Sashe 5
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Murmushi yay wanda bai kai har ƙasan ransa ba ya ce,"Yayi mana Ƙanwata, ai yana da kuɗi kuma yana da ƙwaƙwƙwaran aikin yi, yana da wurin ajiye ki, zai iya riƙe mace kuma ko yanzu aka ce ya fito zai kawo lefe kuma a shirya biki cikin kwanaki ƙalilan, babban ma'aikaci irin wannan ba abun yarwa ba ne".
Na É—an juya idanuna ina daÉ—a jin wani iri cikin raina. Na dakatar da shi da cewa,"Yaya ni duk ba wannan ba. miji me nagarta na ke so, me ilimin addini, tarin kuÉ—insa bai dame ni ba, ni dai ya so ni kawai da dukkan zuciyarsa, in dai akwai rufin asirin da zamu ci musha mu zauna a kowanne irin muhalli ya ishe ni. Kuma kaga shi fa ban san ya halinsa yake ba, ban san É—abi'unsa ba, addininsa ya yake? Nagartarsa ya take? kuma su irinsu ka san matansu basa samun lokacinsu saboda irin aikinsu, ni kuma mijina lokacinsa, soyayyarsa, yardarsa da kulawarsa na ke biÉ—a. Ni Yaya miji irinka kawai na ke so kayi min adu'a Allah yasa shima haka yake".
Shirunsa yasa na É—ago ina kallon, na ce"Yaya". Sai kuma na rasa abun faÉ—a, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yace,"Kin san me?".
Na girgiza masa kaina alamar a'a.
"Ina tsoron rabuwa da ke ne Ƙanwata saboda nayi sabo da ke fiye da tunanin me tunani".
Na karayar da kaina na ce,"To me zai rabamu kuma? Aure fa kawai zan yi".
"Au aure ne ma kawai? Tunaninki mijinki zai yarda da alaƙarmu ne? A irin wannan shaƙuwar tamu? Ko ni ina tsananin kishinki balle mijin da za ki aura, Miji ma irin wannan mutumin, daga lokacin da kika yi aure Sa'ida duk wata alaƙa da ke tsakanina da ke ta rushe babu ita".
Tsorata nayi naja da baya saboda yanda yay furucin cikin huci. Yanayin kuma da ban taɓa ganinsa a ciki ba, kawai sai hawaye ya fara sakko min nasa hannu ina gogewa ina ce masa.
"Yaya indai baka sonsa zan haƙura da shi, ni bana son abin da zai rabamu".
"Ban zauna da shi ban san waye ba amma daga yanayin da na gansa ni kaina zan iya zaɓa miki shi, to amma bai yi min ba, idan na ce bana son aurenki da shi Ya za ki da su Abbaa?".
"Nima ban sani ba amma ba zan iya bijirewa zaɓinsu ba, zan faɗa masa ya ce musu ya janye. Yaya zan fasa aure in har alaƙarmu da kai zata taɓu".
Na faɗi hakan ina kuka sosai, kuma kawai sai gani nayi ya miƙe ya zura takalmansa ya fice.
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR04FT5*
_Not Edited, Plss avoid error mistakes._
________________________
Cikin sati biyu kamar yanda Abbaa ya yanke hukunci aka kawo lefena akwatu biyu maƙil da kaya, sai shinkafa kwano bakwai da dardumar sallah da ƙur'ani da littafan addini. ba ƙaramin ƙoƙarin Yaya Nazifi na gani ba, kuma sosai naji daɗi tunma da naji yanda ake ta santin kayan da ya zuba da yaba masa a irin ƙoƙarin da yay, a lokacin atamfa mai mugun tsada dubu biyu da ɗari biyar ce zuwa uku, kusan duk kayan da aka ɗaga sai Umma ta faɗi tsadarsu da ke ƴar kasuwa ce ita. Don haka murna ba ni ɗaya ba har da Ummani domin kuwa an bawa maƙiya kunya don kaf ƴaƴan Baba Tijjani da aka aurar ba wadda ta sami kaya kamar nawa.
To tun fa daga nan hidima sai ta ɓalle a gidanmu aka shiga shirye shiryen biki, shi Abbaa bai taɓa tsammanin Yaya Nazifi zai iya kawo lefe a ɗan ƙanƙanin lokacin da yanke masa ba, ya tauna tsakuwa ne domin aya taji tsoro, sai ga shi kuma yaga saɓanin tunaninsa, don haka a maimakon ya matse Yaya Nazifi sai ya zamana kansa ya ɗanawa tarko, domin kuwa dai a wannan lokacin ana cikin rufin asiri ne amma cikin jin jiki ake, sam bai da wasu kuɗin aurar da ni, na abincin gida ma da ƙaƙa ake samu, sai Ummani tayi cinikin lemo ake yin cefane da siyan abubuwan buƙata, ga lokacin jikin Kaka sai a hankali don haka duk wasu ƴan kuɗi da suka samo akan magungunansa suke tafiya, kuma kullum ana hanyar asibiti, don hatta kuɗin jarabawata na waec sai bashi Abbaa yaci ya biya acewarsa gwara na haɗa jarabawa duka biyun.
Ni dai sai ya zama gaba ɗaya bana cikin farin ciki, kamar ma ba wata amarya ba, na yi mugun shiga damuwa da ganin yanda iyayena duk suka takura, babu wani me walwala a cikinsu, ko da yaushe suna jugum sai walwalar ƙarfin hali da suke kawai. na shiga damuwa sosai hankalina ya ƙara tashi na rame domin kuwa Abbaa sam a lokacin banda gaisuwata da yake amsawa ba wani magana da ke ƙara haɗa ni da shi, Ummani ce ke ta tausarsa a hakan ma.
Ana saura kwanaki goma biki Yaya Nazifi ya zo, na saka masa kuka akan a ɗaga biki ni kam, yaga na tashi hankalina sosai to da yake shima yana da buƙatar ɗaga ƙafa sai yace zai yi magana da Malam sai su zo a sami Abbaa. Ni dai na san da kamar wuya domin mahaifina kaifi ɗaya ne, ba ya sauka akan maganarsa, shi ya yanke don haka ba zai taɓa janyewa ba na sani, amma wataƙila a wannan karan ya sauko, kuma abin da ya ɗaga min hankali naje gaishe shi da safe naji suna maganar shi da Ummani akan ko kuɗin katifa ma babu balle sauran kayan ɗaki da ake buƙata, gwara ita Ummani ma tun da jimawa an taɓa kawo mata tallan tukwane tayi dabarar siya bayan su itama bata ajiye komai na kicin ba domin duk basu tsammaci zuwan lokacin aurena yanzu ba, yanda suke kaishi da nisa ashe ba haka Allah ya shirya lamarinsa ba, aure ƙanin mutuwa ne idan ya zo babu yacca za'ai.
Malam suka zo suka sami Abbaa da batun a ɗaga aure yace sam ai shi magana ɗaya yake yi, shi dai zuwa ranar asabar zai ɗaura min aure babu ruwansa da inda Nazifi zai ajiye ni, yayi min abin da na ke so ya kuma fita hakkina. Abin da ya rage tsakaninsa da Nazifi riƙe masa ni amana da kuma cika alƙawarin da ya ɗauka na barina in yi karatu a gidansa, shima kuma ta ɓangarensa zai cika alƙawarin da ya ɗauka na ba zai bar Yaya Nazifi da ɗaukar nauyin karatuna ba shi zai ci gaba da ɗauka matsayinsa na mahaifina da hakkin hakan yake akansa, duk abin da ya shafi katatuna a gidan Nazifi shi a mahaifina shi ke da hidimarsa.
To haka dai da karime karimen abubuwa a É—au wancan a siyar a É—auka wancan a siyar, Yayyuna su kawo É—an abin da suka fita suka samo da haka aka haÉ—a aka min kayan É—aki, Ummani kuwa kusan duk wasu kayanta masu daraja sai da ta É—aga ta siyar aka siya min kayan kicin.
Ranar lahadi aka ɗaura aure, ɗaurin auren da ya tara mutane da yawa. Ranar kam nayi kuka sosai na kuma yi mugun danasanin ɗaga hankalin iyayena da nayi akan auren nan, haka naji ina ma ban san Nazifi ba a rayuwata, domin ranar sai bashin kayan abinci aka karɓo aka yi abincin biki.
Daren ranar aka kaini gidana bayan tarin nasihohin da na sha daga wajen mahaifina masu ratsa jiki, irin nasihar da yake ta min akan zaman aure sai naji ina ma ace a warware wannan auren. hatta shi kansa sai da yay kukan rabuwa da ni, Ummani kam da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikinta, abin da ya ƙara sakani kuka a lokacin yanda Abbaana ya dinƙa bani haƙuri akan ƴan kayan da suka yi ƙoƙari wajen siya min, yana faɗa min don Allah kar nayi fushi in sha Allahu bayan aure da ya samu kuɗi zai sauya min komai ya siya min sababbi masu kyau da ƙarko, kuma za su ƙaro min kaya da yawa indai kuɗi suka zo hannunsa, ya san waɗannan sai dai nayi maleji, kuma yasan za'a iya min dariya idan aka gani tunda tsofaffi ne aka siya amma kar na damu sa duk wanda yay min dariya, wata rana zai saka ni dariyar in Allah ya yarda, kuma fushin da yay da ni akan lamarin auren nayi haƙuri, sannan da zarar naji an fara biyan kuɗin jamb na faɗa masa ya tura min kuɗin registration, haka aka fita da ni daga gidanmu kamar zan shiɗe saboda kewar iyayena da zan yi.
Yashaik ne ya aro motar gidan da yake direba aka kaini a ciki saboda shi Yaya Nazifi ba abokai ne da shi ba, Hamisu ne shi kuma adaidata yake ja don haka shine ma yay ƙoƙarin tattaro tawagar masu adaidaita sahu aka dinga ɗiban ƴan kai amarya.