← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 113

Sashe 42

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da na taɓa faɗawa su Malama Alawiyya na taɓa aure ƙaryata ni suka yi wai wallahi kwata kwata ban kama da wacca tayi aure ba, kar nayi wasa da damata na amincewa Malam Isah kawai tunda shi ba ƙaramin yaro ba ne da gaske aurena zai yi babu wasa a maganarsa, ni dai kawai nayi murmushi ban ce musu komai ba saboda Allah ɗaya ya san me na aje a zuciyata dangane da aure wanda ya fita gaba ɗaya a raina, ana hakan kuwa watarana sai Malama Aisha ke cewa ashe da gaske ne ni bazawara ce taji a staff room ɗin Malamai maza ana maganar wai Malam Isah yaje neman aurena ance masa na taɓa aure to yanzu ya janye maganarsa don bai san mene dalilin fitowar tawa ba, shi ne har Malam Amiru ke cewa dama baka shaidar mutum ta fuska, amma ƙila ganin ina da ƙuruciya ne yasa na kaso auren na fito ba zai wuce talaka na ke aure ba abun duniya kuma ya rufe min ido.

Maganar ta tsaya min a rai, da na faÉ—awa Ummani tace ai sai na toshe kunnena akan maganganun mutane.
Yau na dawo daga makarantar na samu wata Kakarmu ta zo, ban ma san da zuwan nata ba don har sai da nayi sallar magriba na fito zan ɗauko abincin rana a kitchen Ummani ke ce min idan na gama cin abincin na shiga ɓangaren Baba Tijjani na gaida Gwaggo Marka.
Aje abincin na yi na ce bari na fara zuwa mu gaisa, ina zuwa kuwa na sameta cikin jikoki ana ta hira, da murnarta ta tarbe ni muka gaisa, take min jajen mutuwar aurena wanda sai da ta zo yaune ma take ji.

Sai kuma ta shiga bani baki da shawara akan da na samu manemi nayi aurena kar dalilin mutuwar wannan in ce ba zan kuma aure ba, Umma ta sako baki tana faɗa mata ai ni da iyayena mun ci buri ba lallai na ƙara yin wani auren ba, don ko yanzu haka anata zuwa wajena ma bana fita Abbaa kuma ya ɗaure min gindi da kansa yake fita ma ya sallami mutum.
Ai fa sai Gwaggo Marka ta kama faÉ—a sosai akan abin da Abbaa yake yi sam bai dace ba, idan shi bai sani ba ai ni suke zubarwa da mutunci, ni dai tana farawa hawaye tuni ya fara suntiri bisa kumatuna wanda na jima ban yi ba, tace na tashi muje can taji daga bakin iyayen nawa mene dalilin hakan kuma mene ribar hakan?

Muka tafi da ita muna zuwa ta komar da faɗan kan Ummani wai wannan ba dacewa ba ne, ashe auren nawa ma sune suka shiga suka fita suka tilastawa mijin nawa ya sake ni. Sai da ƙyar Ummani ta fahimtar da ita shi ne fa ta sassauta murya kuma ta dafa kafaɗata ta shiga lallashina.

Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare da iyayena, ina aiki ina sana'ata ya fiye min wani aure, tuni na cire sha'awar aure a raina da tunani duk wani ɗa namiji.
Sai ta kama ce min ai zancen hakan ma bai taso ba domin akwai lokacin da zan zo da kaina ma ina buƙatar in yi auren, don haka gwara nayi abuna tun da ƙuruciyata ba sai lokaci ya ƙure min ba, amma ita zata fi so ma ace na komawa tsohon mijina idan an sasanta akan na kuma wani auren daban, a cewarta gwara na komawa wanda na riga na saba da shi na san halinsa, na ce Gwaggo Marka ba za ki gane rayuwar da nayi a gidan Nazifi ba ne shiyasa kike batun sasanci.

Ni dai haka na baro ɗakin Ummani ina ta faman hawaye, ban ji daɗin fama min ciwon da Gwaggo Marka tayi ba, tuntuni na haƙa rami na binne Nazifi da duk wani abu da ya dangace shi amma shi ne yanzu take min maganar wani wai na koma masa, ai abun da ma ba zai yiwu ba kenan da waninsa ma ballanta shi.
To a ƴan kwanakin da Gwaggo Marka tayi a gidan sai naji duk gidan ya ishe ni na gaji, ba don komai ba sai don takurawar da tayi min akan maganar aure yanda kasan auren nawa ya shekara dubu da mutuwa, na rasa irin wasu mutanen da kambaba abu, ta matsawa Abbaa ma akan lallai sai ya ƙyale ni na fara sauraron zaurawan da ke ta suntirin zuwa gurina, shi kuwa yace ai zaɓin a wurina yake idan ina so ai zan sanar da su da hankalina kuma na san inda ke min ciwo, sai ce tayi a'a ai har yanzu ni yarinya ce da ƙuruciyata dudu shekaruna nawa suke, kuma kar ya manta mace ma sai ta shekara arba'in take fara tunani irin na ɗan shekara bakwai.
Duk haushinta ya tuƙe ni na ƙosa ta tafi ta bar mana gida, ga shi kome tace sai Kaka ya ara ya yafa dama ƙanwarsa ce, ranar ina jin Abbaa na yiwa Ummani ƙorafin shima ya fara gajiya da maganarta sai kace ita ke ciyar da ni ko kuma ina zaune ne akanta, Ummani tace yay haƙuri kwana nawa ne ma ya rage ta tafi ana gama bikin Hindatu ne.

Ni kuwa dalilin haka sai na tattara kayana na tafi gidan Yashaik, tun da ba dama ayi sallama ace Sa'ida tazo zata ce da yaro jeka kace tana zuwa, kuma ba yanda na iya dole sai na je.
Sai da daddare ne Yashaik na ta zuba idon yaga na fito na tafi Maman Yasmin take faÉ—a masa dalili yace to shikenan ai babu komai, har yake tsokanata yana cewa shima dai akwai wani ogansu a wajen aiki yace zai zo mu sasanta amma tsoho ne don zai yi shekara 70 sai dai akwai dukiya.

Maman Yasmin ta kama cewa,"Allah ya kiyaye ya suttura can yaje wani wajen".

"To ya idan ita kuma tana so fa?".
Nayi saurin cewa,"Bana so ma Yashaik".

Yaro ne yay sallama da cewa wai Sa'ida ta zo a waje, kaina na ƙasa na kama mamaki tunda dai ai Ummani ce kawai ta san ina nan, Abbaa kuwa wai ba zai zo yace masa yazo nan ba, to ko Gwaggo Marka ga sani ne?
Yashaik ya dube ni yaga ban kai hankalina wurin ba tamkar ba sunana aka shigo aka ambata ba. Ya lura dai da gaske na ƙi jinin Maza yanzu.

Sai naji yana cewa da ni,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?".

Na girgiza masa kai da cewa,"A'a".

Hannunsa ya tsame a cikin kwanon abincin da yake ci. Maman Yasmin ta zuba masa ruwa ya wanke hannu yasa hularsa ya fita.
Daga ya leƙa yaga waye kuma shiru bai dawo ba har aka yi isha'i, muka yi sallah muka wuce ɗaki.

Maman Yasmin ta shigo tana cewa da ni,"Sa'ida kin ga Abban Yasmin shiru tun fitar da yay".

Na É—ago kai ina barin linke kayan yaran da na ke yi na ce,"To ko kiran wayarsa za ki yi".

Tace,"Ai kinga wayar tasa nan ya barta, ko kuma can gida ya wuce, Amma dai da can É—in ya tafi sai ya fara shigowa ya faÉ—a min, kinga ba sabonsa ba ne kaiwa haka a waje".

Tashi nayi na sanya hijabina na ce,"Bara na leƙa mu gani".

Ina fita ƙofar gida naga ba ya nan, sai na tsallaka wajen masu kankanar ƙofar gidan ina tambayarsu ko sunga wucewasa sai yake shaida min yaga sun fita shi da wani a machine.
Ban koma ba na wuce gida, naje ma Ummani ta kama min faÉ—an na fito da daddare, na ce to ya zanyi naje gidan mata mijinta ya fita a dalilina muma shiru bai dawo ba, tace to shi É—in yaro ne da za'a kama wani cigiyarsa.

Sai tace ba zan koma na lallamata ta bar ni na fice Abbaa ma bai san naje ba. Na koma na faÉ—awa Maman Yasmin É—in tana dai falo ta kasa zaune, kawai sai na tuna nima haka na ke fa idan ya fiata ya jima bai dawo ba, kai na girgiza na koma É—aki na barta anan a raina ina cewa duk inda yake ma ai zai dawo.
Shiru shiru kuma har sha É—aya da kusan rabi Yashaik bai dawo ba, munyi jugum jugum lokacin don sinitin Maman Yasmin ya hana ni bacci har sai da naji inama ban zo gidan ba.

Can muka ji ƙarar adaidata sahu a ƙofar gida, haka muka yi rige rigen fita ni da ita, yacca ya ganmu hankula tashe sai ya kama dariya yana cewa muyi haƙuri, to yanayin da muka gansa cikin farin ciki sai hankalinmu ya kwanta amma duk mun ƙosa muji ina yaje.

Nan na bar su shi da Maman Yasmin na shiga ɗaki. Washe gari da safe na gama shiryawa zan wuce makaranta sai Yashaik ya kira ni, na zauna gabansa yake faɗa min jiya ai Nazifi ne ya zo wajensa. Gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba na ɗago ido ina kallonsa da jiran jin ƙarashen zancensa.

Kuma lokaci ɗaya na tafi tunanin kwana biyu kenan da muka haɗu da Nazifi ina kan hanyar dawowata daga kasuwar rimi naje na siyowa Ummani kayan zoɓo.
Ni na fara ganinsa a cikin mota na zo tsallakowa titin layinmu ashe shima ya ganni, ya fito daga motarsa ya biyo ni ta cikin layin da na shigo ina ta sauri ƙafata har harɗewa take yi kamar zan faɗi.

Ya sha gabana yanda naga idanuwansa sai na rikice a raina haka kawai naji ko shaye shaye ya fara yi, ni dai tsoro duk ya cika ni na ture shi daga gabana ina cewa ya bani hanya, sai ya ruƙo hijabina yana faɗin na tsaya na saurare shi ba abin da na ke tunani ba ne ya kawo shi wurina.
Chapter 42 · 0% Book details