Sashe 59
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ya zauna daga waje yana jirana, suka zauna tare da wancan mutumin.
EHA Clinics Kano sunan asibitin anan Lamiɗo Crescent yake. Tsawon kwana biyu na ɗauka ana min gwaji wani babban likita ne me zaman kansa kuma bature ne ma, yawancin Drs ɗin duk turawa ne, nurses ɗin kuwa ƙalilan ne waɗanda suka yi karatu a nageria suma kuma duk ƴan private school ne. cikin ikon Allah kuma duba da ƙwarewata da ƙwazona suka tabbar da cewar sun ɗauke ni aiki tare da su, duk wata za su ke biyana dubu ɗari da casa'in.
Ni dai abun tamkar a mafarki haka naji jin salary amount ɗina, Cikin sati guda na fara zuwa aikin, Abbaa bai yarda da batun night duty ba don ce yay indai zan ke aikin dare to gwara a haƙura da aikin, ya saɓi ƙafa shi da Yaya Imam suka je har can suka ga managern wurin, ya roƙe shi yace masa suna son aikin amma in dai zan dinga aikin kwana to gwara na haƙura, amma idan sun yarda aiki ko ce suka yi na fito da asuba to shi zai rako ni ma kafin lokaci, ya yarda na yini acan ɗin amma shi ban da dare, da haka aka tsara roster ɗin morning and evening duty da ni banda night.
Sai da na jera sati guda Abbaa na raka ni kullum kuma idan lokacin tashi yayi shi zai je mu taho tare, har sun saba ma da mutanen asibitin, hatta managern kansa idan yaga zuwan Abbaa sai yace ya shigo daga cikin office É—insa.
Watan farko da na ɗauka albashina jiki na rawa na tafi na curo su, ɗari da casa'in cass kuma babu lissafin kuɗin mota da na abinci, suke bamu na mota duk sati abinci kuwa Ummani dafa min take na tafi da kayana. Naira dubu hamsin na cire na damƙawa mahaifiyata, na zare saba'in na damƙawa Abbaa, na kara cire arba'in na bawa Yaya Imam da Yashaik ashirin ashirin, Yaya Al'amin na ba shi goma sha biyar, na cire biyar na bawa Kaka shima, sauran goman kuwa na kaiwa Baba Tijjani da Baba Sabi'u, naira biyar ban sha'awar naci ba a ciki, don tun ranar da na samu aikin na gama kasafin kuɗin.
Aikuwa tsabagen adu'a da albarkar da aka dinƙa sanya min a cikin gidan nan sai da nayi kukan farin ciki. Har da su Umma aka zo ana taya ni murna nayi ta mamaki, na ce wato idan kana da shi sai ayi da kai, idan baka da shi baka kai ba ɗan iska kawai kake. Ummansu Hindatu ma kanta sai da ta faɗa tace,"Ai ko bata so ki don Allah ba yanzu ta soki don abin hannunki, kiga dai tun da kika dawo fa bata saurareki ba".
Ummani tace,"Allah dai ya kyauta kawai".
______________________________
*_Tambayar da zan yi muku, duba da irin rayuwar da Sa'ida ta fuskanta a gidan tsohon mijinta, mu ɗauki matsayin hakan a zahirin rayuwa, babu yanda ubangiji ba ya lamarinsa, shin kuna ganin ubangiji zai iya ƙadartawa ta komawa Nazifi? A bar shi wataƙila yay nadamar abubuwan da ya aikata, sannan yana cikin hali na a tausayawa masa duk da bamu da tabbacin hakan don yanzu bamu san wacce rayuwa yake ciki ba, ko kuma ace ma Allah ya barsa da dukiyarsa amma kuma yay danasani da nadama yana neman dawo da Sa'ida gidansa, kuma mu ƙaddara wataƙila yana da sa hannu a wancan ɗawainiya ta karatunta, haka itama ɓangaren Sa'idan ta zaɓi komawa gare shi...idan hakan ta kasance ya zamu ɗauki al'amarin dukkan mu? Ko ma dai a ganinmu kwata kwata lamari ne da ba zai fara somuwa ba? Kuma a tsumayinku da tunaninku wanne kalar miji Sa'ida zata ƙara aura tun da dai ba zamu so ta ƙare rayuwanta a zaman zawarci ba....ina jiran jin ra'ayoyin ku akan hakan_*
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR02FT5*
Ƙaramin yaro ya shigo gidan yana cewa,"Salamu alaikum a bada zoɓo".
Ummani da ke daga cikin É—aki tace,"Ana zuwa". Ta fito daidai lokacin tana tambayarsa,"Na nawa?".
"Na É—ari, wai don Allah a bada na roba me kyau".
Tayi murmushi tana cewa,"Ai duk masu kyau ne". Tana saka masa cikin leda wani yaron ya kuma shigowa yace,"Akwai kunun aya?". Tace,"Babu sai gobe idan Allah ya kaimu".
Ta sallami me zoɓo Kaka yace mata,"Me yasa ba ku yi kunun ayar ba bayan kun san anfi son sa".
Tace,"Jiya ne Sa'ida ta dawo a gajiye bata samu damar yi ba".
"To amma ke da ba sai kiyi ba".
"Kaka hannun jikar taka sirri ne da shi, akwai zaƙin hannu idan tayi wallahi yafi nawa daɗi".
Kitchen ta shiga ta ɗauko abinci a ƙaramin filas tace da Kaka,"A shigar maka da shi cikin ɗakin ko anan zaka ci?".
Ya gyara zama daga kishingiÉ—en da yake yace,"Bar min anan cikin É—akin zafi, nepa sun hana wuta yau".
Ta ajiya masa ta ɗauko ruwa ta aje masa, shi kuma yana ta saka mata albarka don shi kansa kaf matan ƴaƴansa yafi son Ummani, a ko da yaushe yabonta yake yi domin ita ɗin macece ta ƙwarai, yanda take masa tamkar shi ya haifeta.
Yashaik ya shigo gidan, a nan tabarmar da Kaka yake ya zauna suna gaisawa, kafin daga bisani ya miƙe ya shiga ciki wurin mahaifiyarsa.
Samunta yay ta fito da kayan sif É—inta dukka tana linkewa, daga gefe ya zauna yan agaishe da ita ta amsa tana tambayarsa ya iyali.
"Me makon ki aika a kira miki Maman Yasmin, yanzu ina ke ina aikin ninkin kaya masu yawa haka".
"Ku dai kun fi so kuyi ta gani na kwance sharaf wuri É—aya bana aikin komai, haka kawai kuma yarinya na can gidanta tana aikinta sai na aika a tasota, a'a kayan nawa suke gaba É—aya yanzu zan gama ai. Yau babu in da kaje kenan?".
Ya sauke numfashi yace,"Ban leƙa ko ina ba, gani nayi gwara in ke hutawa lahadin jiki na buƙatar hutu".
"Haka ne, Allah daÉ—a rufa asiri. Jiya naji ka ce zaku yi magana da Abbaan ku sai ban ga ka dawo ba shiru, ba dai wata matsalar ba ce ko?".
Ya kai hannu yana shiga tayata linkin kayan yace,"Da na ƙyale ne kawai saboda na san ko naje masa da zancen ba karɓa zai yi ba, wataƙila ma raina ya iya ɓaci, sai dai ko ke za ki faɗa masa".
Ummani ta mayar da hankalinta kansa sosai tace,"Menene fa?".
Yace,"Ba fa matsala ba ce". Ya faÉ—a yanda yaga mahaifiyar tasa ta kafe shi da idanu.
"Dama akan Sa'ida ne ban san me Abbaa ke hange ba da yaƙi bawa zaurawan nata dama, haka kuma gaba ɗaya bai son zancen auren nata ba, amma ni gani na ke bai kamata a biye mata ba, duk da cewar dole auren ya sire mata, amma ai ba zamu ɗauka cewa lallai abin da ya faru a farko shi zai kuma faruwa ba ko kuma yayta maimaituwa, kawai ta ɗauka hakan matsayin jarabawarta ba wai saboda dalilin hakan kuma tace ita ba zata ƙara yin wani auren ba. ita macece ko ai na take ko me take yi duk matsayin da take da shi da aurenta tafi daraja a idon duniya, kuma ku kan ku idan da aurenta hankalinki zai fi kwanciya, kuma sannan shekaru tafiya suke ta yi gaba ba dawo baya zasu yi ba, nan da wata shekarar magana ake ta zata shekara talatin idan da rai da kuma lafiya, to ta gama karatun ta samu aikin yi me za'a ƙara jira Ummani? Baka biyewa maganar mutane balle ta dameka amma ana gudun baki, wani bakin kaifi ne sune masu kambun baka, ni gaskiya na fi ga sha'awar tayi aurenta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ta dage da adu'a kawai Allah kar ya maimaita mata irin mijin baya".
Ummani ta numfasa tace,"Ni kaina da ka ganni wlh yanzu hankalina yafi ga tayi auren, Sa'id idan ta fita aikin wannan wallahi sam sam bana samun natsuwa har taje ta dawo hankalina ba'a kwance yake ba, amma lokaci ne duk dai Abbaan naku na daƙile damar hakan, Allah dai ya kawo mata na gari ya musanya mata da mafificin alkhairi".
"To amin ya Allah. Kuma dama Nura ne yay min magana É—azu da safe yace abokinsa Ya ganta yace idan ba'a tsayar da maganar wani akanta ba ya gani yana so".
Ummani tayi murmushi me faÉ—i tace,"Allah sarki, ai na yake to?".
"A can garejin ma su yake shima, kin sansa ma sai dai ba za ki gane shi ba, amma da sallah ƙarama tare suka zo da Nuran ai".
Tace,"To madallah, ai ina ga sai kace masa ya tunkari Abbaan na ku da maganar ko, ya gwada tasa sa'ar ko a kansa dacen yake".
"Ehh to dama ni abin da ma yasa ban masa maganar so na ke na fara bugar cikinta naji ko tana da ra'ayin auren me Æ´aÆ´a".
Ummani tayi gajeriyar dariya tace,"To ita wanne zaɓin saurayi ne da ita yanzu, sai dai kuma wani lamarin na Allah, fatan dai Allah bata wanda yafi wancan".
Da haka suka ci gaba da hirarsu akan maganar Al'amin ma da za'a kai kuɗin aure cikin satin nan, har sai da suka ninke kayan dukka. Shi ya share mata ɗaki ya goge ko ina, yay mata sharar tsakar gida da kitchen suma duk sai da yay mopping, dama sun saba hakan shi da Imam duk sanda suka sameta tana aiki, don shi da yake kusa da suma da sassafe yake zuwa yay sharar soro da ƙofar gida.
Bayan tafiyarsa yana zuwa gida kuwa ya aiko mata Yasmin wadda ta shigo tana ta ƙunci wai Kawu yace ta zo tayi wanke wanke.
Da yamma yaro ya shigo tsakar gida yana ta doka sallama babu wanda ya amsa, Ummani na daga cikin ɗaki a kwance kamar a mafarki taji sallaman wajen ƙofan ɗakinta, tayi saurin tashi tana cewa,"waye ne?".
Yaron yace,"Ai ko ni aka yi, wai ana sallama da me gidan".
Labule ta ɗaga ta leƙo tana cewa da shi,"To masu gidan ai da yawa, kaje kace wa ake nema?".
Ba jimawa ya dawo yana cewa,"Wai Malam Salman".
Ummani tace,"Tooo wallahi ba ya nan, amma kace musu yana kan hanyarsa ta dawowa ko zasu jira shi, suna da yawa ne?".