioma Debare kuma ƙabilar su guda, sai dai ita kirista ce bayan ta aure shi ne ta musulunta. Mahaifina shi ne na uku a ƴaƴansu, kasuwanci ya kai shi garin Oyo, a can garin ya haɗu da mahaifiyata Kafayat Oluwa Sunmola, ita kuma yoruba ce, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninsu wanda har su ke tunanin rayuwa ba tare da junansu ba. All tribes have an issue with each other ba wai tsakanin Igbo da Yaruba ba ne kawai, ƙalubalen farko da suka fara fuskanta a soyayyarsu shi ne ta ya zasu tunkari iyayensu da batun aure, duba da irin yaƙin da ke tsakanin ƙabilu biyun musamman idan aka zo ga ɓangaren sha'ani na aure. domin galibin iyayen ƙabilar Igbo ba sa goyon bayan ƴaƴansu maza su auri mace a wajen ƙabilarsu, an sha gumurzu kafin iyayen mahaifina su yarda ya auri mahaifiyata, sai dai duk da hakan sai ya kasance mahaifiyata bata jin daɗin auren saboda tsangwamar da Kakata ke mata, su ƙabilar Igbo in basa son abu to basa so, idan kuma suna so babu wanda ya kai su so, ta kai ta kawo har iyayen suka yi fushi da mahaifina suka kore shi daga gida, sai Baban Mahaifiyata ne ya ba su wuri, shi yaci gaba da tallafar al'amuran mahaifina tamkar ɗan cikinsa har ta kai ga matakin da ya shiga ya fita ya samar masa aikin soja, dalilin wannan karamci da halacci mahaifina ya sakaya sunan sirikinsa a jikin sunansa, madadin Sadiq Chibuzo Ibrahim sai yake amfani da Sadiq Ibrahim Oluwa, duk wasu takardun aikinsa da wannan sunan yake a amfani kuma da shi duniya ta sansa, sai bayan an haife ni ne aka samu fahimtar juna tsakanin mahaifina da iyayensa har suka yarda ya koma garesu tare da matarsa, lokacin da suka koma Anambra state an yaye ni sai aka bar ni wurin Maman Mamata, suka tafi da Yayana Chibuzo me sunan Kakanmu. na taso cikin soyayya da kulawar Kakana shi yasa nima na ke amfani da Salim Sadiq Oluwa kamar mahaifina madadin Salim Sadiq Chibuzo, sunana na yare Onochie don ko a garinmu da wajen aiki duk haka ake kira na. Papa mutum me mutunci sosai da sosai, ba ya nuna banbancin ƙabila don ko lokacin da Baban su Safiyya yaje neman auren Mamanta wato ƙanwar Mahaifina shi yay conviecing Kakana amma da ba za su taɓa bawa bahaushe auren ƴarsu ba".
Ya numfasa kafin yaci gaba,"Mahaifina babban soja ne, kuma nima soja ne aikina yafi kai ni cross river da Ebonyi, a baya da na zo gare ki da batun aure ne a matsayin saurayi, amma a yanzu ni É—in me iyali ne, nayi aure da matana É—aya Kudrat, tare da yarana uku Rofi'at, Isioma da kuma Foridat, ni da su dukka muna zaune a barrack É—in Edo state".
Sai yay shiru ya É—ago yana kallona, nima shi É—in na ke kallo da tsantsar mamaki, so na ke na auna bayanan da yake min domin kuwa na kasa fahimtar dalilin yi min su, ina ce zuwa yay kawai mu gaisa? Then why this information all of a sudden?
"Abbaa ya faÉ—a miki dalilin zuwana wajen ki?".