Sashe 94
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban kasheta ba, wallahi ba ni na kasheta ba".
Abin da na faɗa kenan na fita a ɗakin kamar zararriya, kamar mahaukaciya haka na koma, ina shiga ɗakina na zube a ƙasa na cire ɗan kwalina nayi wurgi da shi don wani zafi na ke ji ta ko'ina a jikina, kai na ke girgizawa ina ta maganganu ni ɗaya. Duk da sanyin gari amma haka zufa ke tsatstsafo min kamar an watsa min ruwa, da Allah na dogara kuma shi kaɗai zai fidda ni daga taskon da na faɗa.
Rumana ta zo ta rungumo ni jikinta tana kuka itama, sai tasa ɗan ƙaramin hannunta tana share min hawaye tace,"Antyna ki daina kuka, ba na so inga kina kuka".
Kalamanta sai naji tamkar É—an cikina ne ke faÉ—a min, bani da wata kafaÉ—a da zan kwantar da kaina nayi kuka a cikin gidan nan, ita É—in kawai na ke da, sai na kama hannunta itama ina faÉ—a mata ta tayani gaya musu bani na kashe musu Æ´a ba. Allah sarki uwa kamar ta san halin da Æ´arta ke ciki sai ga kiranta ya shigo wayata, ban iya É—aukar wayar ba sai Rumana ce ta É—aga tasa min a kunne.
"Sa'ida ya naji kamar kina kuka".
"Ummani, Ummani ki zo don Allah, ku zo ku cire ni daga wannan bala'in".
"Hasbunallahu wani'imal wakil, me ya faru haka, me ke faruwa Sa'ida? Ke da wa?".
Wani irin numfashi na ke yi me wahalarwa na kasa maganar gaba ɗaya, tana ta tambayata sai Rumana ce tace,"Ummani Anty Amarya ce". Sai naji Ummanin na faɗin,"Sa'ida kishiya kike yiwa kuka?". Kaina ya lanƙwashe ina jin numfashina na neman ɗaukewa, muryar Abbaana da naji ita ta saka na buɗe ido.
"Sa'ida! Sa'ida! Ba ki da lafiya ne? Menene?".
A hankali muryata kamar ba tawa ba nace,"Abbaa ba ni ba ce wallahi, ban yiwa Æ´arsu komai ba Abbaa, Allah ne shaidata bani na kasheta ba amma sun É—ora alhakin mutuwarta akaina, Abbaa ku zo ku taimaka min ban san me za su yi min ba".
Muryan Abbaan a zabure naji ya furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Sai ƙit naji an kashe wayar. Kaina dai na lanƙwashe a kafaɗar Rumana wacce ke riƙe da hannuna tana ta aikin goge min hawaye, ƙwayar idona ƙafe take a wuri ɗaya. Hawayen ma sun daina zubo min sun ƙafe, na zama dai gani nan kamar me rai kamar mara rai, ai na san zamana da Nazifi kuma ya ƙare, to amma ta ya zai barni haka nan? Sakina kawai ai ba zai sa ya huce baƙin cikin da yake ganin na haifar masa ba, to me zai yi min wanda yake ganin ta nan zai ɗauka fansa?
Bani da wani abu da na ke matuƙar so sama da mutuwa a wannan lokacin, ina raye bana raye Allah zai wanke ni na sani. To amma rayuwar na gaji da ita, bana so na ƙara kwana a duniyar nan, da ace nayi haƙuri ban zaɓi Nazifi sama da burin Abbaana ba da ban tsinci kaina a bala'in rayuwa haka ba, danasani ban fifita farin cikin Nazifi akan na iyayena ba, ina nadamar fifita soyayyar Nazifi sama da samarwa kaina rayuwa me inganci.
Kusan kamar bayan minti goma haka aka turo ƙofar ɗakin, sama sama na ke jin komai, idan ka ganni zaka tsammaci nayi dogon suma ne.
"Bata nan ne?". Naji maganar a tsakiyar kaina amma ban iya motsawa ba, ban kuma shaida muryar ba, sai dai ko wace ma bata gane ni ba ce tunda na bata baya. "Gata nan". Rumana tace da ita, duk wani taku nata da nake ji ina jinsa tamkar ana gutsirar naman jikina.
Rumana ta gaida ita tana amsawa lokacin da take zagowa gabana, ta duƙa tana tambayar,"Lafiya dai ko?".
Ni dai kallonta kawai na ke yi da ƙwalalan idanuwana irin wacca aka sassaƙa aka dasa, Anty Naim ce maƙociyata, gaba ɗaya layinmu da ita muka fi mu'amala, Farfesa ce a ABU take lakcarin, tana da kirki sosai don ta kan shigo musha hirarmu da ita, ni ce ma ban fiya shiga gidanta ba, farko farkon zuwana ma har yaranta take turo min. Da aka yi haihuwar nan ne na shiga gidanta na faɗa mata sai yaranta suka ce min ai ta jima bata gari.
Hannu ta kai ta taɓani, naga tayi saurin janye hannunta, ko bata faɗa ba na san ji tayi tamkar ta saka hannun nata ne a garwashi, don ni kaina zafin jikin nawa ƙona ni yake yi. " Subhanallahi Sa'ida ba ki da lafiya ne haka?".
A hankali na ce,"Anty Naim ina wuni".
Tace,"Aa ina batun gaisuwa ina ganinki a haka, me yake damunki. Kuma babu kowa a gidan ne naga sai ƙaramar yarinya tare da ke, me zata iya yi miki wannan, tashi muje asibiti".
Tayi maganar cike da kulawa da nuna damuwarta, Wahaltaccen yawu na haɗiye na ce,"Ai lafiyata ƙalau, nima ban san me yake faruwa ba Anty Naim, ban san me yasa ƙaddara ke ta ƙwallo da ni ba".
Kallona ta tsaya yi kafin tace,"Wata matsala ce Sa'ida?".
Kamar wata susutacciya na kaÉ—a mata kai nace,"A'a babu komai, kawai dai Anty Naim, Ki zauna mana akan gadon".
Yunƙurawa tayi ta zauna bakin gadon tana ta dubana da nazari. Na daɗa cewa,"Kin zo ba zan iya kawo miki komai ba, idan na tashi ƙirjina ne zai faɗo zuciyata ta fito kiyi haƙuri".
Sai ce tayi,"Kai akwai matsala, kira me gidan naki a waya a shaida masa zan kai ki asibiti, zafin zazzaɓi har ya kai ki ga yin surutai".
Ta fada tana cicciɓata ta matsar da ni bakin gado na jingina a jikin gadon, don ce mata nayi ban san ta yanda zan tashi ba, ban san yanda ma ake tashin ba.
Rumana ta kawo mata ruwa ta ajiye. Bata bi ta kan ruwan ba tace,"Na dawo tun wancan satin Yara ke faÉ—a min Amaryar gidan nan ta haihu, har ma kin shiga ki faÉ—a min kika samu bana nan, to fa ina ta cewa zan shigo kinga sai yau Allah yayi".
Idona a gefe ɗaya na ce,"Ehh Anty Naim, wata ɗaya ma kenan. Amma na kashe ɗayar yanzu, na kashe musu Ƴa Anty Naim".
Ai kana jin yanda nayi maganar ma kasan ba'a hayyacina na ke ba.
Ita kuwa da sauri ta furta,"Auzubillahi kisa! kin san me kike faɗa kuwa, Sa'ida ba ki cikin hankalinki duk yanda akai, akwai matsala ni ba wacca za ki ɓoyewa ba ce, mene yake faruwa?".
Sai na kama cewa da ita,"Ai bani da hankali Anty Naim, bani da shi, ya ƙare. Na kasheta na kasheta, amma ban san ta yanda ta mutu ba".
Jin ina maganar zararru sai ta toshe min baki tana cewa da Rumana ta dubo lambar mijina ta faÉ—a masa. Ni kuma sai ce mata na ke yi,"Anty Naim ki taimaka min zuciyata na ke so ki cire min, idan aka gama soyata a waje sai ki mayar min kinji, wayyo jikina ma ki watsa min ruwa me sanyi kinga duk na babbake, kuma don Allah ki taimaka ki kaini inda za'a ciro hotunan da ke cikin idona a nunawa Nazifi ya gani, so na ke ya gani idona ai ya É—auki hoton komai".
Ido na rumtse ina dafe saitin zuciyata, kafin lokaci ɗaya kuma saƙuwa ta sarƙe ni.
"Ruwa! Ruwa Anty Naim, zan sha ruwa Anty Naim, ki ban magani ƙirjina zafi yake min".
"Anty ga ruwan". Rumana ta faɗa tana kafa min kofin a baki, tun da na kafa baki sai da na shanye, tana saukewa nace ta ƙara min, nan ma na kuma shanyewa na ce su ƙara min, Anty Naim tace ya isa haka.
Roƙonta na kama yi akan ta taimaka ta kira min Ummani da Abbaa su zo, su zo yanzun nan, su zo da likitan da zata tashi Noor da ga baccin da tayi, Noor suma tayi amma taƙi tashi, kuma a zo da wanda zai ciro idona a nunawa Nazifi hoton komai.
Ruwa ta watso min a fuska na firgita ina ƙanƙameta jikina sai rawa yake yi.
[2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR14FT5*
Cikin tsananin tausayina Anty Naim ta kewaye ni jikinta. Idona akan Rumana na ce,"Rumana kirawo min Abbaa".
Anty Naim tace,"Sa'ida za ki É—aga musu hankali, barsu tukunna. Duk da ban gama gane kan Al'amarin ba amma kamar kina magana ne akan yarinya ta mutu an ce kece ko?".
Kai na ɗaga mata ban iya cewa komai ba. Sai naji ta sauke gwauron numfashi. Nace mata,"Anty Naim da an kirawo min Abbaan nawa don Allah, shi zai faɗa min maganar da zan ɗan samu sauƙin ciwon da na ke ji a ƙirjina".
Wayar ta karɓa a hannun Rumana tana faɗin,"Yanzu shi ina me gidan na ki?".
"Yana É—akinsa ban san wanne mataki zuciyarsa zata yanke akaina ba".
"To wai Æ´ar mutuwa tayi ne ko me? ki nutsu ki min bayani".
Ido na rufe na ce,"Eyy Anty Naim mutuwa tayi kuma ni na kasheta haka Babanta yace, Babarta ma tace na kashe mata Æ´a, Kakarta ma tace na kashe mata jika".
Ni dai tun da na faɗi hakan kuma sai naji numfashina na karkatsewa. Waya naji an ɗora min a kunne wadda ko ƙararta banji ba, muryar Safiyya naji tana cewa,"Beb wayar Ummani na kira zanwa Abbaa ya jiki sai naji muryar kamar babu lafiya, na ƙara kiranta kuma bata ɗaga ba na dai ji tana mota".
Shirun da taji ta ƙara cewa,"hello Beb, Beb, Sa'ida bacci kike yi ne naji numfashinki na fita da ƙyar, ko ba ki da lafiya ne?".
Cikin wata murya da tayi daban da tawa na ce,"Safiyya ba ni ɗaya ce babu lafiya ba komai ma babu lafiya". Sai na fashe da kuka wanda ya katse maganar da take son ƙara yi, na ce,"Safiyya ɗayan yarinyar Nazifi ce ta mutu kuma sun ce ni na kasheta".
"Kutumar bura'uba kika kasheta kamar ya? Nazifi da matarsa suna shaye shaye ne? Me ma ya kawo zancen kin kashe musu ƴa, sun bugu ne, taɓa ƴar kika yi ko me?".