Sashe 105
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nace,"Amin zamu kai ma in Allah ya yarda, mu da har jikoki sai mun gani, magana ake ta shakara ɗari...Wa yaga surukai sun fara min suntiri a gidan nan, ina ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ina kallonsu ta cikin gilashi, Mahbub ba fa zan bawa yarana munana ba kar ma mummuna ya zo ka tsaya ce masa zaka yi shawara da ni matar gidan, ni dai ƴata me kyau zan aura mata, sai in Babar su Forida ce ban san ba ko ita zata aura musu mummuna, ita ka santa ƴar i dont care ce, ni Rofi'a ta me kyau ce kuma me kuɗi ɗan ƙasar waje, me irin halin Babanta. Yauwa kuma ka shiga tsakanina da Babar su Foridat da ke cewa yarinyata mummuna, zan iya shari'a da ita akan hakan, ba mummuna ba ce ni kuma ban haifi mummuna ba, ban kuma auri mummuna ba duk dai shima ba wani kyan garesa ba".
Aje laptop ɗin yay ya turmushe ni akan gadon yana rufe bakina da nasa, wai na cikasa da magana, kuma zan ƙara maimaita bai da kyau, muka shiga kokawa akan gadon kaman wasu yara, irin wasan da ban san da irinsa ba a baya, haƙiƙa ina son mijina sosai da sosai.
An sama min Harvard University ɗin, da zan tafi ni ɗaya na tafi don lokacin Salim na bakin aiki, naje kano na yiwa su Ummani sallama, Safiyya ma naje gidanta Allah sarki tana ta fama da laulayi, a gidan Hajjo na kwana, washe gari na je gidan Mama A'i kafin na dawo. Da zan tafi Maa da Sisters ɗinsa ne suka min rakiya airpot, Kudrat har da hawaye zan tafi na barta da kaɗaici, Rofi'a kuwa da ƙyar muka rabu yarinyar nan Mommy nah kawai take kira, to ni rabuwarmu da ita ne ma ya saka ni hawaye, ga shi Salim yace ba zai yiwu in tafi da ita ba.
Watana takwas a america muna gab da fara exams na kwanta rashin lafiya me tsanani, lokacin Salim yaje min satinsa uku kuwa da zuwa. Yaje ne musamman saboda taya ni murnar birthday, ƙarin shekaran ma da na mance sai ranar ga shi da gift ɗinsa, har ya kira min Yara vedio call na gansu da cake a gaba, Kudrat na cewa suma za su ci na u cake ɗin anan.
Ciwo fa ba na wasa ba na kwanta, abu tun ana zuwa asibiti ayi allurai a bani magunguna, ta kai da sai da muka koma haɗawa da tasa tasai iri iri duk sai da na gaji da ɓula ni da ake yi.
Ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa abu kamar ba zan rayu ba, Salim da ke ta son tafiya ya gagara tafiyar sai rubuta takarda yay a wajen aiki, abu dai yaga ba zai kai mana ba daman zaman exams ne ya riƙe ni haka dole na aje semester ɗin muka rankayo muka yo gida.
Wuya dai iyaka wuya ina shanta, na koma marabata da matacce numfashi kawai, don komai yi min ake bana iya yin komai da kaina. Hankalin iyayena ya tashi a wannan lokacin ne kuwa dole suka É—akko hanya suka aje kunya a gefe suka zo gidana, Mahaifiyata har da hawayen tausaya min, Abbaa nah kuwa don bai da yanda zai yi ne amma da sai ya zauna zaman jinyata, ga alkunyan iyayen Salim É—in da ke ta faÉ—i tashi akaina ba zai barsa cewa za su tafi da ni gida in jinyar a can ba, duk wanda ya ganni sai yace anyi gwaje gwaje kuwa?
Salim har ya rasa amsar bayarwa ya dinƙa yi, to babu kalar gwajin da ba'a min babu wani ciwo da aka gani ba, general checkup har sau uku aka yi min, a america sai da ya kashe sama da ɗari biyu akan general check up kawai, dama a can aka min sau biyu, ɗayan kuma sai da muka dawo nan.
Ciwo ya daɗa ta'azzara ina ta ƙarewa, lamarin ya bawa kowa tsoro matuƙa, sai da ta kai ga an koma yi min maganin islamic don na hausan ma aje shi aka yi, shima bai yi to, duk irin magungunan da yare ke da shi su kansu sai sallamawa suka yi. Sai aka fara tunanin wai ko sammu aka min, haka aka dinƙa banka min hayaƙi wani sai nayi kamar zan shiɗe, gidanmu ya koma gidan Malamai masu ruƙiyya, sauraron ƙur'ani kuwa 24/7.
Watana uku a kwance ina shan baƙar wahala, Mama A'i ita ta zo ta zauna da ni saboda hidimar ta yiwa Kudrat yawa, baiwar Allah nan ita ke min komai, bata samun hutu ga office ga ɗawainiyan yara, kai ai Kudrat ta wuci a kirata kishiya sai dai ƴar uwa, don ni a yanzu ma na fi jinta a jikina fiye da yanda na ke jin Safiyya, tun balle zuwan Ummani da ta mayar da ita kamar mahaifiyarta.
Nayi amai ta kwashe, na ƙara yi ta kwashe, ta bani abinci na kasa ci, shi Salim ɗin ma ta fisa ƙarfin halin jinyar tawa, saboda shi hankalinsa ne duk ya tashi gani yake kamar tafiya zan yi na bar su.
Wata rana ciwon ya tsananta min cikin dare haka muka É—unguma sai asibiti, muna tafe kan titi mota na jiniya matar laftanar ba kanta.
Da zuwanmu kuwa aka bamu kwanciya. Karon farko tun kwanciyar tawa da aka min allurai aka sa min drip naji daɗi, lokaci ɗaya wani salamman bacci ya zo min. An ce na jima ina bacci don tun cikin daren nan sai washe gari da rana na farka, farko suna zaton ma ko na mutu ne aka ɓoye musu, likita ya ce musu da raina yau ɗin ne dai aka yi nasara alluran baccin ya kama ni, kuma ƙari ma da daɗin jikin da na ɗan samu.
Naji daɗin jikin nawa kuwa, don da na farka babu ciwon cikin, babu inda ke min ciwo kwata kwata, sai dai rashin ƙwari da ɗanɗanon baki irin na wanda ya sha doguwan jinya.
Har ma na samu damar miƙewa zaune da kaina, muna hira da Mama A'i da wata Aunt ɗinsa da Kudrat sai ga shi ya shigo ɗakin, Allah sarki shima duk ya faɗa sosai sai dai yanayin fuskansa bai nuni da damuwa a washe take.
Mama A'i da Aunty Adamma suka tashi suka bamu wuri, Kudrat zata fita ya ruƙo hannunta, kawai sai ya faɗo jikina ya rungume ni sosai yana faɗin,"Myyy Congratulations, Congratulation to us Myy".
Kuma faÉ—in nasa yay daidai da tsala ihun murnar da Kudrat tayi tana buga tsalle ta dire bayan gama duba takardan da ya bata, sai gata itama ta faÉ—o jikina sun rungume ni gaba É—aya sai murna suke. Ni dai mamaki ya kamani kaina ya É—aure, murna a halin da na ke ciki? a hankali na ke tambayarsu menene.
Kudrat ta ɗago a jikina tana faman juyi da takarda a hannu, na bita da ido kafin ta miƙo min hannu tana cewa,"Kinga ban tukwici tukunna". Sai na ɗauke ido akanta na maido kan fuskar Salim da ke ta kallona kamar zai cinye ni.
Kudrat ta zagayo ta bayansa ta kama kafaÉ—una tana girgiza ni cikin wani irin farin ciki.
"Ki yi murna mana, kin fa warke Mommy, ki sakko ki yi tsalle muyi rawa, ciki ne da ke har na 5months, za'a ma mummuna ƙani ko ƙanwa". Sai tayi shiru kafin ta ƙara cewa,"Amma dai sai na ranƙwashi kan Babyn nan, ya san shi ne yaƙi bayyana kansa yake ta wahalar da mu, sannu Mommyn Rofi'a, tumbin da na ke ta yiwa tsiyan yana cin maiƙon America yana girma ashe Babyn mu ne a ciki".
Hannun Salim cikin nawa yana shafawa ina ga tsabagen farin cikin da yake ciki ne ya hanasa yin magana. Ni kuwa tuni na daskare ina ta kallon Kudrat na kasa wani motsi, sai a hankali idanuna ke ƙiftawa. So na ke na harhaɗo kalamanta in cure su wuri guda su bani ma'anar nufinta, don na kasa fahimtar komai daga abinda tace. babu abinda na gane kuma babu wata kalma da nayi capturing idan ba pregranant ba, Abinda na ke so na gane tana batun cikin wata biyar ko? To cikin haihuwa take nufi ko na cin abinci ko na me? Idan na haihuwa ne a jikin wa yake? Na san dai ba a jikina yake ba, idan kuma a jikin nawa ne to sai in wani cikin na daban ba na haihuwan ba, ina alamar samunsa ma? Ciki har 5month ba alamun fitowansa? To ba dai ni ba domin kuwa na shekara goma sha ɗaya a gidan aure na farko ban taɓa ɓatan wata ba balle ɓarin ciki, haka yanzu cikin aure na biyu ina a shekara ta uku ne kuma tun da na zo ni dai ban san lokacin da na yi ɓatan wata ba.
Fahimtata da suka yi ne yasa shi karɓan takardar ya miƙo min, na karɓa ina sauke ƙwayar idona akansa, sai ya ɗaga min gira yana cewa,"Ba ta yanda Allah ba ya lamarinsa, babu me haƙuri da tawakkalin da baya cin nasara, babu wanda ke miƙa lamarinsa ga Allah ubangiji bai dube shi ba, kuma mafi yawan jinkiri alkhairi ne, ga sakamakon jinkirin Myy, ga sakamakon haƙurin Myy, ga sakamakon tawakkalin Myy, dama na faɗa miki kar mu fidda tsammani, Allah ke bayarwa kuma zai bamu to ga shi ya ƙara bamu, ki gode masa Myy".
Duk da a daskare na ke amma na gane duk me ya ce, sai dai kuma kalamin nasa ne ba na tsammanin zuciya da ganganar jiki za su É—auka har su yarda. Na dubi takarda a hankali na shiga karanto bayanin da ke nuni da sunan Sa'ida Salman Madobi da ke rubuce a sama, tana É—auke da ciki har na tsawon wata biyar.
Naji na girgiza akan gadon da na ke, na rufe ido na buɗe, na ƙara rufewa na buɗe har sau uku, na ka kai hannu na mari fuskata kafin na mintsini kaina, ba zan iya gasgata abinda na karanta ba har sai na tabbatar da ba mafarki na ke yi ba tukunna.