← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 113

Sashe 55

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Leɓbansa ne kawai suka motsa, alamu na son yay murmushi sai dai hakan bai samu ba, domin kuwa a yau ɗin karo na farko da yake jin wani abu me kama da tsoro na kama shi, wanda a matsayinsa da sanin waye shi ɗin bai kamata tsoro ya nemi ya masa farmaki ba.
Ya miƙa hannunsa cikin motar ta miƙo masa face mask ya saka, ya ƙara gyara p-cap ɗinsa ya zuba hannayensa cikin aljihun rigar sanyin jikinsa, fuskarsa ta rufu ruf kamar mara gaskiya, ya sake leƙa kansa cikin motar yana duban Ƙanwar tasa da cewa,"Yayi?".

Haƙoranta na gaba suka bayyana dalilin siririyar dariyar da tayi, ta ce,"Ko ni ba zan iya shaidaka ba, balle kuma ita, duk da wani connection ɗin yafi gaban tunanin mutum".

Da dogon yatsansa ya lakuci kumatunta, sannu a hankali kuma ya fara takawa yana tafiya yana jin wani irin yanayi na shigarsa, farin cike yake, farin cikin da zai iya cewa ya girmi nata da duk wani masoyinta makusancinta.

Hanzarin tafiyarsa ya ƙara na gient ɗin namiji kamarsa. "Excuse me". Ya faɗa da amon muryar da ya fito da ɓacin rai, haka ma ɓoyayyar fuskarsa na bayyana zallar kishi da jin haushin mutumin da ya isa gabanta da niyyar taimaka mata ya karɓi trolly ɗin so that taji da jakunkunan hannayenta.

Mutumin yay saurin matsawa gefe yana ba shi haƙuri tsammaninsa ko me gidanta ne. shi kuma ya kai hannu ya kama hannun trolly ɗin, a hankali kuma a miskilance cikin harshen turanci yace,"Barka da dawowa". Ya faɗa ba tare da damuwar ta jisa ko bata jisa ba, shi dai ya amayar, fushinsa kawai akan me zata fito haka fuska a bayyane kowanne kare da doki ya ganta yajinta burge shi, and just imagine ta tsaya tsakiya idon kowa da ke wajen ya ƙare mata kallo kenan, babu ruwanta bata san marairaice fuskan da take yi ma ƙara fitar da kyawun halittarta yake ba.

"Mtssswww". Guntun tsaki ya fita a ƙasan maƙoshinsa, yana jin kamar ya zaro abar da ke cikin aljihunsa ya daki kanta da ita ko ta san da cewa kan hanya take tsaye ba cikin ɗakinta ba.

Ƙwayar idonsa ta manne a saman fuskarta da murmushin jin daɗi da farin ciki yaƙi ɗaukewa. Waya take yi da ahalinta tana faɗin,"Mun sauka yanzu amma ban hango kowa ba, kuna daga ina?".

Tayi maganar kaman zata yi kuka, wanda sautin hakan ya tafi har can ƙasan zuciyarsa ta motsa.
"To Abbaa sai ya ƙaraso Allah ya kawo shi lafiya".
Nayi maganar cikin rashin jin daÉ—i, domin ba haka na so ba, yanda na so ace ina sauka idona yay kwalli da mahaifiyata ko mahaifina, to amma babu komai tunda Yaya Imam da Yaya Al'amin É—in suna kan hanya, kuma na san duk yanda aka yi kuÉ—in mota ne ya hane su tahowa gaba É—ayan su.

Na kai hannu ga trolly É—ita sai naji an ja, nayi saurin É—ago ido in sauke kan dogon mutumin da ya fara takawa, da sauri na dakatar da shi da cewa,"Malam jakata ce".

Bai tsaya ba yaci gaba da tafiyarsa, ni kuma ina ta binsa cikin sauri ina ce masa jakata ce yay mistake ɗin ɗauka ne, sai dai ganin bai juyowa ba tunanina ya bani ko bai jin hausa ne tun da yanayinsa kamar ba na bahaushe ba, don haka cikin yaren turancin da ya samu ƙwarewa yanzu a kan harshena na ce masa,"Jakata ce fa kayi mantuwa".

Nan ma dai kamar bai jini ba, sai na ce to ko kurma ne, don haka muna shigowa cikin wata ƴar rumfa nayi saurin shan gabansa da niyyata na masa alama da hannu ya gane nufina. Bisa tsautsayi ƙafata ta gurɗe har na kai ƙasa dalilin ɗan tudun da na buga, wayata ta faɗi na saddaƙar da tayi raga raga, yunƙurawa nayi na miƙe na zauna kan kujerun ƙasan rumfar ina danne wajen da na buge idona a rumtse.

"Sorry please".
Buɗe ido nayi na gansa sunkuye gabana kaman zai kai hannunsa kan ƙafata wurin da na dafe sai dai kuma bai yi hakan ba, ya dai ɗauko wayata ya miƙo min.
Haka ɗaya naji ƙirjina ya buga sosai, irin bugawar nan da yake a lokacin da mutum ya shiga fargaba ko tsananin tashin hankali na saƙon mutuwa.

Wani sanyayyan ƙamshi ne ke tashi daga jikinsa ya ziyarci hancina, ban san dalilin da hakan ya haifar mini da haɗiye dunƙulallen yawu tare da jin motsawar zuciyata, kuma lokaci guda naji jikina yay sanyi, hannu na miƙa na karɓi wayar ina faɗin,"Thank you".

"Sannu". Ya sake furtawa muryansa can ƙasa.

"Na gode. Dama jakan da ka É—auka nawa ne ina ga baka lura ba ne".
"Na sani, na taimaka miki ne".

"Hope ba ki ji ciwo ba?".

Ina duba wajen na ce,"Ban ji ba".
"Sorry na taimaka miki ba tare da izininki ba".

Sai yanzu ya ɗago kansa wanda na san ya kalle ni ne ta cikin baƙin gilashin da idanunsa ke rufe a ciki, babu ta yanda zan iya ganin fuskarsa domin kuwa face mask ya ɓoyeta. Me na ke ji ne? Tamkar na san muryarsa, anya kuwa! Ta ya hakan ma zata kasance?
Tunanin da na ke ya yanke ganin ya miƙe yana barin wajen da sassarfa.

Na bi bayansa da ido ina kallonsa, ban san me yasa na ke ganin kamar na taɓa ganin me tafiya irin tasa ba, ba ya ga nan ma ga muryarsa da na ke da tabbacin na taɓa jinta, haka ƙamshin ma kamar na san shi? Sai dai duk me yaja bugawar ƙirjina akan hakan? Waye shi ɗin?
Tambayar ƙasan ran nawa ta haɗe da saukar ƙwayar idona akan bayan rigarsa da ke da tambarin S a jiki, ni dai har ya ɓacewa ganina ban ɗauke idona da tunanin wani abu akansa ba.

Wayata na cire key na danna lambar Safiyya, tana É—agawa tace,"Beb ina ta kiran wayanki ban samu".

Na ce,"To ai sai da muka sauka na mayar da sim É—ina na nan".
"Beb can't wait to see you, an dawo lafiya".
"Lafiya lau, ina Daughter nah?".

Sautin murmushinta ya fita da cewa,"Ga ta tana bacci, itama ai ta ƙosa taga Mum ɗinta, kina airpot ɗin ina ne yanzu? Kano ku ka sauka ko Abuja?".

"Muna Abuja". Sai yanzu ta ankare da yanayin fitar sautin muryata tace,"Beb lafiya dai? Yaushe rabon da naji muryanki a irin haka, menene?".

Na karyar da wuya ina ɓata fuska na ce,"Kinga fa basu zo ɗaukana ba, kuma tun jiya sai da na cewa Abbaa na tura musu kuɗi sai ce yay a'a akwai kuɗi, kuma yanzu mun yi waya ma yana ce min Yaya Imam ɗin na kan hanya bai ma ƙaraso ba, don Allah haka zan ta zama anan ni ɗaya babu wanda na sani, ga sauran nan duk ƴan gidansu sai ɗaukan su suke yi".

Na ƙarashe maganar idanuna na cika da ruwan hawayen da ke neman zubowa, kawai sai jin ihun Safiyya nayi a gabana ta faɗo jikina ta maƙalƙale ni, nima kuwa ban san lokacin da nayi mata wata runguma ba ina cewa,"Me yasa haka Beb, ni ki daina suprising ɗina irin haka".

Muka saki juna tana bina da kallo da cewar,"Sa'ida ke ce kuwa? Kin ga yanda kika koma na rantse da Allah kamar sake halittanki aka yi, wannan kumatun fa, naga ƙashin wuyanki ko yana nan".

Ta faɗi hakan tana ɗaga jesy hijab ɗin jikina tana aikin taɓa wuyana. "Beb ƙashin ma ya koma, kuturu yarinyar nan anya kuwa karatu kika je kika yi. Ko da yake ai result ɗinki kaɗai ya nuna ba wasa kika je kika yi ba, kin san duk wani handle ena na social media sai da na sa vedion result ɗinki, weldone ƙwaruwata za great first class".

Dariya na ke sosai cikin jin daÉ—i, ina dubanta na ce,"Amma ya akai kika zo nan?".

"Na san za ki dawo zan ƙi zuwa Beb, haba zance ne ai, muna nan Abuja ma fa tun last week Daddyn Amal ya zo seminer, jiya kina ce min zaku dawo yau kwana ne kawai ban ba a wajen nan, amma ina nan jirgin ku ya sauka na ce bari sai kin kira ni tukunna".

Ina dubanta na ce,"To mu tafi gidan ki idan Yaya Imam É—in ya zo ya same ni acan, ido yay min yawa duk na kasa natsuwa, kuma wani iri na ke ji, wanne turare ne a jikinki?".

Ta miƙe tana faɗin,"Turaren da kika ba ni lokacin da naje miki visiting...Ke bara dai na fara tofe ki da li'ilafi, Allah Beb gaba ɗaya kin wani sauya, wannan karan kam ai sai miji me tsadar gaske, mijin hawa jirgi sama duk watan duniya, mijin haskawa a tv mijin da ƙasa da duniya ta sansa in sha Allahu".

Ɓata fuska nayi. "Abeg na ce miki ki bar min zance irin wannan, mu tafi ni. Ina ma kika baro Amal ɗin wai?".

"Ke ni ban iya aikin dinƙa yawo da ita tana mota na barta".
Na waro ido ina ce mata,"What! Ƙaraman yarinyar za ki bari a mota, Safiyya wai ke kam yaushe ne ranar hankalin ki, ce na ke da kika yi aure kin saitu".

Na faɗa ina ƙara saurin tafiyata tare da tambayarta in da motar tasu take, dama na ƙosa naga Babyn nata don tun da aka haifeta ban ganta ba, sun dai je min ita mijinta lokacin tana fama da laulayi. Kuma can sai na hango Yaya Imam tsaye yana faman ɗaga kai shi da Yaya Al'amin, wani sabon farin ciki ya lulluɓe ni naji kamar na kwasa da gudu na ƙarasa wajensu.

Amma duk da hakan ban fasa gudu gudu sauri sauri ba ina ƙwala masa kira, na bar Safiyya da faman ƙwala min kiran da take yi tana ga motar tasu can, ina ce mata ga Yaya Imam ɗin can ya zo bari na je nemana suke. Ni dai ina zuwa tsananin farin ciki na kasa dakatar da kaina kawai na faɗa jikinsa da matuƙar murna.

"Ke dilla mene haka sakar ni mana, gaban mutane fa mu ke".

Yaya Al'amin yace,"Ah tou ba kun kaita turai ba, ta manta Æ´ar nigeria ce anan É—in ma bahaushiya".
Chapter 55 · 0% Book details